Za mu ba TCN cikakken goyon baya a Kano, cewar DSS da NSCDC

Manhaja logo

Daga BABANGIDA S GORA a Kano

Hukumar Kula da Al’amuran Ƙasa da Safayo ta Jihar Kano ta yi na’am da buƙatar kwamitin ma’aikatar rarraba wutar lantarki TCN wajen gudanar da ayyukan da su ke shirin aiwatarwa na fahimtar da mutanen da suke zaune kan layukan dogo irin haɗuran da ke tattare da zaman gami da yunƙurin maido wannan layuka da jama’a suka gina gidaje kan shi da yake mallakin hukumar tun tsawon lokaci.

Hakan na zuwa ne lokacin da babbar sakayariyar ma’aikatar ƙasa da sufayo Hajiya Zainab Ibrahim ta karvi kwamitin na TCN na lasa bisa jagorancin Mr Kangeh Anengeh Cephas yayin ziyarar neman goyon bayan gwamnati Jihar Kano na aikin da za su gabatar a jihar.

 Zainab Ibrahim ta kuma ƙara da cewa wannan yunƙuri ne na ceto al’ummar Jihar Kano daga kamuwa da irin cuttukan da zama kusa da wannan layin wuta na dogo yake haifarwa, kana ta ce lallai za su yi iya yin su wajen kamawa don ƙwato filayen da layin yake kai da yawan jama’a suka gina gidajen su a kai wanda mallakin TCN ne.

A nasa jawabin yayin da yake karɓar kwamitin, Daraktan hukumar farin kaya na Jihar Kano Alh. Alhassan Muhammad ya yi masu barka da zuwa, sannan ya ce lallai za su taimaka matuƙa kasancewar suma ma’aikatan gwamnati tarraya ne kamar TCN don haka za su yi aiki tare don cimma nasarar.

Sai  kwamanda na rundunar kula da al’mubazzaranci da vata sauran kayan gwamnati Mr Adamu Idris Zakari ya ce sanin kowa ne kusan rundunar sa na aiki kafaɗa da kafaɗa ne da TCN don kuwa dukkan guraren da kayan TCN suke jami’an su ne ke kula da su.

Zakari ya cigaba da cewa lallai lokacin gudanar da wannan aiki da an basu umarni to abu makawa za su aiwatar, inda kuma ya buƙaci mazauna kan wannan layi wuta mallakin TCN da su ƙoƙarta barin guraren don kaucema kamuwa da cuta da rashin samun kuzari na namiji da ma yawan samun ɓarin ciki saɓanin haihuwa.

Shi ma tun farko shugaban kwamitin Mr Kangeh Anengeh ya bayyana wa hukumomin da suka ziyarta cewa lallai shugaban TCN na ƙasa Engr, Dr Sule Abdul’aziz ya umarci wannan kwamiti na mutane shida don zagayawa jihohin ƙasar nan domin neman goyon bayan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki hanyar faɗakar da jama’a irin abinda TCN ke da niyyar yi, don haka suna buƙatar goyon bayan su.

Cikin tawagar da suka jagoran ci wannan aiki akwai tawaga guda uku; ta farko tawagar kwamitin daga Abuja na biyu akwai tawagar Manajan Darakta mai kula da shiyyar shida da ke Kano, wato Engr. Dangote, sai tawagar ‘yan jaridu don haskaka wa jama’a dukkan matsalolin dake akwai ga zama wannan gurare kuma mallakin TCN.