Editor

9513 Posts
Yanayin kare haƙƙin ɗan Adam na ‘yan ƙananan ƙabilun Sin ya kai matsayin ƙoli a tarihi

Yanayin kare haƙƙin ɗan Adam na ‘yan ƙananan ƙabilun Sin ya kai matsayin ƙoli a tarihi

Daga CMG HAUSA Mataimakin darektan huhumar kula da harkokin ƙabilun ƙasar Sin Zhao Yong, ya ce ƙasar Sin ta samu sabon sakamako a tarihi, yayin gudanar da aikin hada kan ƙabilu daban daban na ƙasar, kuma yanayin kare haƙƙin ɗan adam na ‘yan ƙananan ƙabilun Sin ya kai matsayin ƙoli a tarihi. Jami’in ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yana mai cewa, idan an waiwayi tarihin JKS cikin tsawon shekaru 100, za a lura cewa, babban sakamakon da aka samu a aikin haɗa kan ƙabilun ƙasar, shi ne an samu wata hanyar daidaita matsalar ƙabilu mai tsarin musamman na…
Read More
Wai shin ‘yan Nijeriya za su koma su cigaba da girmama shugabanni?

Wai shin ‘yan Nijeriya za su koma su cigaba da girmama shugabanni?

Daga KWAMARED IBRAHIM ABDU ZANGO Na rasa dalilai ƙwarara ta yadda al’adunmu na ƙwarai suka shuɗe babu girmama shugabanni: wannan abu ya biyo bayan cewa wai kai ya waye! Babu wani addini cikin Duniyar nan da yake sako-sako da tarbiyyar al’umma ko ina a Duniya kuwa. Tarbiyyar jama’a ita ce ke tafiyar da rayuwar al’umma gabaɗaya. Mene ne dalilin daje jawo rashin tarbiyya a yanzu cikin al’umma, kususan tamu a wannan lokaci? Da ɗai babu ko shakka siyasa ta cikin wata aba dimokraɗiyya su ne asalin kawo cikas ga tarbiyya saboda ƙarairayin da suka rataya bisa waccan kalma dimokraɗiyya. Gaskiya…
Read More
Makomar Arewa ta fi ƙarfin siyasar 2023

Makomar Arewa ta fi ƙarfin siyasar 2023

Daga ISAH ABDULLAHI ƊANƘANE A Arewa lokaci ne a yanzu da ake buƙatar haɗin kai, ajiye bambancin ra'ayin ni ɗan Jam'iyyar APC ko PDP ko APGA ne ko dai wacece don haɗin kai, a samu nasara Lokaci ya yi da 'yan Arewa za su dawo su yi wa kansu karatun ta natsu, a ajiye ƙiyayya, hassada, kwaɗayi da tsoro tsakanin juna, a fuskanci babbar barazana da ke barazana ga ƙara raba makomar Arewa, da suka haɗa da: rashin ingantaccen tsaro, talauci, yunwa da rashin ayyukan yi, da kuma matsalar taɓarɓarewar ilmi. Dattawan Arewa da masu riƙe da madafun iko da…
Read More
Shin ana sane ake bawa ‘yan shaye-shaye mafaka a gwamnatance da siyasance?

Shin ana sane ake bawa ‘yan shaye-shaye mafaka a gwamnatance da siyasance?

Daga AMB. AUWAL MUHAMMAD ƊANLARABAWA Ni Amb Auwal Muhd Ɗanlarabawa, ina kira a kan shugabanni da hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a kan a kawo ɗauki wuraren da ake shaye-shaye kamar sakatariyar ƙananan hukumomi da ma'aikatun gwamnati da sauran wuraren taruwar 'yan siyasa don magance ta'ammali da kayan maye. Ni a ganina, da yawa ana kokawa da yadda matasa ke amfani ma'aikatun Gwamnati da wuraren da ake hada-hadar siyasa tare da fakewa ana shaye-shaye, wanda ba mai hanawa ballantana saka doka ta hana su cigaba da aikata laifuka. Hakazalika, Masu kawo ƙorafi sun bayyana cewa idan aka…
Read More
Ɗan shekara 17 ya ƙirƙiri na’urar saƙago a Kano

Ɗan shekara 17 ya ƙirƙiri na’urar saƙago a Kano

Wani matashi ɗan asalin Jihar Kano mai shekara 17 ya ƙirƙiro na’urar saƙago wanda ake kira da ‘Robot’ a Turance, da ya ke sarrafata ta hanyar motsi da hannunsa. Matashin, mai suna Isah Barde dai wanda bai jima da kammala karatun Sakandare ba, ya ƙera na’urar ce ta hanyar amfani da kwalaye da ƙarafa. Isah dai ya bayyana cewa, yana da burin zama kwarare a fannin nazarin fasahar saƙago, duk da cewa iyayensa masu ƙaramin larfi ne. A zantawarsa da manema labarai, matashin ya ce, tsawon shekara uku ya ɗauka yana haɗa na’urar, wacce ya bayyana a matsayin wani ɓangare…
Read More
Alena: Baƙar fata ma fi ƙarancin shekaru da ta samu gurbin karantar fannin likitanci

Alena: Baƙar fata ma fi ƙarancin shekaru da ta samu gurbin karantar fannin likitanci

Alena Analeigh Wicker mai shekaru 13 ta kasance ɗaliba baƙa ta farko da ta fara samun gurbin karatu a fannin karatun likita a yayin da take shekaru 13 kacal a Duniya. Alena Analeigh Wicker ita ce ɗaliba baƙa ta farko da ta aka fara amsa a fannin karatun likitanci a Duniya. Ita dai wannan 'yar yarinya wacce ta fito daga garin Fort Worth na Texas ta Amurka ta kasance tana karance-karance tun tana 'yar shekara 3. Sannan ta yi kwasa-kwasai na share fagen jami'a yayin da take shekaru 11 kacal. Sanna ta shiga kwalejin tana shekara biyu domin samun karatun…
Read More
GAMJIK 2022: Yadda marubutan adabi suka ɗaura ɗamarar yaƙi da rubutun batsa

GAMJIK 2022: Yadda marubutan adabi suka ɗaura ɗamarar yaƙi da rubutun batsa

Na samu gayyata ta musamman daga ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Kano wato GAMJIK ta hannun abokina kuma marubuci Mansur Usman Sufi, bayan gayyatar da aka yi wa wasu ƙungiyoyin marubuta da nake jagoran ta, waɗanda kuma har wa yau suna daga cikin ƙungiyoyin da suka shiga Gasar Muhawara da GAMJIK ta shirya, domin ƙara ƙarfafa zumunci a tsakanin marubutan adabin Hausa, da ba da gudunmawa a ɓangarorin cigaban rayuwa. Babu shakka taro ya ƙayatar sosai, kuma an gudanar da shi cikin nasara, saboda yadda aka samu halartar dandazon marubuta daga sassan arewacin ƙasar nan, tsofaffin marubuta, matasa masu tasowa, manazarta…
Read More
Xi ya bayyana ƙwarin gwiwa game da farfaɗowar yankin Arewa maso Gabashin Ƙasar Sin

Xi ya bayyana ƙwarin gwiwa game da farfaɗowar yankin Arewa maso Gabashin Ƙasar Sin

Daga CMG Hausa Shugaban Ƙasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin ƙolin JKS Xi Jinping ya bayyana cikakken ƙwarin gwiwarsa game da farfaɗowar yankin arewa maso gabashin ƙasar Sin. Xi ya yi wannan tsokaci ne yayin rangadin sa a birnin Jinzhou na lardin Liaoning dake yankin. Yayin ziyarar birnin a jiya Talata, shugaba Xi ya ce salon zamanantar da ƙasar Sin, na tattare da burin samar da walwala da jin dadi ga ɗaukacin al’ummar kasar ba wai wasu tsiraru kaɗai ba. Shugaban na Sin, ya kuma yi kira da a ƙara azama wajen aiwatar da dabarun farfado da yankin na Arewa…
Read More
Auren ‘yar boko!

Auren ‘yar boko!

Daga AMINA YUSUF ALI 'Yar boko! Wannan shi ne sunan da ake kiran macen da ta yi karatu kuma take yin aiki ko take karatun gaba da Sakandare, ko ta gama, ko tana aikin albashi ko ma ba ta aikin. Wannan shi ne lissafin kuɗin goro da ke wa mace 'yar boko a ƙasar Hausa. Masu karatu barkanmu da haɗuwa a wani makon mai albarka! Ta cikin jaridarku mai farin jini, Manhaja. A yanzu kuma za mu tsunduma kan maudu'inmu na wannan mako. A kan auren 'yar boko da irin abubuwan da suke tattare da auren. Duba da yadda a…
Read More
Mijina ne babban abokina – Halima Ahmad Dahir

Mijina ne babban abokina – Halima Ahmad Dahir

"Rashin jajircewa ne ke hana mata 'yan jarida kai wa sama" "Mata da yawa ba sa kai tunaninsu kan yadda za su taimaki mazansu a sana'arsu" Daga AISHA ASAS A yau dai shafin Gimbiya ya ɗauko wa masu karatu wadda ta cancanci mata su kirata da Gimbiya, kasancewar ta jajirtacciyar mace kuma abin koyi ga mata. Mai karatu zai amince da hakan ne ta irin nasarorin da ta samu a ɓangarorin da mata da yawa suke ganin mata ba sa samun kai. Jajirtacciyar 'yar jarida ce da ta kai matsayin riqe babban matsayi a aikin jarida, kuma ta kwashe tsayin…
Read More