Editor

9513 Posts
Xi ya aike da saƙon ta’aziyya ga takwaransa na Masar kan gobarar da ta tashi a wata majami’a a Masar

Xi ya aike da saƙon ta’aziyya ga takwaransa na Masar kan gobarar da ta tashi a wata majami’a a Masar

Daga CMG HAUSA Yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da saƙon ta'aziyya ga takwaransa na ƙasar Masar Abdel Fattah al Sisi, biyo bayan gobarar da ta tashi a wata majami’a a Masar. Xi ya ce, ya firgita da samun labarin gobarar da ta tashi a wata majami’a a Masar, wadda ta yi sanadiyar asarar rayuka da dama. Kuma a madadin gwamnati da jama'ar ƙasar Sin, da kuma shi kansa, ya miƙa saƙon ta'aziyya ga wadanda lamarin ya shafa, tare da jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da wadanda suka jikkata, da kuma yiwa waɗanda suka ji rauni fatan…
Read More
Dole ne Japan ta daina goyon bayan masu ra’ayin nuna ƙarfin soja

Dole ne Japan ta daina goyon bayan masu ra’ayin nuna ƙarfin soja

Daga CMG HAUSA Ranar 15 ga watan Agustan bana, aka cika shekaru 77 da ƙasar Japan ta sanar da mika wuya ba tare da gindaya sharaɗi ba, amma al’ummomin ƙasashen duniya suna damuwa matuka, saboda sun ga yunƙurin da wasu ‘yan siyasar ƙasar masu ra’ayin nuna ƙarfin soja suke nunawa, musamman ma kan batun Taiwan. A kwanakin baya bayan nan, shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta sabawa manufar “ƙasar Sin ɗaya kacal a duniya”, ta kai wa yankin Taiwan na ƙasar Sin ziyara, inda ta sha suka daga ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da kasa sama da 170. Amma firayin…
Read More
Dangantakar Sin da ƙasashen Afrika: Yabon gwani ya zama dole

Dangantakar Sin da ƙasashen Afrika: Yabon gwani ya zama dole

Daga FA’IZA MUSTAPHA Ƙasashen Afrika na kara samun ci gaba da ƙara amfana daga kyakkaywar dangantakar moriyar juna dake tsakaninsu da ƙasar Sin. A wannan mako, ƙasar Habasha ta ƙaddamar da manyan ayyukan ci gaba guda biyu masu muhimmanci ga tattalin arziki da walwalar jama’a da suka hada da yankin ciniki cikin ’yanci na farko a ƙasar da kuma wani babban titin da ya fara daga shataletalen Alexander Puskin zuwa babban titin Gotera, dake birnin Addis Ababa. A ko da yaushe, na kan ce dangantakar Sin da ƙasashen Afrika dangantaka ce ta zahiri da idanu ke iya gani, sannan al’umma…
Read More
Ba a sauya wa Jihar Kaduna suna ba – Gwamnatin Jihar

Ba a sauya wa Jihar Kaduna suna ba – Gwamnatin Jihar

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi watsi da rahoton da ya ce ta sauya wa jihar suna zuwa Jihar Zazzau. Mai ba da Shawara na Musamman ga Gwamnan Kaduna kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, shi ne ya yi watsi da rahoton a madadin Gwamnatin Jihar cikin wata sanarwa da ya fitar ran Talata, yana mai cewa labarin ba gaskiya ba ne. Adeleke ya bayyana rahoton a matsayin na bogi, tare da kira ga al'ummar jihar da su yi watsi da labarin. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito wasu kafafen yaɗa labarai a intanet sun ce,…
Read More
Abubuwan da za su taimaka wajen inganta zaɓen 2023 – Dambazau

Abubuwan da za su taimaka wajen inganta zaɓen 2023 – Dambazau

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa, tsarin karɓa-karɓa zai taka rawa gaya wajen inganta zaɓuɓɓukan 2023. Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar-Janar Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen Taron Lacca na 2021 da kamfanin Blueprint ya shirya ranar Talata Abuja. Kazalika, Dambazau ya ce sake fasalin ƙasa gami da sha'anin addini na daga cikin abubuwan da idan aka riƙe su za su yi tasiri mai ma'ana ga babban zaɓen na 2023. Ya ƙara da cewa, tun bayan samun 'yancin kai, Nijeriyar ta gudanar da manyan zaɓuɓɓuka guda shida, wanda idan Allah Ya so…
Read More
Taron Blueprint: Ba a baro Daniel Amokachi a baya ba

Taron Blueprint: Ba a baro Daniel Amokachi a baya ba

Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Super Eagles kuma Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Ƙwallon Ƙafa, Daniel Amokachi, ya samu halartar Taron Lacca na Shekara-shekara na 2021 da Kamfanin Blueprint ya shirya. Taron wannan karon na gudana ne a Zauren Taro na Ƙasa da Ƙasa da ke Abuja. Daniel Amokachi cikin kwat a zauren taro
Read More
Ɓarayi sun dira gidan Jarumi Saka tare da buƙatar miliyan 20

Ɓarayi sun dira gidan Jarumi Saka tare da buƙatar miliyan 20

Daga AISHA ASAS Ɓarayi ɗauke da makamai sun afka wa gidan fitaccen jarumi barkwanci a masana'antar finafinai ta Kudu, wato Nollywood, Hafiz Oyetoro, wanda aka fi sani da Saka. A ranar Litinin ɗin da ta gabata, a gidansa da ke Abeokuta, Jihar Ogun. Kamar yadda makusanci kuma abokin jarumin Kayode Soaga ya bayyana wa manema labarai, ɓarayin sun dira gidan Saka suna masu neman ya ba su zunzurutun kuɗi har miliyan 20, ko kuma su aika shi lahira. "Ɓarayin sun shigo ne wuraren ƙarfe biyu na dare, ɗauke da manyan bindigogi taƙil da alburusai da kuma wasu makamai. Ba ɓata…
Read More
Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakani na da Will Smith kafin marin Oscar, cewar ƙanin Chris

Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakani na da Will Smith kafin marin Oscar, cewar ƙanin Chris

Daga AISHA ASAS Biyo bayan bidiyon ban haƙuri ga Chris da jarumi Will Smith ya fitar wanda ya ambaci sunan ƙanin Chris Tony Rock a ciki, hakan ya ba wa ƙanin na Chris damar mayar da martani ga waɗanda suka yi ma shi ca a lokacin da ya tofa albarkacin bakinsu kan lamarin na marin da aka yi wa yayansa jarumi Chris. Da yawa sun kira maganganun da Tony ya yi a matsayin katsalandan kan abinda bai shafe shi ba, sai dai kiran sunanshi da Will Smith ya yi ya ba shi damar sanar da masu ganin shishiginsa abinda ba…
Read More