Editor

9513 Posts
Shirin KEEP na Gwamna Bala ya ƙarfafa tattalin arzikin mutane 8,000

Shirin KEEP na Gwamna Bala ya ƙarfafa tattalin arzikin mutane 8,000

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Shirin ƙarfafa Tattalin Arzikin Jama’a na Ƙauran Bauchi, kuma Gwamnan jiha, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed wanda aka yi wa laƙabi da ‘Ƙaura Economic Empowerment Programme (KEEP) da aka ƙaddamar a bara, a yanzu haka ya rarraba kuɗaɗe da kayayyakin sana’o’i daban-daban waɗanda a jimlace sun tasar ma Naira biliyan guda da miliyan dubu ɗari biyu kyauta wa mutane dubu takwas da ke cikin ƙananan hukumomi goma sha shida na jihar. Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya ce har-ila yau gwamnatinsa ta rarraba KeKe Napep guda 1,000 ga ‘yan acaɓa da motoci bus-bus guda 154 lokacin da…
Read More
Kotu da ɗaure ƙasurgumin mai satar mutane, Wadume, shekara bakwai

Kotu da ɗaure ƙasurgumin mai satar mutane, Wadume, shekara bakwai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Shari'a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta ɗaure ƙasurgumin mai satar mutanen nan domin karɓar kuɗin fansa da ke Jihar Taraba, a Kudu maso Gabashin Nijeriya, Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume, shekara bakwai ba tare da zavin tara ba. A shari'ar da aka shafe tsawon shekara uku kotu ta samu Wadume da laifi a kan tuhuma ta biyu da ta goma daga cikin goma sha uku da kuma wasu mutum biyu waɗanda Babban Lauyan Gwamnatin Nijeriya ya gabatar a kansu bakwai. Laifukan da aka ɗaure shi a…
Read More
Li Keqiang ya jaddada muhimmancin sanya sabon kuzari don samar da cigaba

Li Keqiang ya jaddada muhimmancin sanya sabon kuzari don samar da cigaba

Daga CMG HAUSA Daga ranar 16 zuwa 17 ga watan nan, firaministan ƙasar Sin Li Keqiang, ya ziyarci birnin Shenzhen na lardin Guangdong dake kudancin ƙasar Sin, inda ya jaddada cewa, ya dace a bi ra’ayin jagorancin shugaba Xi Jinping, irin na gurguzu mai salon musamman na ƙasar Sin a sabon zamanin da muke ciki. Da tabbatar da sabon ra’ayin samar da ci gaba, da daidaita ayyukan kandagarkin annobar COVID-19, da raya tattalin arzikin ƙasa, da ci gaba da aza tubali mai inganci na farfado da tattalin arzikin ƙasar, a wani ƙoƙari na tabbatar da samar da guraben ayyukan yi…
Read More
Babu nasara ga ’yan awaren Taiwan

Babu nasara ga ’yan awaren Taiwan

Daga SAMINU HASSAN Bisa dukkanin shaidu da dalilai na zahiri, ’yan a waren yankin Taiwan na ƙasar Sin, da masu mara musu baya daga ’yan siyasar ƙasashen yamma, ba su da wani buri da ya wuce jefa Taiwan cikin yanayi na ruɗani. Lura da hakan ne ma ya sanya mahukuntan ƙasar Sin dukufa matuka, wajen yin aiki kafaɗa da kafaɗa da masu burin ci gaban tsibirin Taiwan, wajen shawo kan duk wasu batutuwan da suka shafi sake ɗinkuwar yankin da babban yankin ƙasar Sin cikin lumana. Ko shakka babu, aiwatar da wannan manufa ta hanyar nacewa salon ƙasa ɗaya tsarin…
Read More
Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar Sin ta yi watsi da ra’ayin Blinken kan batun “tarkon bashi na Ƙasar Sin”

Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar Sin ta yi watsi da ra’ayin Blinken kan batun “tarkon bashi na Ƙasar Sin”

Daga CMG HAUSA A yayin ziyarar da ya kai ƙasashen Afirka a kwanan nan, sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka Antony Blinken, ya sake yin tsokaci kan batun "tarkon bashi na ƙasar Sin". Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya musanta wannan batu a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa Alhamis din nan. Yana mai cewa, batun "tarkon bashi na ƙasar Sin" karya ce da ƙasar Amurka da ƙasashen yammacin duniya suka ƙirƙira, don kauce wa nauyin da ya rataya a wuyansu, wanda ba kowa ne ya yarda da shi ba. Don haka, ya…
Read More
‘Sanadin Kenan’ (1)

‘Sanadin Kenan’ (1)

Daga FATIMA IBRAHIM GARBA DAN-BORNO Cikin natsuwarsa ya nufi wurin da aka tanada domin wanke hannu a cikin ofishin nasa, ya zare safar hannunsa yana jin zuciyarsa kamar zata fito waje, saboda tsantsar ɓacin rai. Ya rasa wacce kalma zai yi wa abokinsa amfani da ita, wajen tunatar da shi illar da ke cikin abin da yake ƙoƙarin aikatawa. "Mus'ab shawara na zo nema a wurinka amma kake so ka caza mini ƙwaƙwalwa." Wanda aka kira da Mus'ab bai yi magana ba, ya ci gaba da wanke hannayensa da ruwan dettol, yana jin gefen kansa yana shirin tarwatsewa. Dole ya…
Read More
Masu shirya finafinai ba sa daraja gudunmawar marubuta – Ummi Zee Aflam

Masu shirya finafinai ba sa daraja gudunmawar marubuta – Ummi Zee Aflam

"Da alƙalamin marubuci kowanne ɗan fim ke taka rawa" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Marubuta mutane ne masu ɗimbin baiwa, da suka fito daga ɓangarorin rayuwa daban daban. Babu wani fage da za ka tarar babu marubuci a ciki. Bilhasali ma marubuta su ne malaman al'umma, domin duk wani fage na ilimintarwa sai da marubuta suka ɓata hankalin dare, sannan suka tsara rubutun yadda za a isar da shi ga al'umma. A ɓangaren rubutun adabi, akwai marubuta da ke ba da gudunmawa wajen bunƙasa rubutun zube da na wasan kwaikwayo, wanda masu shirya finafinai ke ɗauka don tsara yadda za a…
Read More
Yankin Taiwan wani ɓangare ne da ba za a iya ware shi daga Ƙasar Sin ba

Yankin Taiwan wani ɓangare ne da ba za a iya ware shi daga Ƙasar Sin ba

Daga AMINA XU Shugaban Ƙasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na ƙasar Amurka Joe Biden a daren ran 28 ga watan Yuli, inda ya nanata matsayin da Sin take ɗauka kan batun yankin Taiwan, wato tun fil azal, yankin wani ɓangare ne na ƙasar Sin da ba za a iya ware shi ba. Kwanakin baya, batun yankin Taiwan na ƙasar Sin ya jawo hankalin duniya, wasu abokanmu sun yi min tambaya kan tarihin yankin Taiwan. To, yanzu zan yi muku bayani. Tun fil azal, Taiwan wani yanki ne na ƙasar Sin, ganin yadda Sinawa ne suka fara gano…
Read More
Gaskiya ba ta ɓuya…

Gaskiya ba ta ɓuya…

Daga IBRAHIM YAYA Bisa ga dukkan alamu, ci gaban da ƙasar Sin ta samu a fannoni daban-daban da irin gudummawar da take bayarwa ga ci gaban zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunƙasuwar tattalin arziki da sauran sassan rayuwa a faɗin duniya, ya damu wasu ƙasashe, waɗanda suke kallo kansu a matsayin jagororin duniya. Wannan ya sa daga lokaci zuwa lokaci, irin waɗannan ƙasashe suke neman ɓata sunan ƙasar Sin ko salon jagorancin ƙasar da al’ummar ƙasar suka yi na’am da shi ko wani tsari da ta gabatar da nufin inganta rayuwar daukacin bil-Adama, kamar shawarar ziri ɗaya da hanya…
Read More
Wang Yi zai karɓi baƙuncin taron masu gudanarwa game da haɗin gwiwar Sin da Afirka

Wang Yi zai karɓi baƙuncin taron masu gudanarwa game da haɗin gwiwar Sin da Afirka

Daga CMG HAUSA Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, zai jagoranci taron ƙolin masu tsara aiwatar da ayyukan da suka biyo bayan taron ministocin dandalin tattaunawa kan haɗin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) gobe Alhamis 18 ga watan Agustan da muke ciki. Mambobin hukumar zartaswar taron kolin ƙungiyar tarayyar Afirka, da ƙasashen Senegal, da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo, da Libya, da Angola da wakilan ministocin ƙasashen Habasha, da Masar da Afirka ta Kudu, wato tsoffin shugabannin Afirka na dandalin FOCAC, da wakilan hukumar gudanarwar ƙungiyar tarayyar Afirka, za su halarci taron. Fassarawar Ibrahim
Read More