19
Aug
Daga CMG HAUSA A yayin taron manema labaru da aka gudanar a yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin ya yi bayani game da sakamakon da aka cimma a taron manyan wakilai game da nazarin matakan aiwatar da sakamakon taron ministocin dandalin tattaunawar haɗin gwiwa tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka FOCAC na 8, inda ya bayyana cewa, yanayin taron ya yi kyau kuma yana da ma’ana sosai. Ɓangarorin biyu sun yi musayar ra’ayoyi da cimma daidaito kan yadda za a aiwatar da sakamakon taron ministocin FOCAC na 8 da kuma inganta haɗin gwiwar abokantaka a tsakanin Sin…
