20
Aug
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe lauya mazaunin Zamfara, Barista Benedict T. Azza Esq. sannan suka yar da gawarsa a gefen Babbar Hanyar da ke kusa da ofishin FRSC, Gusau. Shugaban ƙungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA) reshen Gusau, Barista Junaidu Abubakar Esq. ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka miƙa wa Blueprint ranar Jumma'a. Barista Abubakar ya ce, “A jiya da misalin ƙarfe 2230 na safe a gidana na samu kiran waya har sau uku daga abokan aikinmu inda suka sanar da ni cewa wasu ‘yan…
