21
Aug
Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Wata ƙungiya mai zaman kanta, mai suna Accountability and Democratic Project (ADEP) ta rubuta wa Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC da ya cire sunan tsohon babban hafsan sojojin sama na ƙasa, Abubakar Saddique daga yi wa Jam'iyyar APC takara a Jihar Bauchi. Ƙungiyar ta nuna buqatar neman cire sunan Sadique a matsayin ɗan takara na cikin wata takarda da rubuta ta kuma aike wa INEC. Ƙungiyar ta yi koken cewa ɗan takarar bai gabatar da cikakkun takardunsa ga hukumar zaɓen, kamar yadda doka ta tanada ba. A cewar ƙungiyar, Air Marshall…
