Editor

9513 Posts
Amurka mai satar mai daga Ƙasar Sham

Amurka mai satar mai daga Ƙasar Sham

Daga MINA Abokai, kwanan baya an bankado wasu ayarin motocin dakon mai na sojin Amurka sunafitar da man da suka sata daga ƙasar Sham zuwa sansaninsu dake Iraƙi ta wata hanya da ta hada ƙasar Sham da Iraƙi. Tun daga shekarar 2015, Amurka ta fara aikata irin wannan laifi,awatan Agustan da muke ciki kaɗai, Amurka ta aikata irin wannan abin kunya na satar mai da fitar da shi zuwa Iraƙi har a ƙalla sau 6. Yayin da fararen hula a birnin Damascus babban birnin ƙasar, ke dogayen layi don sayen man. “Duniya a zanen MINA” na zana wani hoto game…
Read More
Sin da Nijeriya sun sa hannu kan takardar kafa tsarin haɗin gwiwa tsakanin asibitocinsu

Sin da Nijeriya sun sa hannu kan takardar kafa tsarin haɗin gwiwa tsakanin asibitocinsu

Daga CMG HAUSA Jakadan ƙasar Sin dake tarayyar Najeriya Cui Jainchun ya gana da ministan kiwon lafiya na Najeriya Osagie Ehanire, inda suka sa hannu kan takardar kafa tsarin haɗin gwiwa tsakanin asibitoci na hukumar lafiya ta ƙasar Sin da ma’aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya. Sun kuma yi musanyar ra’ayi kan yadda sassan biyu za su kara ƙarfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a ɓangaren kiwon lafiya. Yayin ganawar da suka yi a Abuja a ranar 19 ga wata, jakada Cui ya bayyana cewa, asibitin al’umma ta jami’ar Peking da asibiti jami’ar Abuja, za su hada gwiwa domin tabbatar da matsayar…
Read More
Zan haɗa kan ‘yan Nijeriya idan na lashe zaɓe – Atiku

Zan haɗa kan ‘yan Nijeriya idan na lashe zaɓe – Atiku

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya samu gagarumar tarba cikin ƙasaitaccen biki a garin Jada, wanda nan ne mahaifarsa. Da ya ke masa maraba, cikin ƙasaitaccen yanayi da aka shirya na musamman, shugaban ƙaramar hukumar Jada Honorable Salisu Muhammed Solo ya ce, suna mutuƙar alfahari da kasancewar Atiku ɗansu, inda ya yi alƙawarin mara masa baya a takarar shugabancin Nijeriya da ya ke yi.  A jawabinsa yayin taron, Sanata Dino Melaye ya bayyana muhimmancin ziyayar zuwa gida, inda yace wannan ya nuna cewar Atiku ya san asalin sa…
Read More
Masanin Nijeriya: Sin aminiyar ƙasashen Afirka ce a kodayaushe

Masanin Nijeriya: Sin aminiyar ƙasashen Afirka ce a kodayaushe

Daga CMG HAUSA An kira taron masu shiga tsakani na tabbatar da sakamakon taron ministoci karo na 8 na dandalin taron tattauna haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka a ranar 18 ga wannan wata ta kafar bidiyo, inda shehun malami a cibiyar nazarin yadda ake daidaita rikici da wanzar da zaman lafiya ta tarayyar Najeriya, Oboshi Agyeno ya bayyana yayin da yake zantawa da wakilinmu na CMG cewa, sakamakon da aka cimma a jere yayin taron sun nuna cewa, a ko da yaushe ƙasar Sin ta kasance babbar aminiya ga ƙasashen Afirka. Oboshi Agyeno ya ƙara da…
Read More
Ba mu jan ragamar mulki haka sakaka, inji Gwamna Bala

Ba mu jan ragamar mulki haka sakaka, inji Gwamna Bala

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya bayyana cewar, gwamnatinsa ba za ta ja ragamar mulki da sulhuntawa da son zuciya ko bin tafarkin rashin gaskiya ba, sai ta hanyar bin tsarin shari’a, zayyanannun al’adu da kuma wasu yanayi. Kamar yadda gwamnan ya ce, ana tabbatar da kyakkyawan mulki ne ta hanyar bin dokoki, don haka ya kasance wajibi a gudanar da mulki ta tsarin bin doka, samar da ƙwararrun ma’aikata, haɗi da kuɗaɗe domin tafiyar da gwamnati cikin sauƙi. Gwamna Bala yana yin wannan jawabi ne a yayin da yake rattaɓa hannu akan wasu…
Read More
Ruwan sama ya zauna, taki ya tashi

Ruwan sama ya zauna, taki ya tashi

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A can tarihin noma ba batun takin zamani. Wannan ma kai tsaye shi ya sa a ka ambace shi da takin zamani. Abun da mu ka sani shi ne a zamanin can baya a na amfani da takin kashin dabobi ne da ma kwasar bola a kai gona don ƙarfafa kyan yabanya. Wancan takin a kan kira shi da na gargajiya kamar yadda a ke zayyana magungunan kauci da sayu a matsayin maganin gargajiya. Kazalika a shekarun baya akwai wadatar filayen noma masu lafiya da ba sa buƙatar taki mai yawa wajen samar da yabanya. Ba…
Read More
Gidauniyar Action Aids ta gudanar da taron ranar matasa ta duniya

Gidauniyar Action Aids ta gudanar da taron ranar matasa ta duniya

Daga BABANGIDA S GORA a Kano Alhamis da ta gabata gidauniyar da ta ke gudanar da aikinta ƙarƙashin uwar ƙungiyar ta ƙasa watau Action Aid ta bi sauran ƙungiyoyin duniya wajen gudanar da taro kan hanyoyin da matasa za su bi don samun hanyoyin da za su zama mafita a rayuwarka ta yau da kullum. Da ta ke jawabi yayin taron daraktar gidauniyar ta ƙasa, Ene Obi, ta yi matuƙar farin ciki da irin yadda al'umma jihar kano suke ba wannan ƙungiya goyon baya tare da da haɗin kai da ya samo asali wajen jajircewar shugaban wannan gidauniya da sauran…
Read More
Sheikh Giro yana nan raye, inji makusancinsa

Sheikh Giro yana nan raye, inji makusancinsa

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Shugaban makarantar Uthman bin Affan da ke garin Argungu a Jihar Kebbi, Malam Nasiru Abubakar Mera, ya ƙaryata labarin mutuwar Shehin Malamin Addinin Musulunci Sheikh Abubakar Abdullahi Giro Argungu da labarin mutuwarsa ya mamaye kafafen yaɗa labarai na sada zumunci a safiyar jiya Alhamis. Malam Nasiru Abubakar Mera, wanda makusancin shehin malamin ne wanda a lokacin da ya ke zantawa da Wakilin Blueprint Manhaja ta wayar tarho ya nuna rashin jin daɗinsa bisa ga irin yadda musulmi ke ƙirƙiro ƙarya saboda kawai ya tayar da hankalin Musulmi. Ya ƙara da cewa Malam Giro yana…
Read More
Taron Blueprint ya yi armashi

Taron Blueprint ya yi armashi

*Janar Dambazau ya nemi a tsaurara matakan yaƙi da  ta'addanci Daga AMINA YUSUF ALI Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Nijeriya, Laftana Janar Abdulrahman Bello Dambazau (mai ritaya), ya yi kira da a yi garambawul a sashen tsaron ƙasar nan domin magance ƙalubalen tsaro da suke fuskantar ƙasar nan.  Dambazau ya qara da cewa, dole ne a yi nazari na gaggawa a kan salon yaƙi da ta'addancin da muke da shi a Nijeriya, musamman ma saboda yawaitar samun ɓata-gari masu shigowa daga wajen Nijeriya, abinda a cewar sa ya jefa rayuwar 'yan Nijeriya a cikin tasku. Tsohon ministan ya yi…
Read More
NBC ta ɗaga wa kafofin da ake bi bashi ƙafa zuwa 23 ga Agusta

NBC ta ɗaga wa kafofin da ake bi bashi ƙafa zuwa 23 ga Agusta

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), ta dakatar da shirinta na garƙame tashoshin rediyo da talabijin faɗin a ƙasa zuwa wani ɗan lokaci. Hakan ya faru ne sakamakon saka baki da Cibiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa da Ƙasa (IPI) reshen Nijeriya ta yi don samar da maslaha. Tun farko, NBC ta lashi takobin ƙwace lasisin wasu gidajen talabijin da rediyo a faɗin ƙasa kimanin su 52 bashin da ake bin su bashi sakamakon ƙin sabunta lasisinsu. Yanzu dai NBC ta ce ta bai wa kafofin da lamarin ya shafa zuwa ƙarfe shida na…
Read More