22
Aug
Sanata Abdullahi Adamu ya kasance shi ne Shugaban Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya, kuma ya riƙe muƙamin gwamnan Jihar Nassarawa har na tsahon zango biyu, kuma sannan tsohon sanata ne da ya bar gado, ya amshi shugabancin jam’iyyar. Ya amshi ragamar jam'iyyar ne daga hannun Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe a watan Maris, 2022, a yayin da wutar rikici ta ke tsaka da ruruwa a cikin jam'iyyar. A wannan cikin tattaunawar ta musamman da jaridar Daily Trust, Sanata Adamu ya bayyana kyakkyawan fatansa na ganin wutar rikicin da ta ruru a wasu jihohi a jam'iyyar za a kashe…
