Editor

9513 Posts
Ya halaka matarsa saboda ta shanye masa koko

Ya halaka matarsa saboda ta shanye masa koko

Wani matashi a Jihar Neja ya halaka matarsa har lahira saboda rikicin da ya ɓalle tsakaninsu saboda koko. Lamarin ya faru ne a Ƙauyen Kadaura da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Rafi da ke jihar. An samu bayanai akan yadda ya fara da lakaɗa ma ta duka kawo wuƙa wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta. Wani matashi mai shekaru 20 ya halaka matarsa bisa rikicin da su ka samu saboda Koko kamar yadda majiyoyi su ka tabbata. An samu labarin yadda lamarin ya faru a ƙauyen Kadaura da ke ƙaramar hukumar Rafi, inda matar ta rasa ranta bayan mijinta ya zane ta.…
Read More
Ta kashe mijin abokiyar maɗigonta a Anambara

Ta kashe mijin abokiyar maɗigonta a Anambara

Wata mata ta kashe mijin abokiyar maɗigonta ta hanyar daɓa masa wuƙa a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Rahotanni sun nuna cewa, ba a bayyana sunan matar da ta yi kashe Ikechukwu Onuma da aka fi sani da ‘Ayaaya Onye-Obodo’ ba, amma tana aiki a Kwalejin horo na lafiya a Onitsha. Ta gudanar da wannan aika-aikar ne a gidan mutumin a kan titin Ogboli da misalin qarfe 9:20pm na daren Talata a birnin Onitsha da ke jihar Anambra. Marigayi Mista Onuma ya isa gida ba tare da matarsa ta sani ba, inda ya tarar da ita da…
Read More
MURIC ta buƙaci a gaggauta yin adalci kan kisan Sheikh Aisami

MURIC ta buƙaci a gaggauta yin adalci kan kisan Sheikh Aisami

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Kare 'Yancin Musulmi (MURIC) ta yi kira da a gaggauta yin adalci kan kisan shahararren malamin nan Shaykh Goni Aisami da wasu sojoji biyu suka yi. MURIC ta bayyana kashe malamin da aka yi a ranar Juma'a, 19 ga Agustan 2022 a matsayin kisan wulaƙanci wanda ya zama wajibi a bi wa marigayin kadinsa. Ƙungiyar ta yi waɗannan kalaman ne cikin sanarwar manema labarai da ta fitar ran Litinin ta hannun daraktanta, Farfesa Ishaq Akintola. Sanarwar ta ce, “Wani soja da ya yi iƙirarin yana bakin aiki ya kashe fitaccen malamin Islaman nan da ke Gashua,…
Read More
Nasarorin haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka a shekaru goman baya

Nasarorin haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka a shekaru goman baya

Daga LAWAL SALE Hulɗa dai tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka ta fara ne da daɗewa tun a lokacin da ƙasar Sin tana hada hadar cinikayya da ƙasashen ƙetare a kan daɗaɗɗiyar “hanyar siliki’’ da kuma lokacin gwagwarmayar neman ’yanci da Afirka ta yi fama da shi daga hannun ’yan mulkin mallaka daga farkon 1950 wanda ƙasar Sin ta yi rawar gani domin ganin ƙasashen Afirka sun samu ’yancin kai. A sakamakon samun ’yancin da ci gaba da kulla hulɗar diplomasiyya ne ƙasashen na Sin da Afirka suka samu damar ƙulla zumunta wadda ta kai ga irin haɗin gwiwar da…
Read More
Ƙulla dangantaka da Ƙasar Sin domin samun sakamakon moriyar juna cikin sauri

Ƙulla dangantaka da Ƙasar Sin domin samun sakamakon moriyar juna cikin sauri

Daga CMG HAUSA Ranar 21 ga watan Augusta, muhimmiyar rana ce ga shawarar Ziri D'Ɗaya da Hanya Daya. A wannan rana, jirgin kasan ƙasar Sin ya tashi daga tashar ƙasa da ƙasa ta Xi’an dake yammacin ƙasar, ya nufi birnin Hamburg na Jamus. Wanda ya zama karo na 10,000 da jirgin ƙasa na ƙasar Sin ya je Turai a bana. A kuma ranar ce, aka fara fitar da jiragen ƙasa masu sauri na ƙasar Sin a hukumance, inda aka tura jiragen ƙasa masu amfani da lantarki da jerin jiragen gwajin layin dogon Jakarta zuwa Bandung, daga tashar ruwa ta Qindao…
Read More
Sin ta bayyana kalaman jakadan Amurka a Sin a matsayin shaidar dake nuna tunani irin na danniya

Sin ta bayyana kalaman jakadan Amurka a Sin a matsayin shaidar dake nuna tunani irin na danniya

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, ya ce kalaman da jakadan Amurka a Sin Nicholas Burns ya yi a lokacin wata zantawa da kafar watsa labarai ta CNN a kwanan nan, na nuni ga irin tunani na danniya da Amurka ke da shi. Jami’in na Sin ya ce, yayin zantawar Burns da kafar ta CNN, ya tabo batun ziyarar kakakin majalissar wakilan Amurka a yankin Taiwan, inda ya sauya fari zuwa baki, yana mai cewa an zuzuta lamarin fiye da kima. Ƙasar Sin ta gabatar da kakkausan ƙorafi ga Amurka a lokuta daban-daban, don gane…
Read More
Fulani ku haɗa kanku

Fulani ku haɗa kanku

Ga dukkan alamu za a iya samun shawo kan wasu matsaloli da ke tattare da ƙabilu na Fulani. Mun ji sabon shugaba na Tabito Fulako wanda tsohon gwamna na jihar Bauchi ne. Malam Isah Yuguda wanda ya zamo shugaba na dukkanin ƙasashen nafiyar Afrika. Muna fatan yan uwa fulani a taho a haɗu a zamo an maido ma jinsin kima da martaba irin ta tun farko. Fulani mun gado kunya da kawaici da kamun kai amma a ka samu wasu waɗanda rashin ilimi da rashin tarbiyya ya rinjaye su zuwa ɗaukar hanyar ta'addanci da badala. Muna fatan Allah ya sanya…
Read More
Rubutun batsa na iya haifar da yawaitar aikata fyaɗe – Rahama Sabo Usman

Rubutun batsa na iya haifar da yawaitar aikata fyaɗe – Rahama Sabo Usman

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Gamayyar Ƙungiyoyin Marubutan Jihar Kano, wato GAMJIK, ƙungiya ce da marubutan adabi suka kafa domin ƙarfafa haɗin kai a tsakanin su da samar da tsari wajen fitar da labaran hikayoyi masu inganci da suka dace da tarbiyyar addinin Musulunci da al'adun al'ummar Arewa. Wani gangami da ƙungiyar ta runguma kuma take neman goyon bayan hukumomi, gwamnati da marubutan adabi a kansa shi ne yaƙi da yaɗuwar rubutun batsa da ya ke neman mamaye harkar rubutun adabi a halin yanzu, matsalar da ƙungiyar GAMJIK ke ganin tana buƙatar a yi mata rubdugu, don a kawo ƙarshen ta…
Read More
Kotu ta tasa ƙeyar matashin da ya yi sanadiyyar rasa ƙafar matashiya Fatima a Sakkwato

Kotu ta tasa ƙeyar matashin da ya yi sanadiyyar rasa ƙafar matashiya Fatima a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Wata kotun majistare dake a Sakkwato ta tasa ƙeyar Aliyu Sanusi Umar matashin da ake zargi da yin tuƙin ganganci da ya yi sanadiyar rasa ƙafar ɗalibar makarantar Khalifa dake Sokoto Fatima. Wannan dai ya biyo ne bayan ƙarar da lauyan Fatima suka shigar a gaban kotu, da suke buƙatar kotun ta ƙwato wa Fatima haƙƙinta daga wanda ake zargi da zama sillar rasa ƙafarta. Mahaifin Fatima bayan fitowa daga kotu Lauyan mai ƙarar a zaman kotun na ranar Litinin ya buƙaci kotun da ta duba yuwar bada belin wanda ake zargin la'akari da tanadin…
Read More
Dandalin shawara

Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Aunty Ayshat Ina jin daɗin karanta littafinki, dan Allah ni ko matsalata a kullum idan na yi wanka, na shirya, in mijina ya dawo, sai ya ce, akwai iya wanka, amma babu gashi, babu hasken fata. Dan Allah aunty ko da akwai abinda za ki bani shawara akai. Please ki taimaka mani. A huta lafiya. Na gode. AMSA: Wa'alaiki salam warahmatullah. Da farko zan fara da bayyana miki bambancin biyayya ga miji da kuma biye wa miji kan wasu buƙatu na ra'ayin kansa. Duk da cewa addini ya ce, ki bi mijinki sau da…
Read More