Editor

9513 Posts
Kannywood: Gyara ta sai ‘yan cikinta – Martani ga Gidan Dabino

Kannywood: Gyara ta sai ‘yan cikinta – Martani ga Gidan Dabino

Daga KAMAL IYANTAMA Kamar yadda na yi katari na karanta a wata jaridar Hausa, inda fitaccen marubuci Ahmad Gidan Dabino (MON) ya yi wani ƙayataccen bayani mai cike da alfanu, kuma bayanin ya burge ni. Kada a ɗauka martanin da na rubuta a sama, martani ne na suka ko kushe, a'a martani na yabawa zan yi wa Gidan Dabino, wato yadda Kannywood ta zama a yanzu abin babu daɗin ji da gani, wanda kuma gyaran ta sai 'yan cikinta. Misali; Baturen da zai zo ya ce zai rubuta ma asali da tarihinka a matsayinka na Bahaushe, ai ka san labarin banza ne…
Read More
Gudunmawar sojojin ga cigaban tsaro da zaman lafiya

Gudunmawar sojojin ga cigaban tsaro da zaman lafiya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Bahaushe ya yi wata karin magana da ke cewa, 'soja birgimar hankaka, kowa ya ga baqin ku zai ga farin ku'. Haka kuma za ka ji yana yi wa soja kirari da cewa, na gwamna ga rawa ga yaƙi! Waɗannan wasu kalmomi ne da ake amfani da su wajen kambama irin jarumta da rawar ganin da sojoji ke takawa, a matsayin su na dakarun tsaron ƙasa da tabbatar da zaman lafiya. Matsayin soja a kowacce ƙasa ta duniya ba ƙarami ba ne, saboda kasancewarsa ginshiqin kafuwar kowacce ƙasa. Masana tsarin aikin soja na faɗin cewa, kafuwar…
Read More
Kyan alƙawari cikawa

Kyan alƙawari cikawa

Daga CMG HAUSA Akwai wasu mutane 2, ɗaya ya iya magana sosai, amma yakan manta da maganar da ya faɗa, yayin da ɗayan ba ya son magana, sai dai duk wani alƙawari da ya yi, zai yi ƙoƙarin cika shi. A cikin mutanen nan 2 wanne ka fi so? Tabbas za a ƙulla abota tare da mutum na biyu ko? Saboda “Alƙawari kaya ne”. Ba za a iya dogaro kan wani ba, idan ba zai iya cika alƙawari ba. Wani babban dalilin da ya sa ƙasar Sin ta zama aminiyar ƙasashen Afirka, shi ne yadda suke iya dogaro da ita,…
Read More
Girmama cikakken ’yanci da yankunan ƙasa, wajibi ne a kan kowacce kasa babba, ko ƙarama

Girmama cikakken ’yanci da yankunan ƙasa, wajibi ne a kan kowacce kasa babba, ko ƙarama

Daga FA’IZA MUSTAPHA A matsayinta na shugabar kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya a wannan wata, ƙasar Sin, bisa jagorancin wakilinta na dindindin, ta kira taro kan samar da tsarin tsaro da ya dace da yanayin da ake ciki da girmama cikakken ’yanci da yankunan dukkan kasashe, domin samun yanayin tsaro mai ƙarƙo a duniya. Haƙiƙa kiran wannan taron da Wakilin Sin Zhang Jun ya yi ta zo a daidai lokacin da ya dace, ganin yanayin ƙalubale da duniya take ciki da kuma yadda ake keta cikakken ’yancin ƙasashe da takalar fada da kuma ingiza tayar da rikici. Zamanin mulkin…
Read More
Taƙaddamar Sin da Amurka ba za ta taimaka wa gwamnatin Biden a yaƙin da take yi da hauhawar farashin kayayyaki ba

Taƙaddamar Sin da Amurka ba za ta taimaka wa gwamnatin Biden a yaƙin da take yi da hauhawar farashin kayayyaki ba

Daga CMG HAUSA Ba'amurke masanin tattalin arziki Jeffrey Sachs, ya ce taƙaddamar da Sin da Amurka ke yi game da wasu batutuwa na cinikayya da tattalin arziki, ba za ta taimakawa gwamnatin Joe Biden na Amurka ba, a yaƙin da take yi da hauhawar farashin kayayyaki. Yayin zantawarsa da kafar CNBC cikin shirin tashar na "Street Signs Asia", Mr. Jeffrey Sachs, ya ce bai kamata gwamnatin shugaba Biden ta ci gaba da aiwatar da takunkuman da tsohuwar gwamnatin shugaba Trump ta ƙaƙaba wa ƙasar Sin ba, la’akari da cewa, ga alamu na zahiri, shi ma shugaba Biden din na bin…
Read More
An sanya hannu kan yarjeniyoyin kasuwanci na biliyoyin kuɗaɗe yayin baje kolin na’urorin zamani na Chongqing

An sanya hannu kan yarjeniyoyin kasuwanci na biliyoyin kuɗaɗe yayin baje kolin na’urorin zamani na Chongqing

Daga CMG HAUSA Rahotanni na cewa, an rattaba hannu kan manyan yarjejeniyoyin kasuwanci guda 7, waɗanda suka kai darajar kuɗin Sin yuan biliyan 212.1, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 31.1, yayin baje kolin na’urorin zamani mai laƙabin “Smart China Expo 2022”, wanda aka buɗe a ranar Litinin a birnin Chongqing, na kudu maso yammacin ƙasar Sin. Yarjejeniyoyin kasuwancin dai sun ƙunshi fannonin samar da ababen hawa dake amfani da na’urori masu ƙwaƙwalwa, da fasahohin samar da manhajojin fasahar sadarwa, da fasahohin ƙirƙire-ƙirƙire, da amfani da na’urori wajen sarrafa kayayyakin masana’antu. Ana kuma fatan yarjejeniyoyin za su ingiza ƙarfin birnin Chongqing, na…
Read More
Marigayi Alhaji Dakta Shehu Idris

Marigayi Alhaji Dakta Shehu Idris

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris na ɗaya daga cikin manyan sarakunan Arewancin Nijeriya. Mai martaba sarki mutum ne masani, sannan kuma abin girmamawa a duk faɗin Arewa. Yana da karimci. Ɗaya daga ciki ɗimbin hikimomi da Allah ya yiwa mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris ita ce tafiya da mutanen a cikin mulkinsa, yakan tuntuvi jama’a a kan abubuwan da ka je. An haifi mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris a shekarar 1937. Shi ɗa ne ga Malam Idris Autan Sambo, shi kuma ɗan sarkin Zazzau na 10, Malam…
Read More
Marigayi Alhaji Ado Abdullahi Bayero

Marigayi Alhaji Ado Abdullahi Bayero

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alhaji Ado Bayero shi ne Sarki na 55 a jerin sarakunan Kano kuma sarki na 13 a sarakunan Fulani. Tun daga farkon sarautar Kano zuwa shekarar 2017, marigayi Alhaji (Dr.) Ado Bayero shi ne sarkin da ya fi kowane sarki daɗewa a kan karagar mulkin Kano. Sarki ya mulki Kano na tsawon shekaru 51 tun daga 1963 har zuwa 2014. Tsohon ma’aikacin banki, wakilin doka, ma’aikacin hukumar En’e (NA), kuma tsohon wakilin Nijeriya a ƙasar Sinigal. Daraja, da martabar masarautar Kano ta ɗaukaka a iya tsawon mulkinsa. Haihuwarsa: An haifi Alhaji (Dr.) Ado Bayero a ranar…
Read More
Me yake kawo zargi a zaman aure?

Me yake kawo zargi a zaman aure?

Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a shafinku na Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako kuma muna tafe da matsalar zargi a zaman aure. Wannan matsala ta zama ruwan dare a cikin gidajen aure. Mene ne zargi? Da farko dai zargi yana nufin zaton wani abu yana faruwa ko zai faru ko kuma ya riga ya faru wanda kuma babu tabbaci a ciki. Kawai zuciyar mutum za ta dinga yi masa saƙe-saƙe da wasi-wasi na akwai wasu abubuwa da suke faruwa ko ya gane meye shi ko bai gane ba. Kuma ko yana…
Read More
Mai juna biyu ta datse mazaƙutar mijinta da wuƙa a Taraba

Mai juna biyu ta datse mazaƙutar mijinta da wuƙa a Taraba

Wata matar aure mai shekara 25 ta datse mazaƙutar mijinta a garin Tella da ke ƙaramar hukumar Gassol na Jihar Taraba. Matar mai suna, Halima ta tafka wannan aika-aikar ne a ranar Talata yayin da mijinta, Umar Aliyu ke sharar barci. Ƙanin wanda abin ya faru da shi, Shagari Umar, ya ce, ihun Aliyu ne ya jawo hankulan mutane inda suka zo suka tarar da shi kwance cikin jini. Umar ya yi ikirarin cewa, “mun ga matarsa Halima zaune a gefen gado riƙe da wuƙar da ta yi amfani da shi wurin datse mazaƙutar ɗan uwanmu. Ya ƙara da cewa,…
Read More