Editor

9513 Posts
Masarautar Lafiya ta naɗa Dr. Justina Kotso sarautar Tauraruwar Ilimin Matan Nasarawa

Masarautar Lafiya ta naɗa Dr. Justina Kotso sarautar Tauraruwar Ilimin Matan Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya A ƙarshen makon da ya gabata ne Masarautar Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa ta naɗa wa shugabar makarantar Kimiyya da Fasaha ta gwamnatin jihar wadda aka fi sani da Isa Mustapher Agwai Polytechnic dake Lafiya, Dokta Justina Kotso sarautar Tauraruwar Ilimin Matan Jihar Nasarawa.  Da yake jawabi jim kaɗan bayan ya naɗa wa shugabar makarantar sarautar, Mai martaba Sarkin Lafiya wanda shi ne kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiyan jihar, mai shari’a Sidi Bage mai ritaya ya bayyana cewa masarautar ta yanke shawarar naɗa wa Dokta Justina Kotso sarautar ne bayan ta yi la’akari da…
Read More
Ƙwararru: Shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” na bunƙasa ci gaban nahiyar Afirka

Ƙwararru: Shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” na bunƙasa ci gaban nahiyar Afirka

Daga CMG HAUSA Wasu masu bincike, kuma ƙwararru game da al’amuran ƙasa da kasa na yankin gabashin Afirka, sun bayyana shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” da ƙasar Sin ta gabatar, a matsayin manufar dake ingiza ci gaban nahiyar Afirka. Ƙwararrun sun yi tsokacin ne a jiya Laraba, yayin taron yini guda da ya gudana ta kafar bidiyo, mai taken "Muhimmancin shawarar ziri ɗaya da hanya daya ga nahiyar Afirka." Ɗaya daga cikin ƙwararrun Frederick Golooba Mutebi daga ƙasar Uganda, ya ce shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya, ta zamo ginshikin aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, da rage matsalar…
Read More
Duniya ba ta buƙatar duk wani nau’i na yaƙin cacar baka

Duniya ba ta buƙatar duk wani nau’i na yaƙin cacar baka

Daga SAMINU HASSAN A baya bayan nan, yayin zaman kwamitin tsaro na MƊD game da rikicin ƙasar Ukraine, an tabo muhimman batutuwa game da halin da ake ciki, don gane da wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa, wanda a yanzu haka ya doshi wata na 7. Tuni sassan duniya daban daban suka dandani raɗaɗin tasirin wannan rikici, kama daga kamfa, da hauhawar farashin makamashi a sassan nahiyar Turai, zuwa ƙarancin hatsi, da takin zamani da sassan ƙasashe masu tasowa, kamar nahiyar Afirka ke fama da shi. Game da wannan batu, tsagin ƙasar Sin na ganin a wannan…
Read More
Xi ya aike da wasiƙar taya murna ga taron haɗin gwiwar kafofin watsa labarai tsakanin Sin da Afirka karo na biyar

Xi ya aike da wasiƙar taya murna ga taron haɗin gwiwar kafofin watsa labarai tsakanin Sin da Afirka karo na biyar

Daga CMG HAUSA Yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasiƙar taya murna ga taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kafofin watsa labarai tsakanin Sin da Afirka karo na 5. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tun bayan kafa shi shekaru 10 da suka gabata, dandalin ya samar da wata muhimmiyar kafa ga kafofin watsa labaru na Sin da Afirka, wajen inganta tattaunawa da haɗin gwiwa, kana ya taka muhimmiyar rawa wajen sa ƙaimi ga yin musaya da yin koyi da juna, tsakanin wayewar kan Sin da Afirka, da zurfafa cikakkiyar dangantakar haɗin gwiwa bisa manyan tsare-tsare…
Read More
Jarin Sin ya taimaka wajen raya tsarin samar da kayayyaki a Afrika

Jarin Sin ya taimaka wajen raya tsarin samar da kayayyaki a Afrika

Daga CMG HAUSA Majalisar kula da harkokin kasuwanci tsakanin Sin da Afrika (CABC), ta fitar da wani sabon rahoto kan jarin da ƙasar Sin ta zuba a ƙasashen Afrika, wanda ya bayyana cewa, cikin shekaru 22 da suka gabata, ɓangarorin biyu sun samu dimbin nasarori ta kowacce fuska tare da haɗa gwiwa a bangarori da dama. Rahoton da aka fitar a jiya, ya ce manyan jami’an majalisar sun ce kamfanonin ƙasar Sin sun yi kyakkyawan tasiri, kana sun kasance wani ɓangare mai matuƙar amfani na kasuwar Afrika. Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa
Read More
Yaƙin Afghanistan ba fim ba ne

Yaƙin Afghanistan ba fim ba ne

Daga CMG HAUSA “Dana ɗaya ya faɗo daga jirgin sama a filin jiragen sama na Kabul, ɗayan kuma har yanzu ba mu san inda yake ba”. Kalaman da Mohammad Rezayee, dan ƙasar Afghanistan ya yi a kwanan baya a yayin da yake tattaunawa tare da jaridar The Times ta Burtaniya a kwanan baya, sun tunatar da mu kan abin da ya faru a shekara ɗaya da ta gabata. A watan Agustan shekarar 2021, Amurka ta janye sojojinta daga ƙasar Afghanistan ba tare da ɗaukar nauyin da ke bisa wuyanta ba, matakin da ya sa dubu dubantar ‘yan Afghanistan suka kutsa…
Read More
Sai an sha wuya a kan sha daɗi

Sai an sha wuya a kan sha daɗi

Daga IBRAHIM YAYA Sanin kowa ne cewa, duk ƙasar dake fatan samun ci gaba har ma a rika jin amonta a duniya, wajibi ne al’ummarta su zage damtse wajen ganin wannan buri ya tabbata. Kamar sauran al’ummomin ƙasashen duniya, al’ummar Sinawa sun hada ƙarfi da ƙarfe wajen gina ƙasar Sin mai bin tsarin gurguzu mai sigar musamman ta ƙasar Sin a sabon zamani. Gagarumin ci gaban da ƙasar Sin ta cimma a cikin shekaru 10 da suka gabata (2012-2022), sun haɗa da fannonin tattalin arziki, da binciken sararin samaniya, da fannin ƙirƙire-ƙirƙire da inganta muhalli da zaman rayuwar jama’a da…
Read More
Magidanta idan Allah Ya hore ma ku, na gida ma su shaida – Farida Shehu Sa’ad

Magidanta idan Allah Ya hore ma ku, na gida ma su shaida – Farida Shehu Sa’ad

"Burina in ga fuskar maraya a cikin murmushi" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Tausayawa da nuna jin ƙai ga maraya abu ne mai matuƙar muhimmanci wanda addini ke ƙarfafawa, sai dai ba kasafai ake samun mutane masu nuna halin ya kamata wajen tallafa wa maraya ba, ko da kuwa na kusa da su ne ballantana wanda babu dangin Iya ba na Baba. Duk da halin ƙuncin rayuwa da akasarin ýan Nijeriya ke ciki, mutane irin su Hajiya Farida Shehu Sa'ad da ke zaune a Jos, na daga cikin ƙalilan ɗin mutanen da suka ɗauki al'amarin inganta rayuwar marayu da yaran talakawa…
Read More
Tafiyar Shekarau da Kwankwasiyya: Tarihi ne yake neman maimaita kansa

Tafiyar Shekarau da Kwankwasiyya: Tarihi ne yake neman maimaita kansa

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN Jiya na ke jin wani labari, wai Shekarau zai bar NNPP ya koma wata jam'iyar, gaskiya ne ko ba gaskiya ba ne? Ni dai ba ni da tabbaci, amma in ya zama gaskiya ne, to ma iya cewa tarihi na neman maimaita kansa kenan. Lokacin yaƙin basasar Kano tsakanin Tukurawa da Yusufawa; Yusufawa ba su samu sarautar Kano ba, sai suka fice daga Kano su kai sansani a wajejen Takai. Daga nan suka haɗa runduna don su shigo Kano su ƙwaci sarautar Kano, don su ƙara ƙarfi sai suka dinga tura wasiƙu wajen Sarakuna irin su…
Read More
Atiku ko Tinubu: Wanne ba wanne ba?

Atiku ko Tinubu: Wanne ba wanne ba?

Daga RAHMA ABDULMAJID Eh! Akan yan takararmu guda biyu waɗanda da alamar su ne za su fafata da gaske a kan kujerar shugaban ƙasa. Alhaji Atiku Abubakar ɗan Shekaru 76 (wataƙil da takwas) da Alhaji Ahmad Bola Tinubu dan shekaru 70 (wataƙil 78). Ga duk mai kallon wasan kwaikwayo mai dogon zango, ya san munin ƙarshe. Hakazalika, mai kallon ƙwallon ƙafa ya san bugun fanareti a wasan ƙarshe. To a siyasar waɗannan mutanen ma da alamar za mu san wasan ƙarshe, domin  ko za su buga wasan ƙarshe inda a wannan karon dolen dole ne ɗaya ya yi wa ɗaya…
Read More