Editor

9513 Posts
An ƙaddamar da shirin KAZBO karo na uku

An ƙaddamar da shirin KAZBO karo na uku

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato ta ƙaddamar shirinta na ƙarfafa mata iyayen marayu na kiyon kaji da aka fi sani da KAZBO wato kaza, zabo da mata ɗari da suka fito daga gundumomi daban-daban. Da yake jawabi lokacin ƙaddamar da shirin, Shugaban Zartarwar Hukumar ta Zakka da Waƙafi Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato), ya ce manufar wannan shirin shine ƙarfafa uwayen marayu domin su iya dogaro da kansu ta hangar kiyon kajin. Ya bayyana cewa hukumar tasa ta samu ƙwarin guiwar ƙaddamar da wannan bisa nasarorin da aka samu tun fara shirin…
Read More
Ƙungiyar Ɗalibai ta BMGGG ta yi tir da yunƙurin assasa Dogara a matsayin mataimakin shugaban ƙasa

Ƙungiyar Ɗalibai ta BMGGG ta yi tir da yunƙurin assasa Dogara a matsayin mataimakin shugaban ƙasa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Wasu gungun Musulmi dake ƙarƙashin lemar Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi ta Nijeriya (MSSN) sun bayyana ƙarara cewar, ko da wasa ba za su taɓa goyon bayan yunƙurin da wasu ‘yan siyasa ke yi ba na ganin sun ɗora Yakubu Dogara a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa wa ɗan takarar Shugaban Ƙasa, Asiwaju Ahmad Bola Tinubu a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar APC ba a gabanin babban zaɓen shekarar 2023. Gungun, da suke da laƙabin “Bauchi Muslim Good Governance Group (BMGGG)”, sun kuma ce, ba za su taɓa goyon bayan Dogara wa kowane irin muƙamin shugabanci na ƙasar…
Read More
’Yan daba sun far wa ’yan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

’Yan daba sun far wa ’yan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne wasu ɓatagari su ka kai wa 'yan majalisar dokokin Jihar Bauchi farmaki a gidan shaƙatawarsu, inda su ka raunata mutum shida tare da lalata motoci da tagogi a gidan. Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, (NAN) ya bayar da rahoton cewa majalisar ta faɗa cikin rikicin shugabanci inda a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne mambobi 22 su ka kaɗa ƙuri’ar rashin goyon baya ga shugaban majalisar, Abubakar Suleiman da sauran masu riƙe da muƙamai a majalisar. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Babale Abubakar, ya shaida…
Read More
Gwamnatin Nijeriya za ta ɗauki mutum miliyan ɗaya aikin ƙidaya

Gwamnatin Nijeriya za ta ɗauki mutum miliyan ɗaya aikin ƙidaya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Ƙidaya ta Nijeriya (NPC) ta ce gwamnati za ta ɗauki 'yan ƙasar miliyan ɗaya aiki domin gudanar da ƙidayar jama’a a shekarar 2023. Hukumar ta ba da tabbacin cewa, an samar da kyakkyawan tsarin gudanar da ƙidayar don hana 'yan siyasa da masu mummunar aniya amfani da wannan dama. Jaridar Daily Trust ta rawaito kwamishinan hukumar mai kula da jihar Ekiti Mista Deji Ajayi na bayyana hakan ranar Litinin a Ado Ekiti a wani taron manema labarai da ya kira kan ƙidayar gwaji da za a gudanar a jihar. A yayin da yake…
Read More
Masarautar Katsina ta soke hawan sallah na bana

Masarautar Katsina ta soke hawan sallah na bana

Daga UMAR GARBA a Katsina Masarautar Jihar Katsina wadda mai Martabata Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ke jagoranta, ta sanar da cewa ba za ta gudanar da hawan Sallah ba kamar yadda aka saba a bana. Bayanin hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da masarautar ta fitar wa manema labarai a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun mai taimaka wa sakataren masarautar kuma wato Sarkin tsaftar Katsina Alhaji Sule Mamman Dee.  Sai dai sanarawa ta bayyana cewar mai martaba sarki zai halarci Sallar Idi idan Allah ya kaimu ranar Asabar da ake sa ran gudanar da Sallah…
Read More
Wutar lantarki ta ja ɓarawo ya rasu yayin sata a turansifoma

Wutar lantarki ta ja ɓarawo ya rasu yayin sata a turansifoma

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ‘yan sandan Jihar Abiya ta tabbatar da cewa wani da a ke zargi ɓarawon kayan taransifoma ne ya rasa ransa bayan da wuta ta ja shi a ƙauyen Amoji-Ukwu da ke Ƙaramar Hukumar Obingwa a jihar. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Geoffrey Ogbonna, ya bayyana cewa, wanda ake zargin varawo ne da har ya yanke wayoyi biyu a jikin na’urar ta taransifoma da sanyin safiyar Juma’a.Ogbonna ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a ranar Asabar a Aba.…
Read More
Gwamna Bello ya hana haƙar ma’adinai a Jihar Neja

Gwamna Bello ya hana haƙar ma’adinai a Jihar Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanya dokar dakatar da haƙar ma’adinai a ƙananan hukumomin Shiroro, Munya da kuma Rafi. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Ahmed Ibrahim Matane ya fitar da yammacin Litinin. Ta cikin sanarwar ‘, sakataren ya ce akwai buƙatar a dakatar da haƙar ma’adinai sakamakon yadda rashin tsaro ke ƙara ƙamari a 'yan kwanakin nan ta yadda 'yan bindiga ke kai hare-hare. Haka kuma ya ƙara da cewa an lura da cewa wuraren haƙar ma’adinai na janyo masu aikata laifuka waɗanda ke ci…
Read More
Ango da amarya sun yi mutuwar kasko

Ango da amarya sun yi mutuwar kasko

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani ango da amarya sun yi mutuwar kasko, bayan angon ya bulbula wa amaryar tasa fetur ya kunna mata wuta, ita kuwa ta ƙanƙame shi don su mutu tare.  Kamar yadda jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labarai, lamarin ya faru ne ranar Asabar a Otun-Akute.  Tun farko dai amarya Lateefat ta bar gidan angon nata ne da ya aure ta shekaru uku da suka wuce, ta koma gidan maƙwabtansu saboda ta zarge shi da dukanta da kuma yi mata zagin cin mutunci. …
Read More
Zargin safarar sassan mutum: An tsare Ekweremadu da matarsa har zuwa Agusta

Zargin safarar sassan mutum: An tsare Ekweremadu da matarsa har zuwa Agusta

Daga BASHIR ISAH An tsare Sanata Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice, bayan da kotun da ke sauraron kararsu ta dage zamanta ya zuwa 4 ga Agustan 2022. An gurfanar da ma’auratan ne a kotun Westminster Majistare kan zargin safarar sassan jikin mutum. Wasu manyan ‘yan Nijeriya sun halarci zaman kotun, ciki har da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark, don nuna goyon baya ga Ekweremadu. Tun farko, lauyan Ekweremadu, Gavin Irwin ya musanta niyyar cin zarafin yaron da lamarin ya shafa da aka ce wanda yake karewa ya yi.Kazalika, ya ce yaron ya yi ƙarya dangane da yawan shekarunsa, sai…
Read More
Burin ƙasar Sin shi ne “a gudu tare a tsira tare”

Burin ƙasar Sin shi ne “a gudu tare a tsira tare”

Daga SAMINU HASSAN Yayin da ake ci gaba da gudanar da taron ministocin harkokin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar G20, a tsibirin Bali na ƙasar Indonesia, hankula na karkata ga ganawar da manyan jami’an sassan ƙasashe daban daban, mahalarta taron za su gudanar. Cikin irin waɗannan ganawa, akwai wadda aka tsara gudanar ta tsakanin ministan wajen ƙasar Sin Wang Yi, da sakataren wajen Amurka Antony Blinken, a gefen taron mai matuƙar muhimmanci. Masharhanta dai na ganin idan har ana son cimma gajiya daga ganawar sassan biyu, to ya zama wajibi ɓangaren Amurka ya nuna sahihanci, da yin magana ɗaya, ta yadda…
Read More