Editor

9513 Posts
Sakkwatawa sun fi ɗinkin sallah bana fiye da baya – Shugaban Ƙungiyar Teloli

Sakkwatawa sun fi ɗinkin sallah bana fiye da baya – Shugaban Ƙungiyar Teloli

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Yayin da al'ummar Musulmi ke cigaba da gudanar da shagulgulgulan Babbar Sallah bana ta 1443AH, da alamu a sallar ta zo da yanayi na bazata la'kari da irin yadda al'umma ke ƙoƙarin sabunta suturar da za su gudanar da shagulgulgulan Babbar Sallar bana. A cewar shugaban Ƙungiyar Teloli na Jihar Sakkwato, Yusuf Muhammad Bello Tafarkin Taloka, sallar bana ga teloli sai sam-barka. "Alhamdulillah gaskiya yanayin ɗinkin wannan shekarar ya haura na shekarar da ta gabata iya gwargwado kamar yadda kake gani, kamar yadda ake zuwa kara sayen rago haka ake rububin zuwa wajen teloli domin…
Read More
’Yan ta’adda sun harbe kwamandan ‘yan sanda a Katsina

’Yan ta’adda sun harbe kwamandan ‘yan sanda a Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan bindiga sun harbe wani babban Kwamandan 'yan sanda da ke kula da shiyyar Dutsinma, ACP Aminu Umar Dayi, yayin musayar wuta a ƙauyen Yoni da ke Ƙaramar Hukumar Safana a Jihar Katsina.  Rundunar 'yan sanda, wacce ta tabbatar da harin da aka kai wa tawagar tasu a ranar Talata, ta ce ASP Aminu Umar Dayi da wani jami’insu sun rasa ransu a rangamar.  Kamar yadda jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Gambo Isah ya tabbatar wa manema labarai a Katsina, ASP Aminu Umar Dayi ya gamu da ajalisa ne a lokacin da…
Read More
Gwamna Matawalle ya ƙirƙiro Hukumar Tsaron Jama’a a Zamfara

Gwamna Matawalle ya ƙirƙiro Hukumar Tsaron Jama’a a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Bayan shekaru goma ‘yan bindiga na kashe dubban jama’a, tare da karɓar biliyoyin kuɗaɗen fansar waɗanda ake garkuwa da su, Jihar Zamfara ta kafa wata sabuwar Hukumar Tsaron Jama’a, mai suna Community Protection Guard (CPG). Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana sanarwar kafa hukumar tare da fara yi wa matasan da aka fara ɗauka atisayen ba su horon tunkarar gagarimin aikin daƙile hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane. Sanarwar dai ta fito ne daga bakin Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna, Jamilu Birnin-Magaji, a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara. Sanarwar ta ce sabbin jami’an tsaron…
Read More
Harin gidan yarin Kuje: Ana neman ‘yan Boko Haram 33 ruwa a jallo

Harin gidan yarin Kuje: Ana neman ‘yan Boko Haram 33 ruwa a jallo

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce, tana neman 'yan Boko Haram 33 ɗin da suka tsere yayin harin da aka kai gidan yarin Kuje ruwa a jallo. Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Ƙasa (NCoS) ta bayyana cewa, mutum 33 da ake nema fursunoni ne masu alaƙa da ta'addanci kuma mambobin Boko Haram. A ranar Talatar da ta gabata mahara suka kai mummunan hari a gidan yarin na Kuje da ke Abuja, lamarin da ya yi sanadiyar tserewar fursunoni sama da 800 wanda daga cikin mutum 64 masu alaƙa ne da ta'addanci. Waɗanda ake nema ruwa a jallon…
Read More
Malami ya yi ‘wuf’ da ‘yar Shugaba Buhari, Nana Hadiza

Malami ya yi ‘wuf’ da ‘yar Shugaba Buhari, Nana Hadiza

Daga BASHIR ISAH Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari'a, Abukar Malami, ya yi wuf da 'yar Shugaba Buhari, Nana Hadiza. An ɗaura auren ne a Juma'ar da ta gabata a cikin masallacin Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ahalin ɓangaren ango da amarya suka halarta. Da wannan, ya tabbata Nana Hadiza 'yar shekara 41, ta zama mata ta uku a gidan Malami. Sauran 'ya'yan Shugaba Buhari da suka yi aure tun bayan zamansa Shugaban Ƙasa a 2015, sun haɗa da Zahra Ahmed Indimi da Yusuf Buhari da Aisha Mohammed Sha’aban, sai ta baya-bayan Nana Hadiza.
Read More
HOTUNA: Yadda alhazai suka kwana a Muzdalifa

HOTUNA: Yadda alhazai suka kwana a Muzdalifa

Daga MU'AZU HARƊAWA a Saudiyya Bayan kammala tsayuwar Arfah a ranar Juma'a, mahajjata sun dunguma zuwa Muzdalifa inda suka kwana kamar yadda ibadar aikin Hajji ta tanadar. Bayan sallar Asuba ta yau Asabar, sai suka tafi jifar Jamrah daga nan kuma su zarce zuwa masallacin Harami a Makka su yi Ɗawafi da Sa'ayi sannan su koma Muna su jira kwanaki biyu na jifa ta biyu da ta uku da kuma yin hadaya da sauran su.
Read More
Ayyukan da sin ke bada gudummuwar aiwatarwa a Kongo Brazzaville na taka muhimmiyar rawa wajen haɗin gwiwar ƙasashen biyu a fannonin al’adu da kiwon lafiya

Ayyukan da sin ke bada gudummuwar aiwatarwa a Kongo Brazzaville na taka muhimmiyar rawa wajen haɗin gwiwar ƙasashen biyu a fannonin al’adu da kiwon lafiya

Daga CMG HAUSA A watan Maris ɗin shekarar 2013, yayin ziyarar aiki da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya kai Jamhuriyar Kongo, ya halarci bikin ƙaddamar da ɗakin karatu na jami'ar Marien Ngouabi, tare da yanke ƙyalle don murnar kammala aikin gina asibitin sada zumunci tsakanin Sin da Kongo Brazaville. Jami'ar Marien Ngouabi da ke Brazzaville, babban birnin ƙasar Kongo Brazzaville, ita ce jami'ar gwamnati mafi girma a ƙasar, kuma ɗakin karatu na jami'ar da aka gina ƙarƙashin taimakon kasar Sin, shi ne mafi fadi, wanda kuma ke da na’urorin zamani mafi yawa a ƙasar. Asibitin sada zumunta na Sin…
Read More
Ƙasar Sin ta yi kira da a nace kan ra’ayin haɗin gwiwa na haƙiƙa a taron G20 a Indunusiya

Ƙasar Sin ta yi kira da a nace kan ra’ayin haɗin gwiwa na haƙiƙa a taron G20 a Indunusiya

Daga CMG HAUSA Ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya yi kira a yau Juma'a ga ƙasashen duniya a tsibirin Bali na ƙasar Indunusiya, da su tsaya tsayin daka kan haɗin gwiwa tsakanin ɓangarori daban-daban, da raya hulɗa mai inganci a wannan lokaci mai cike da ƙalubaloli. Wang ya bayyana hakan ne a yayin taron ministocin harkokin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar G20 da aka gudanar a tsibirin Bali na ƙasar Indunusiya. Wang Yi ya ce, da farko, ya kamata ƙasashe su kasance abokan hulɗa tare da mutunta juna da tuntubar juna bisa daidaito. Kamata ya yi a tafiyar da…
Read More
Tsohon Shugaban Ƙasar Angola, Eduardo dos Santos ya kwanta dama

Tsohon Shugaban Ƙasar Angola, Eduardo dos Santos ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Bayanai daga Ƙasar Angola, sun ce Allah ya yi wa tsohon shugaban kasar, Jose Eduardo dos Santos rasuwa. Jaridar PM ta ruwaito cewar marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a da misalin ƙarfe 11:10 na safe agogon Spaniya a wani asibitin Barcelona bayan da ya yi fama da rashin lafiya na dogon lokaci. Santos ya mulki Ƙasar Angola na gomman shekaru inda ya bar duniya yana da shekara 79. Fadar Shugaban Ƙasar ta sanar da rasuwar marigayin a shafinta na Facebook, inda ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga kasa da ma duniya baki ɗaya. An…
Read More
Buhari ya ƙaddamar da sabuwar hanyar Nguru-Gashua-Bayamari a Yobe

Buhari ya ƙaddamar da sabuwar hanyar Nguru-Gashua-Bayamari a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da buɗe sabuwar hanyar da Gwamnatin Tarayya ta kammala wadda ta tashi daga Nguru zuwa Gashua ta wuce Baymari tare da miƙa ta a hannun gwamnatin Jihar Yobe a ranar Lahadin makon jiya. Da yake jawabi a madadin Shugaba Buhari a wajen taron buɗe hanyar, Ministan Wutar Lantarki, Abubakar D. Aliyu, ya bayyana aikin hanyar a matsayin ɗaya daga cikin muhimman ayyukan da Gwamnatin Tarayya ta gudanar a faɗin qasar nan domin bunƙasa harkokin sufuri da tattalin arziki a ƙasar nan. Ya ce: “Kamar yadda za ku shaida, za…
Read More