Editor

9513 Posts
Gwamnonin APC na zawarcin Wike

Gwamnonin APC na zawarcin Wike

Daga BASHIR ISAH Yayin da rikicin cikin gida na Jam'iyyar DP ke ƙara ƙamari, ita kuwa jam'iyya mai mulki, APC, na ƙoƙarin yin amfani da wannan dama wajen zawarcin Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da sauransu. An iya fahimtar hakan ne bayan da wata tawagar APC da ta ƙunshi gwamnonin APC da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar suka ziyarci Wike. Gwamnan Legas, Sanwo-Olu da takwarorinsa na Ondo, Rotimi Akeredolu da Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da sauransu, na daga cikin tawagar ta ziyarci Wike ɗin a Juma'ar da ta gabata. Ana raɗe-raɗin cewar dalilin ziyarar shi ne, don zawarcin Wike…
Read More
Jama’a na kokawa da yawaitar tsibirin shara a birnin Kano

Jama’a na kokawa da yawaitar tsibirin shara a birnin Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Yanzu haka dai al'umma musamman a ƙwaryar Birnin Kano na kukawa da irin ɗimbin tarin shara da ta yi latutu a wurare daban-daban ba tare da ana kwashewa akan lokacin da ya kamata ba. Tarin sharar dai ana iya ganinsu a gefen manyan hanyoyi da gefen kasuwanni da tsibi-tsibin tarin sharar a unguwanni da dama, duk kuwa da cewa akwai kamfanin shara da gwamnatin Kano ta yi yarjejeniya da shi ta miqa masa ragamar tsaftace Jihar Kano. Mutane da dama da suka koka sun nuna cewa a halin yanzu da ake ciki ƙazanta ta yi…
Read More
Kwalejin Isa Mustapha Agwai ta Jihar Nasarawa ta rantsar da sabbin ɗalibanta

Kwalejin Isa Mustapha Agwai ta Jihar Nasarawa ta rantsar da sabbin ɗalibanta

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Sama da ɗalibai 700 ne suka ɗauki rantsuwar kasancewa ɗaliban Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Isa Mustapha Agwai mallakar Gwamnatin Jihar Nasarawa dake birnin Lafiya, fadar jihar, wato wadda aka fi sani da Isa Mustapher Agwai Polytechnic a turance a lokacin wani babban bikin ɗaukar rantsuwar wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na makarantar a ƙarshen makon da ya gabata.  A jawabin shugabar makarantar, Dokta Justina Ajiode Kotso ta faro ne da taya sabbin ɗaliban murnar samun damar karatu a makarantar, inda ta ce an kafa makarantar ne da nufin samar da ingantaccen…
Read More
Tinubu ya amince ya ɗauki mataimaki Musulmi – Ganduje

Tinubu ya amince ya ɗauki mataimaki Musulmi – Ganduje

Daga SANI AHMAD GIWA Gwamanna Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu ya amince zai ɗauki Musulmi a matsayin mataimakinsa. Ganduje ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da manyan malaman jihar kusan 100 suka kai kai masa ranar Juma'a a gidan gwamnatin jihar. Gidan talabijin na Channel TV ya ambato gwamnan na cewa, ''mun ba shi shawara ya ɗauki Musulmi a matsayin mataimaki kuma ya amince, saboda ba wani abu ba ne sabo a Nijeriya''. Ya kumna yi kira ga taron malaman da su…
Read More
Kotu ta wanke tsohon shugaban FIFA daga zargin cin hanci

Kotu ta wanke tsohon shugaban FIFA daga zargin cin hanci

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotu a Switzerland ta wanke tsohon shugaban FIFA Sepp Blatter da mataimakinsa Michael Platini kan zargin cin hanci. Blatter, mai shekara 83, ya bai wa Platini wasu kuɗi da suka kai kimanin Swiss francs miliyan biyu, daidai da fan miliyan 1.5 a ranar 18 ga watan Junairun 2011, bayan mako biyu aka tura kuɗin zuwa asusun Platini daga asusun FIFA. Dukkansu dai sun musanta aikata ba daidai ba, inda suka ce kuɗin da aka biya Platini kuɗi ne na wani aiki da ya yi wa FIFA. Bayan bayyana a gaban a yau Juma'a, Blatter ya ce,…
Read More
Gwamna Ganduje ya yi afuwa ga fursunoni 90

Gwamna Ganduje ya yi afuwa ga fursunoni 90

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa fursunoni casa’in afuwa. Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar gidajen gyaran hali ta Nijeriya shiyyar Kano Musbahu Lawan Kofar Nassarawa ya fitar. Sanarwar ta ce, gwamnan ya yi musu afuwar ne a ziyarar bikin Babbar Sallah da ya kai gidan gyaran halin. Kazalika sanarwar ta ce, cikin mutanen da gwamnan ya yi wa afuwa har da mutane goma sha uku da aka yanke wa hukuncin Ƙisa. Musbahu Lawan ya kuma ce gwamna Ganduje ya biya wa mutane saba’i’n da bakwai diyyar…
Read More
Ministan Harkokin Wajen Ƙasar Sin ya gana da Sakataren Harkokin Wajen Ƙasar Amurka a Indinusiya

Ministan Harkokin Wajen Ƙasar Sin ya gana da Sakataren Harkokin Wajen Ƙasar Amurka a Indinusiya

Daga CMG HAUSA Yau ne, ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya gana da sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka Antony Blinken a gefen taron ministocin harkokin wajen ƙasashen G20 a tsibirin Bali na ƙasar Indonesia. Wang ya bayyana cewa, a halin yanzu, dangantakar da ke tsakanin ƙasashen Sin da Amurka na cikin wani mawuyacin hali, wanda gwamnatin Amurka da ta shude ta haddasa, har ma tana kara fuskantar ƙalubale. Babban dalili kuma shi ne, kasar Amurka tana da matsala game da yadda take kallon ƙasar Sin, kuma manufofinta game da ƙasar Sin sun kauce daga hanyar da ta dace.…
Read More
Ƙasar Sin ta yi kira da a warware savanin siyasa a yammacin Afirka da Sahel ta hanyar shawarwari

Ƙasar Sin ta yi kira da a warware savanin siyasa a yammacin Afirka da Sahel ta hanyar shawarwari

Daga CMG HAUSA Mataimakin zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD Dai Bing, yi kira da a gudanar da tattaunawa domin warware sabanin siyasa da ake fama da shi a yammacin Afirka da yankin Sahel. Da yake jawabi a yayin zaman kwamitin sulhu na MƊD game da ofishin MDD mai kula da yammacin Afirka da yankin Sahel (UNOWAS) a ranar Alhamis din da ta gabata, Dai Bing, ya ce tilas ne a ƙara kaimi "don tsayawa tsayin daka kan turba madaidaiciya wajen warware bambance-bambancen siyasa a yammacin Afirka da Sahel ta hanyar tattaunawa." Da yake karin haske kan zabuka a ƙasashen…
Read More
An Gudanar da kwas ɗin horar da ƙwararru masu aiki da alluran gargajiya na Sin karo na farko a Ƙasar Zimbabwe

An Gudanar da kwas ɗin horar da ƙwararru masu aiki da alluran gargajiya na Sin karo na farko a Ƙasar Zimbabwe

Daga CMG HAUSA An gudanar da bikin ƙaddamar da kwas din horar da ƙwararru masu aiki da alluran gargajiya na Sin karo na farko a cibiyar masu kula da alluran dake birnin Harare na ƙasar Zimbabwe, inda likitoci da masu ba da jinya daga wurare daban daban na ƙasar Zimbabwe 20 suka halarci kwas din na tsawon watanni 3, da koyon fasahohin ba da jinya ta alluran gargajiya na Sin, ta yadda za su yayata fasahohin zuwa wurare daban daban na ƙasar Zimbabwe don amfanawa jama’ar ƙasar. Shugaban kula da kwas din kuma shugaban tawagar likitocin Sin dake kasar Zimbabwe…
Read More
Sama da maniyyatabn Kano 900 ne su ka rasa aikin hajjin bana

Sama da maniyyatabn Kano 900 ne su ka rasa aikin hajjin bana

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Sama da maniyyata 900, gami da jami'an Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ne za su rasa aikin Hajjin bana sakamakon matsalar rashin jirgin da zai yi jigilarsu. Manhaja ta rawaito cewa tun da fari, Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta bai wa kamfanin jirgin sama na Azman Air damar jigilar alhazan Kano, su 2,229 zuwa ƙasar Saudiyya. Sai dai kuma Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta qi amincewa da jirgin Azman a bisa hujjar cewa ba shi da girman da zai kwashi alhazai da yawa a lokaci guda. Wannan na zuwa…
Read More