10
Jul
Daga JAMIL GULMA a Kebbi Layya dai wata ibada ce da ta samo asali tun lokacin Annabi Ibrahim (AS), lokacin da Allah (SWT) ya umarce shi da ya yanka abin yankawa ranar 10 ga Zul-Hajji, wanda shi ne watan 12 kuma watan ƙarshe a shekarar Musulunci. Layya ita ce dabbar da ake yankawa, domin neman yardar Allah daga cikin nau'o'in tumaki da awaki da shanu ko kuma raƙuma, waɗanda suka cika shekarun yin layya, kuma sun kuvuta daga kowane aibi. An sharɗanta yanka dabbar layya a ranar 10 ga Zul-Hajji da yini biyu bayan dawowa daga sallar idi bayan kuma liman…
