11
Jul
Daga WAKILINMU A jiya Lahadi ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal ya kai ziyarar ta’aziyya Masarautar Kwatarkwashi game darasuwar sarkin masarautar, Mai Martaba Ahmad Umar Mai Kwatarkwashi. Dauda Lawal wanda shi ne ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, ya kai ziyarar ne da zimmar jajanta wa masarautar da ma al’ummarta bisa wannan babban rashin. Idan dai ba a manta ba, marigayi Mai Martaba Sarki Ahmad Umar Mai Kwatarkwashi ya rasu ne a ranar Alhamis, 9 ga Yunin 2022. Sabon sarkin masarautar, Mai martaba Alhaji Ahmad Garba Bunu ne ya amshi baƙuncin tawagar ta Gamjin Gusau wacce…
