Christophe Galtier ya zama sabon kocin PSG

An naɗa Christophe Galtier a matsayin kocin Paris St-Germain bayan tafiyar Mauricio Pochettino.

Galtier ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyu daga nan zuwa shekarar 2024.

Kocin mai shekaru 55, wanda ya jagoranci Lille ta lashe kofin Ligue 1 a shekarar 2021, shi ne koci na bakwai da PSG ta yi tun bayan da Qatar ta karɓe kulob ɗin a shekarar 2011.

Galtier yana ɗaya daga cikin masu horarwa biyu kacal da suka hana PSG lashe gasar Ligue 1 a shekaru goma da suka gabata, tare da Leonardo Jardim na Monaco a 2016-17.