12
Jul
Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewar, wani taron gaggawa da ya taso a Abuja shi ne dalilin da ya sa Gwamnan jihar, Umar Andullahi Ganduje ya rasa zaman karɓar gaisuwar sallah daga Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar don ƙarin haske kan abin da ya hana Gandujen zaman karɓar gaisuwar basaraken a matsayin wani ɓangare bikin Sallah a Litinin ɗin da ta gabata. Sanarwar ta ce, a wannan rana, Ganduje ya halarci wani taron gaggawa da ya taso…
