Editor

9513 Posts
Yadda aka gudanar da taron ƙaddamar littafin ‘Daular Usmaniyyah’

Yadda aka gudanar da taron ƙaddamar littafin ‘Daular Usmaniyyah’

Daga AMINU AMANAWA a Sokoto Littafin 'Daular Usmaniyya' da ya yi tsokaci sosai kan tarihin daular mafi ƙarfi a nahiyar Afirka da na 'Ma'a Mu'awiyah', ya taɓo tarihi da rayuwar bajimin Malami Mu'awiyah da ma Al-fa'alul Hassan. Ma'ana, fata nagari na daga cikin littafan da matashin malami a Sakkwato Malam Nasirudden Abubakar ya ƙaddamar bayan ɗokar dogon lokaci yana rubuce-rubuce da ma duba litattafan masana. Blueprint Manhaja ta halarci bikin qaddamar da littafan da aka ƙaddamar a makarantar haddar Alƙur'ani da sauran ilmummuka ta Sarkin Musulmi Maccixo da ke Sokoto. Ga kuma tsarabar musamman da Wakilinmu ya yi wa shafinmu…
Read More
Har da kawuna a waɗanda suka nemi gurɓata min rayuwa – Aisha Kallari

Har da kawuna a waɗanda suka nemi gurɓata min rayuwa – Aisha Kallari

"Mata ku cire kunya, ku sanar da iyayenku idan aka ci zarafinku" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Duk da yake ana ɗaukar jinsin mata a matsayin mutane masu rauni, wato raunin jiki da na zuciya, amma ba duk mace ce ta ke da wannan raunin ba. Wasu matan Allah ya ba su zafin nama, kaifin ƙwaƙwalwa, hangen nesa, da ƙarfin zuciya. Suna iya tunkarar kowacce matsala kuma su yi nasarar kawar da ita. Matan da ake cin zarafin su tun suna ƙanana ko wulaƙanta rayuwarsu ta wasu hanyoyi daban daban, sukan fuskanci ƙalubale mai yawa a rayuwarsu, wanda yake jirkita mu…
Read More
Tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya, wai waye yake ƙoƙarin kawo wa ɗalibai cikas?

Tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya, wai waye yake ƙoƙarin kawo wa ɗalibai cikas?

Daga NAFI'U SALISU  Yajin aikin Malaman Jami’o’i ba sabon abu ba ne a Nijeriya, musamman a lokacin da ɗalibai ke ƙoƙarin kammala zangon karatu, ko kuma lokacin da ya kamata a ce sun kama karatun ka’in-da-na’in. Wannan wani al’amari ne da faruwarsa kan sosa rayuka da dama, a ciki har da na iyayen ɗaliban da ‘ya’yansu dake karatu a Jami’a. Hakazalika, a duk lokacin da aka ce Malaman Jami’o’i suna yajin aiki, a kan daɗe ana kai ruwa rana tsakaninsu da Gwamnatin Tarayya, wanda kuma daga bisani a kan samu maslaha a ɗinke bakin zaren domin ɗalibai su dawo makarantu…
Read More
A kiyaye amfani da addini don son zuciya

A kiyaye amfani da addini don son zuciya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Nijeriya na daga cikin ƙasashen duniya na sahun farko da jama'ar ƙasar ta ke da son addini. Wata majiyar ma na cewa, Nijeriya ce ƙasar da mutanen ta ke da tsananin son al'amarin addini. Komai na 'yan Nijeriya sai ka samu addini a ciki, ko da kuwa a sautin ƙarar waya ne, sai ka fahimci ƙarar wayar Musulmi da ta wanda ba Musulmi ba. Muna nuna son junan mu saboda addini, mu taimaki bare saboda addini, mu gujewa ɗan uwa saboda addini. Akwai masu addini na tsakani da Allah, akwai 'yan na gada, 'yan son zuciya…
Read More
Ya kamata ƙasashen Larabawa su ɗauki darasi daga Ƙasar Sin, su daina biye wa ƙasashen yamma

Ya kamata ƙasashen Larabawa su ɗauki darasi daga Ƙasar Sin, su daina biye wa ƙasashen yamma

Daga FA'IZA MUHAMMAD MUSTAPHA Rahoton Arab Barometer da kafar yaɗa labarai ta BBC ta wallafa a baya bayan nan, ya ce ƙasashen Larabawa sun yanke kauna da tsarin demokuraɗiyyar ƙasashen yammacin duniya, saboda yadda tattalin arzikinsu ya yi rauni a ƙarƙashin tsarin. Wannan rahoto ya tuna min da ziyarar da shugaban Amurka zai kai yankin gabas ta tsakiya a cikin wannan mako, wadda ya bayyana a matsayin mai muhimmanci ga tsaron ƙasarsa da kuma neman nasara a takararta da Sin. Amurka ta gaza gane cewa, kan al’umma ya waye, babu wanda ke buƙatar danniya da fifiko irin nata da kuma…
Read More
Xi ya yi murnar kafa ƙungiyar ƙasa da ƙasa kan kafar intanet

Xi ya yi murnar kafa ƙungiyar ƙasa da ƙasa kan kafar intanet

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar kafa kungiyar ƙasa da ƙasa ta tattauna batutuwan da suka shafi kafar intanet. Xi Jinping ya jaddada cewa, kafar intanet na da alaka da makomar bil adama. Kuma Sin ta shirya haɗa hannu da kasa da ƙasa wajen ɗaukar ƙungiyar a matsayin wata muhimmiyar dama ta inganta tabbatar da kafar ta intanet ta kasance buɗɗaɗiya mai cike da tsaro da tabbatar da adalci, kuma mai ƙwari da kuzari, ta yadda jama’a a faɗin duniya za su amfana. An gudanar da taron ƙaddamar da ƙungiyar ne yau,…
Read More
Ƙasar Sin za ta cigaba da taimakawa Sri Lanka iya ƙarfinta

Ƙasar Sin za ta cigaba da taimakawa Sri Lanka iya ƙarfinta

Daga CMG HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya jaddada yayin taron manema labarai na yau Talata cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da taimakawa iya ƙarfinta, wajen kyautata yanayin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasar Sri Lanka. Har ila yau a yau din, Wang Wenbin, ya musanta furucin da babban jami’in ofishin jakadancin Amurka a yankin Hong Kong, Hanscom Smith ya yi game da yanayin yankin, yayin da yake gabatar da jawabinsa na murabus. A cewar kakakin, Amurka ta yi watsi da gaskiya, tana tsokacin da bai dace ba game da manufar shugabanci a HK,…
Read More
Me ya sa maza suke kasa sauke haƙƙin iyalansu?

Me ya sa maza suke kasa sauke haƙƙin iyalansu?

Daga AMINA YUSUF ALI Wai meye ma haƙƙoƙin da suke kan namiji na iyalinsa? Musulunci Addini ne wanda cikin hikima za a ga ya kawo dukkan wasu hukunce-hukunce na zamantakewa. Don haka zaman aure ma bai bar shi a baya ba. Ya tsara haƙƙoƙin mace da miji a aure. Kuma ya jaddada su a cikin Al-Ƙur'ani da hadisai, domin a samu daidaito da fahimtar juna. A cikin haƙƙin da aka ɗora wa mace babba daga ciki shi ne ta yi biyayyar aure. Ta bi mijinta sau da ƙafa tare da ƙauna da tausayawa. Sannan mace ita ke da haƙƙin kula…
Read More
Wani taron ni ke biya kafin a bar ni na yi wasa a wurin – Bilya Kwatarne

Wani taron ni ke biya kafin a bar ni na yi wasa a wurin – Bilya Kwatarne

"Sana'ar barkwanci ke ciyar da matana biyu har ma da 'ya'yana" Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Sakkwato jiha ce daga cikin jihohin da Allah ya albarkata da 'yan wasan gargajiya tun a zamanin baya da su Ɗan Wanzam, Ta rana, 'Yar mai Albasa, Boka Mai Kwankeli da makamantansu har zuwa wannan lokaci da ake samun matasa masu tasowa da ke wasan kwaikwayo na barkwanci domin nishaɗi ko kuma neman abin saka wa a bakin salati. Wakilin Blueprint Manhaja a Sokoto, Aminu Amanawa, ya zanta da Bilya Kwatarne, matashin da ke wasan barkwanci da tauraruwarsa ke haskakawa, yake kuma ci gaba…
Read More
Yadda bikin auren wadda ta auri kanta ya gudana a Indiya

Yadda bikin auren wadda ta auri kanta ya gudana a Indiya

Wata mata a ƙasar Indiya ta kafa tarihi bayan ta yi abin da ake zaton shi ne bikin aure na farko irinsa a ƙasar. Rahotanni sun ce, matar mai suna Kshama Bindu mai shekara 24, ta auri kanta da kanta ne tare da gudanar da bikin auren a gidanta a gaban ƙawaye da abokan aikinta a ranar 8 ga Yunin da ya gabata. Da farko ta shirya yin bikin auren ne a wani wurin bauta tare da wani limamin wurin bautar a birnin Badodara, amma Shugabar Jam’iyyar Bharatiya Janata, Sunita Shukla, ta yi adawa da bikin auren a wurin bautar.…
Read More