Editor

9513 Posts
Kiran Adamu ga Kiristoci: Ku daina fargaba kan tikitin Musulmi da Musulmi

Kiran Adamu ga Kiristoci: Ku daina fargaba kan tikitin Musulmi da Musulmi

*Sabuwar Gwamnatin APC za ta yi muku adalci, inji Shugaban Jam’iyyar Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya shawarci mabiya addinin Kirista da su daina wata fargaba a kan tsayar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa na 2023 a ƙarƙashin tutar jam’iyyar ta APC, wanda ya kasance Musulmi da Musulmi a matsayin shugaba da mataimaki da jam'iyyar ta tsayar ƙarƙarshin takarar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya na mai ba su tabbacin samun cikakken adalci, idan har APC ta sake kafa gwamnati a 2023. Shugaban ya ce, yanayin halin da siyasar ƙasar ke ciki…
Read More
Nasko Ɗakingari da matasa 5,000 sun bar APC zuwa PDP a Kebbi

Nasko Ɗakingari da matasa 5,000 sun bar APC zuwa PDP a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Alhaji Nasiru Nasko Ɗakingari, tsohon ɗan takarar shugabancin Ƙaramar Hukumar Suru a ƙarƙashin Jam'iyyar APC kuma shugaban matasa daga ƙaramar hukumar, tare da matasa sama da 5,000 da ke goyon bayansa, sun bar Jam'iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP ta adawa a Jihar Kebbi. Da ya ke zantawa da wakilinmu a garin Ɗakingari, Alhaji Nasko ya bayyana cewa, ana zaton adalci a APC, amma sai abin ya zama akasin haka wannan ainihi shi ne babban dalilin da ya sanya suka bar jam'iyyar. Ya ƙara da cewa tun da farko sun bayyanawa magoyabayan su da cewa bisa…
Read More
Farashin abinci na cigaba da tashin gwauron zabi a Abuja

Farashin abinci na cigaba da tashin gwauron zabi a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Farashin kayan abinci na ci gaba da tashin gwauron zabi a Abuja da Jihar Nasarawa, inji rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN. Wani bincike da NAN ta gudanar ya nuna cewa a Nasarawa da Babban Birnin Tarayya, mazauna garin na cikin takaici saboda ƙarin farashin kayan abinci. Wani ɗan kasuwa a kasuwar Kubwa, Dini Suleiman ya ce a baya ana sayar da buhun wake kan Naira 27,000 amma yanzu a na sayar da shi kan Naira 49,000. Suleiman ya ce a baya ana sayar da buhun shinkafa 'yar gida tsakanin Naira 15,000 zuwa…
Read More
Hukumar NEDC ta buƙaci matasa su rumgumi sana’ar bola-jari

Hukumar NEDC ta buƙaci matasa su rumgumi sana’ar bola-jari

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Hukumar Raya Shiyyar Arewa maso Gabas (NEDC) ta yi kira ga ɗaukacin matasa marasa ayyukan dake cikin shiyyar da su tsumduma cikin sana’ar bola-jari da zummar rage zaman kashe wando da ya zama katutu a zuƙatan matasan ƙasar nan. Da yake yin jawabi a bikin rufe bita ta kwanaki bakwai wa ‘yan bola-jari guda ɗari dake Jihar Bauchi kan sabbin matakai cin galaba akan sana’ar ta mayar da bola kuɗi, wani mashawarcin hukumar, Dokta Ahmed Sabo ya buƙaci mahalarta bitar da su yi matuƙar amfani da abubuwan da suka koya domin faɗaɗa kasuwancinsu, har ma…
Read More
Dalilin da ya sa muka kai hari kurkukun Kuje – ’Yan bindiga

Dalilin da ya sa muka kai hari kurkukun Kuje – ’Yan bindiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan bindigar da suka kai hari gidan yarin Kuje da ke Abuja ranar Talata, sun bayyana cewa sun kai hari ne don su kuɓutar da mutanensu saboda sun ga shugaban ƙasa yana yi wa gaggan ɓarayi afuwa.  Wata majiya mai tushe ta ruwaito wasu masu tsaron gidan yarin na Kuje suna bayyana cewa sun ji 'yan bindigar suna fadar haka a lokacin da suka kai harin.  Manhaja ta bada rahoton cewa 'yan bindigar sun fitar da mutane kusan 900, yayin da sama 300 suka dawo. Daga ciki, 69 kwamandojin Boko Haram ne.  A lokacin…
Read More
Tsaro: Sarkin Bauchi ya buƙaci ‘yan Nijeriya su lazimci addu’o’i

Tsaro: Sarkin Bauchi ya buƙaci ‘yan Nijeriya su lazimci addu’o’i

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu, ya buƙaci ‘yan Nijeriya su duƙufa wajen gudanar da addu’o’i ga Allah Mabuwayi gagara misali ya kawo ƙarshen matsalolin ta’addanci da suke cusa tsoro da fargaba a zukatun jama’ar ƙasar. Sarkin na Bauchi ya yi kuma kira ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya da cewa, ba tare da la’akari da nasabar addini ko ƙabilanci ba, su cuɗanya da juna cikin zamantakewa, haɗi da guje wa shiga sharo ba shanu da zai haddasa zaman ɗar-ɗar da ban tsoro da za su daƙushe walwalar jama’a. Mai Martaba Rilwanu Adamu, wanda kuma…
Read More
Za a shirya babban taron muhimman al’adun gargajiya na aikin gona na duniya a Ƙasar Sin

Za a shirya babban taron muhimman al’adun gargajiya na aikin gona na duniya a Ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA A shekarar 2002 ne hukumar kula da abinci da aikin gona ta MƊD(FOA) ta gabatar da wata shawara dangane da muhimman al’adun gargajiya na aikin gona na duniya. A bana ne, aka cika shekaru 20 da gabatar da wannan shawara. Daga ranar 17 zuwa 19 ga wata, za a gudanar da babban taron muhimman al’adun gargajiya na aikin gona na ƙasa da ƙasa a gundumar Qingtian ta lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin, babban taken taron shi ne, kiyaye al’adun gargajiya na aikin gona tare da kara azama kan farfadowar yankunan karkara daga dukkan fannoni. Muhimman…
Read More
Ƙasashen yammacin duniya ne suka ƙirƙiro batun tarkon bashin Sin kan ƙasashen Afrika

Ƙasashen yammacin duniya ne suka ƙirƙiro batun tarkon bashin Sin kan ƙasashen Afrika

Daga CMG HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce batun da ake kira da wai tarkon bashi na ƙasar Sin, batu ne kawai da masu adawa da dangantakar Sin da ƙasashe masu tasowa a Afrika da wasu yankuna don gaggauta samun ci gaba, suka ƙirƙiro. Wang Wenbin, ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Laraba. Rahotanni na cewa, wani rahoto da Gidauniyar Debt Justice ta Birtaniya, mai bibiyar harkokin da suka shafi bayar da bashi ba bisa adalci ba, ta fitar, ya zayyano wasu bayanai daga Bankin Duniya da asusun IMF da wasu cibiyoyi,…
Read More
Wadda ta sha ingiza matsalolin abinci a duniya

Wadda ta sha ingiza matsalolin abinci a duniya

Daga LUBABATU LEI Hukumar kula da shirin abinci ta MƊD (WFP) ta yi gargaɗi a kwanan baya cewa, 'yan Adam ka iya fuskantar “matsalar abinci mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu”. Matsalar kuma ta fi yin tasiri ga ƙasashen Afirka. Hauhawar farashin abinci a sakamakon matsalar ƙarancin abinci na matuƙar addabar al’umma, musamman na ƙasashen da ke fama da rashin ci gaba. Amma kuma manyan kamfanonin hada hadar cinikin abinci na duniya na cin muguwar riba sabo da matsalar. Daga cikin manyan kamfanonin cinikin abinci mafiya girma guda huɗu na duniya, wadanda ke shafar kimanin kaso 75% zuwa…
Read More
Yadda taron bada kyaututtuka ga zakarun gasar rubutacciyar waƙa ya gudana

Yadda taron bada kyaututtuka ga zakarun gasar rubutacciyar waƙa ya gudana

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Ƙungiyar Gamayyar Marubuta da Manazarta waƙoƙin Hausa reshen Jihar Kano, ta gudanar da taron bada kyaututtuka ga zakarun gasar rubutacciyar waqa da suka sanya akan Illolin fyaɗe da cin zarafin mata. Taron wanda ya gudana a American Space da ke ɗakin karatu na Murtala Muhammad Laburare, Kano a ranar Lahadin da ta gabata. Gasar mai jigo akan 'Illolin fyaɗe da yadda za a magance su'. An samu 'yan takara guda 15, maza 10, mata 5. Muhammad Lawan PRP shine ya zama zakara da waƙarsa mai suna 'Bulaliya" da maki 235. Sai Nasir Usman Babaye da…
Read More