16
Jul
Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin jihar Ebonyi ta garƙame reshen Bankin GT na garin Abakaliki babban birnin jihar sakamakon rashin biyan haraji. Gwamnatin ta bayyana cewa, ta kulle bankin ne sakamakon qin biyan haraji ga gwamnatin jihar Ebonyi. Kuma ta sha alwashin za ta cigaba da kulle shin har sai ya biya harajin da ake bin sa. Tawagar masu ruwa da tsaki na ofishin hukumar tattara haraji ta jihar sun ziyarci bankin a safiyar ranar Talatar da ta wuce sannan suka ba da umarnin kulle shi a nan take. Shugaban tawagar, Okoro Celestine, wanda shi ne shugaban hadaɗɗiyar hukumar tattara…
