Editor

9513 Posts
Kumbon dakon kaya na Tianzhou-3 na Ƙasar Sin ya rabu da tashar sararin samaniya ta ƙasar

Kumbon dakon kaya na Tianzhou-3 na Ƙasar Sin ya rabu da tashar sararin samaniya ta ƙasar

Daga CMG HAUSA Kumbon dakon kaya na Tianzhou-3, mai dakon kayayyaki zuwa tashar sararin samaniya ta ƙasar, ya rabu da babban ɓangaren tashar na Tianhe a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10:59 na safiya, agogon Beijing, bayan ya kammala dukkan ayyukan da aka tsara zai gudanar. A ranar 20 ga watan Satumban 2021 ne, ƙasar Sin ta yi nasarar harba kumbon Tianzhou-3 daga cibiyar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan na kudancin ƙasar Sin, dauke da kayayyakin da nauyinsu ya kai kimanin ton 6, zuwa tashar ta sararin samaniya. A yanzu haka, kumbon Tianzhou-3 na cikin yanayi mai kyau…
Read More
Ƙasar Sin za ta inganta manufofin taimaka wa dukkan ɓangarorin tattalin arziki

Ƙasar Sin za ta inganta manufofin taimaka wa dukkan ɓangarorin tattalin arziki

Daga CMG HAUSA Biyo bayan koma bayan da aka fuskanta sanadiyyar annobar COVID-19 da sauran matsaloli daga waje, babban bankin ƙasar Sin, zai inganta aiwatar da wasu manufofin kuɗi domin taimakawa dukkan ɓangarorin tattalin arziki. Yayin taro karo na 3 na ministocin kudi na ƙasashen G20 masu ƙarfin tattalin arziki, Gwamnan babban bankin ƙasar Sin Yi Gang, ya gabatar da sabon bayani game da ci gaban tattalin arziki da harkokin kuɗi na Sin yayin taron, yana mai cewa hauhawar farashin kayayyaki na matsakaicin mataki, kuma ana sa ran matakin zai daidaita. Ya ce bankin zai inganta samar da tsarin taimakawa…
Read More
Wang Yi ya jajenta wa Ministan Harkokin Wajen Pakistan game da afkuwar ambaliyar ruwa a ƙasar

Wang Yi ya jajenta wa Ministan Harkokin Wajen Pakistan game da afkuwar ambaliyar ruwa a ƙasar

Daga CMG HAUSA Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya aike da sakon jaje ga takwaransa na ƙasar Pakistan Bilawal Bhutto, kan ambaliyar ruwa da ta afku a ƙasarsa. Wang Yi ya bayyana cewa, ya kaɗu matuƙa da samun labarin cewa, wurare da dama a Pakistan sun fuskanci mummunar ambaliyar ruwa, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi. Ya ce, yana miƙa ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma jajantawa waɗanda suka jikkata, da mutanen yankin da lamarin ya shafa. Ya kara da cewa, gwamnati da jama'ar kasar Sin, za su…
Read More
An horar da matasa masu amfani da zaurukan sada zumunta fiye da 200 a Bauchi

An horar da matasa masu amfani da zaurukan sada zumunta fiye da 200 a Bauchi

Daga ABBA YAKUBU ABUBAKAR a Bauchi A wani ɓangare na bukin cika shekaru biyu da kafuwar ƙungiyar haɗin kan matasan Arewa masu aiki da zaurukan sada zumunta na soshiyal midiya ta Arewa Media Writers ta shirya gudanar da wata gagarumar bita ta wuni biyu a Jihar Bauchi, domin ƙara wayar da kan ýan ƙungiyar dabarun amfani da zaurukan sada zumunta da yadda za su ci moriyar damar da ake samu. Taron wanda aka fara shi da yammacin ranar Jumma'a a babban ɗakin taro na otel din Zaranda ya samu halartar ýaýan ƙungiyar daga dukkan jihohin Arewa, waɗanda suka fara shiga…
Read More
Ƙaruwar kuɗin shigar manyan kamfanonin Sin a rabin farkon bana ta zarce hasashen da aka yi

Ƙaruwar kuɗin shigar manyan kamfanonin Sin a rabin farkon bana ta zarce hasashen da aka yi

Daga CMG HAUSA Rahotannin hukumar kula da kadarorin ƙasa ta majalisar gudanarwar ƙasar Sin sun nuna cewa, karuwar kuɗin shigar manyan kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiyar ƙasar a rabin farko na bana, ta zarce hasashen da aka yi, kuma ingancin ci gabansu yana ƙara kyautatuwa. Jimillar adadin kuɗin shigar manyan kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiya ta ƙasar Sin, ta kai yuan triliyan 19.2, adadin da ya ƙaru da kaso 12 bisa dari a kan makamancin lokacin a bara. Kuma jimillar ribarsu, ta kai yuan biliyan 1409.36, adadin da ya karu da kaso 7.1. Kana adadin ribar da suka samu bayan da suka…
Read More
Masaniyar Kenya: Tattalin arzikin Ƙasar Sin yana da juriya

Masaniyar Kenya: Tattalin arzikin Ƙasar Sin yana da juriya

Daga CMG HAUSA Masaniyar tattalin arziki dake aiki a jami’ar Riala Beatrice ta Kenya, Mathiri-Mysore, ta ce tattalin arzikin kasar Sin yana da juriya, duk da cewa, kasar tana fama da cutar COVID-19 da sauye-sauyen yanayin siyasar duniya. Mathiri Mysore, ta bayyana haka ne yayin da take zantawa da manema labaran kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan. Ta kara da cewa, ƙasar Sin ta gamu da matsala yayin da take fama da yaduwar cutar a wasu sassanta, amma sai ta fitar da manufofi a jere domin daidaita tattalin arzikin cikin nasara. A ganinta, kuɗin shigar yawancin al’ummun ƙasar…
Read More
Ƙasar Sin ta yi kira da a kyautata dokoki domin samun cigaba mai ɗorewa a ɓangaren teku

Ƙasar Sin ta yi kira da a kyautata dokoki domin samun cigaba mai ɗorewa a ɓangaren teku

Daga CMG HAUSA Zaunannen wakilin Sin a MƊD Zhang Jun, ya yi kira da a karfafa kiyaye dokoki a ɓangaren harkokin teku domin bunƙasa samun ci gaba mai dorewa. A cewarsa, tekuna na kyautata rayuwa, kuma suna dauke da albarkatu. Sannan, sun kasance mahaɗar sassan duniya, tare da samar da dandali mai muhimmanci na inganta ci gaba mai ɗorewa. Ya ce a yanzu, tsarin tafiyar da harkokin teku a duniya na fuskantar ƙalubale, kamar gurbatar muhalli da sauyin yanayi, da ƙaruwar matakin teku. Kuma, ƙasa ɗaya tilo ba za ta iya magance wadan nan matsaloli ba, har sai ƙasa da…
Read More
Gwamnatin Kano ta ƙwace gurɓatacciyar fulawa buhu 487

Gwamnatin Kano ta ƙwace gurɓatacciyar fulawa buhu 487

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayen Kaya ta Jihar Kano, KSCPC ta ƙwace kimanin buhun fulawa 487, da ta lalace a wajen ajiyar kaya a kasuwar abinci ta duniya da ke Dawanau da ke birnin Kano. Manajan-Darakta na riƙo a hukumar, Baffa Babba Ɗan'agundi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin hukumar,  Musbahu Yakasai ya fitar a ranar Talata a Kano.  Ɗan’agundi ya ce wasu mutanen kirki ne su ka bai wa hukumar bayanan sirri game da fulawar wacce aka kawo kasuwar da nufin sayar da ita.  Ya ƙara da cewa bayan an kai…
Read More
An gano musabbabin mutuwar tsohon shugaban Angola

An gano musabbabin mutuwar tsohon shugaban Angola

Binciken farko da aka gudanar a Spain, ya nuna cewa, tsohon shugaban Angola, Jose Eduardo dos Santo ya yi mutuwar Allah ne, saɓanin zargin da ‘yarsa ta yi na cewa, kashe shi a aka yi. Dos Santos wanda ya yi wa Angola mulkin kama-karya tsakanin 1979 zuwa 2017, ya mutu ne a ranar Juma’ar da ta gabata a wani asibiti da ke birnin Barcelona, inda ya tare tun a watan Afrilun 2019. An kwantar da dos Santos mai shekaru 79 a sashin kula da marasa lafiya da ke cikin matsanancin hali a asibitin bayan ya gamu da bugun zuciya a…
Read More
An kashe ƙananan yara 2,515 a shekarar da ta gabata – Majalisar Ɗinkin Duniya

An kashe ƙananan yara 2,515 a shekarar da ta gabata – Majalisar Ɗinkin Duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya za ta gudanar da bincike game da kisa da kuma raunin da aka yi wa ƙananan yara a ƙasashen Ukraine da Habasha da Mozambique. Babban Magatakarda na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana haka a cikin wani sabon rahoto da aka fitar, wanda ya gano cewa, ƙananan yara 2,515 ne aka kashe, sannan aka raunata dubu 5,555 sakamakon tashe-tashen hankulan da suka auku a bara.Rahoton na shekara-shekara mai taken ƙananan yara da rikici’ wanda aka wallafa a Litinin ɗin nan, ya kuma tabbatar cewa, lallai yara dubu 6, 310 ne aka tilasta musu taka rawa a…
Read More