Editor

9513 Posts
Gwamnatin Ganduje ta haramta hawa adaidaita sahu bayan ƙarfe 10 na dare

Gwamnatin Ganduje ta haramta hawa adaidaita sahu bayan ƙarfe 10 na dare

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta haramta yin amfani da baburan masu ƙafa uku da aka fi sani da adaidata sahu bayan ƙarfe 10:00 na dare. Hakan na cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Litinin. Sanarwar ta ce, gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin magance matsalar tsaro da jihar ke fama da ita. Muhammad Garba, ta cikin sanarwar ya kuma bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis ɗin makon nan. Kazalika, sanarwar ta buƙaci masu tuƙa baburan na…
Read More
Biden bai cimma yunƙurinsa kan batun yankin Gabas ta Tsakiya ba

Biden bai cimma yunƙurinsa kan batun yankin Gabas ta Tsakiya ba

Daga CMG HAUSA A jiya ne, bayan da shugaban ƙasar Amurka Joseph Biden ya gama ziyararsa a yankin gabas ta tsakiya tare da komawa birnin Washington, manyan kafofin watsa labaru bi da bi suka bayyana ra’ayoyinsu kan wannan ziyara. Kafin ziyarar, shugaba Biden ya taba bayyana cewa, za a buɗe sabon babi kan dangantakar dake tsakanin Amurka da yankin gabas ta tsakiya, amma ya koma ba tare da samun sakamako mai kyau ba. Lokacin da Amurka ta fice daga ƙasar Afganistan cikin gaggawa ba tare da la’akari da muradun kawayenta ba, sannan kuma a lokacin da Amurka ta nuna ɓangaranci…
Read More
Wannan abu ya sa Afirka ta zama abin koyi

Wannan abu ya sa Afirka ta zama abin koyi

Daga BELLO WANG Yau 18 ga watan Yuli rana ce da MƊD ta kebe don tunawa da Nelson Mandela. Idan an ba ni damar takaita ruhin marigayi Mandela da kalma daya, zan zaɓi “Hakuri”. Saboda ya taba bayyana cewa, “Lalata abu na da sauƙi, amma wanda ya duƙufa wajen tabbatar da zaman lafiya shi ne jarumi.” A sabili da ruhinsa na haƙuri, bayan da Mandela ya kammala zamansa na shekaru 28 a gidan kurkuku, kuma ya zama shugaban ƙasa baƙar fata na farko a tarihin ƙasar Afirka ta Kudu, bai nemi yin ramuwar gayya ga mutanen da suka taba cin…
Read More
Yayin da INEC ta tsawaita rajistar masu zaɓe…

Yayin da INEC ta tsawaita rajistar masu zaɓe…

An yi farin ciki sosai a Nijeriya biyo bayan matakin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ɗauka na tsawaita aikin rijistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR). Kamar yadda jadawalin INEC ɗin ya nuna, ya kamata a kawo ƙarshen rijistar masu kaɗa ƙuri’a ne a ranar 30 ga watan Yunin 2022. Sai dai kuma, ba da daɗewa ba ne aka yi ta yin tururuwa a cibiyoyin rajistar don neman yin rajista, lamarin da ya sa cibiyoyin cika da kuma sanya jami’an hukumar aiki ba dare ba rana. Akwai abubuwan da suka sa jinkiri yin rijista ga wasu ’yan…
Read More
Kuna da ‘yancin tsayawa ko barin APC, ba sauran rarrashi – Adamu ya faɗa wa mambobin jam’iyya

Kuna da ‘yancin tsayawa ko barin APC, ba sauran rarrashi – Adamu ya faɗa wa mambobin jam’iyya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya soki fusatattun 'ya'yan Jam'iyyar APC musamman wasu daga cikin mambobin majalisar wakilan Nijeriya da aka ruwaito suna shirin ficewa daga jam'iyyar sakamakon rashin nasararsu a zaɓen fidda gwanin da ya gudana kwanakin baya. Adamu da yake hira a gidan talabijin na Arise, ya bayyana cewa, mambobin jam'iyyar APC ɗin suna da 'yancin cigaba da tsayawa cikin jam'iyyar ko kuma ficewa, inda ya ce babu sauran wani rarrashi ko roƙon mutum ya tsaya a jam'iyyar. Sai dai kuma Adamu ya nuna damuwarsa da yadda wasu mambobin…
Read More
Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta Keffi ta soma jarrabawar neman gurbin karatu

Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta Keffi ta soma jarrabawar neman gurbin karatu

Daga BASHIR ISAH A ranar Alhamis, 14 ga Yulin 2022, Kwalejin Nazarin Kimiyya da Fasahar Kiwon Lafiya ta Jihar Nasarawa da ke Keffi, ta kaddamar da jarrabawar neman gurbin karatu na shekarar 2022/2023 domin bai wa masu sha'awar shiga kwalejin damar da suke buƙata. Dalibai maza da mata daga ciki da wajen Jihar Nasarawa ne suka haɗu a harabar kwalejin da ke babbar hanyar Keffi zuwa Abuja don rubuta jarrabawar. Jarrabawar wadda za a shafe kwana tara ana gudanar da ita, an tsara gudanar da ita ne ta hanyar amfani da kwamfuta kai tsaye, kamar yadda kodinetan shirin, Mista Emmanuel…
Read More
Ƙarar da PDP ta shigar don soke cancantar Tinubu wasan yara ce – Adamu

Ƙarar da PDP ta shigar don soke cancantar Tinubu wasan yara ce – Adamu

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu ya bayyana cewa, ƙarar da jam'iyyar PDP ta shigar don neman soke Tinubu daga takarar shugabancin ƙasar nan a 2023, da ita da wasan yara duk ɗaya ne. Domin ba wani abu ne da ya kasance barazana ga jam'iyyarsu ta APC ba. Jam'iyyar PDP dai ta shigar da wata ƙara a kan hukumar zabe ta ƙasa INEC, da ɗan takarar APC Bola Tinubu, da Dakta Peter Obi a kan yadda suka sauya abokan takararsu na wucin gadi a yayin kuma da suke yin takara da wasu abokan takarar daban.…
Read More
Ba ni da masaniyar kayar da APC a zaɓen Osun – Shugaban APC

Ba ni da masaniyar kayar da APC a zaɓen Osun – Shugaban APC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a ranar Lahadi ya yi ikirarin rashin sanin nasarar ɗan takarar jam’iyyar PDP kuma zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke. Adeleke ya doke ɗan takarar jam’iyyar APC, Gboyega Oyetola a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ƙarshen mako. Rahotanni sun nuna cewa, tun daga lokacin ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya ɗan takarar PDP murna. Sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa ta yi shiru kan sakamakon zaɓen. Da ya ke magana a cikin shirin da ake sa ido a gidan talabijin na Arise, shugaban jam'iyyar APC na…
Read More
Za a sallamo Osinbajo daga asibiti bayan an yi masa tiyata cikin nasara

Za a sallamo Osinbajo daga asibiti bayan an yi masa tiyata cikin nasara

Daga AMINA YUSUF ALI An yi wa mataimaakin Shugaban ƙasar Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo tiyata cikin nasara. Kuma ana sa ran za a sallame shi nan da kwanaki kaɗan bayan ya ƙara jin ƙwarin jikinsa. A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne dai aka yi wa Osinbajo tiyata a cinyarsa wanda tawagar ƙwararrun likitoci suka gudanar a wani asibiti dake yankin Ikejan Jahar Legas. Mai taimaka wa Mataimakin Shugaban ƙasar a fanni yaɗa labarai, Laolu Akande, shi ya ba da wannan bayani a jawabin manema wanda aka wallafa a ranar Asabar. A cikin jawabin, Akande ya bayyana cewa, wasu…
Read More
Yadda PDP ta lallasa APC a zaɓen Osun

Yadda PDP ta lallasa APC a zaɓen Osun

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan takarar gwamnan Jihar Osun a ƙarƙashin Jam'iyyar People Democratic Party (PDP), Sanata Ademola Adeleke ya laahe zaɓe a ƙananan hukumomi 17 a cikin 30 da ke Jihar Osun. Ya lallasa abokin karawarsa na Jam'iyyar All Progressive Congress (APC), kuma gwamnan jihar na yanzu, Adegboyega Oyetola wanda ya samu nasarar cin ƙananan hukumomi 13. Ga dai yadda sakamakon zaɓen gwamnan ya kasance kamar yadda Hukumar INEC ta bayyana a ranar Asabar 16 ga Yuli, 2022. Ƙaramar Hukumar BoluwaduroAPC – 5,649PDP – 5,860Dr. Kehinde Bolarinwa Ƙaramar Hukumar ILESA ta GabasAPC – 13,452PDP – 10,969Farfesa Adepoju…
Read More