19
Jul
Daga CMG HAUSA Jami’in hukumar kula da aikin sadarwar ta ma’aikatar kula da masana’antu da aikin sadarwa ta ƙasar Sin Wang Peng ya bayyana a gun taron manema labarai da aka yi yau Talata cewa, yawan tashoshin sadarwar 5G da Sin ta gina, sun kai miliyan 1 da dubu 854, daga cikinsu ƙarin sabbin tasoshin da aka gina a watannin Afrilu da Mayu da Yuni ya kai kusan dubu 300, matakin da ya tabbatar da cewa, duk wata gunduma na iya kama da sakwani na 5G, yayin da kowane ƙauye ke iya kama layin Intanet. Raya manyan ababen sadarwa, ya…
