Editor

9513 Posts
Gaskiyar zance game da auren biloniya, Nwoko, da ‘yar wasan barkwanci, Emmanuella

Gaskiyar zance game da auren biloniya, Nwoko, da ‘yar wasan barkwanci, Emmanuella

Daga AISHA ASAS A cikin satin da ya gabata ne kafafen sada zumunta suka karaɗe da zancen auren fitaccen mai kuɗin nan na Kudu, Ned Nwoko da kuma sharararriyar 'yar wasan barkwanci Emmanuella Samuel, inda ake yaɗa cewar har an masu baiko, ma'ana Ned ya nemi iznin aurenta har wurin iyayenta. Wannan zancen ya jawo ce-ce-kuce tsakanin masoyan Emmanuella da ke ganin rashin dacewar su da kuma masu kallon iyalin biloniyan wanda a kwanan nan aka haifa ma shi jinjiri, wanda jaruma Regina Daniels ta haifa masa. Sai dai an kasa samun wanda zai fayyace sahihancin wannan zance, don haka…
Read More
‘Yan sanda sun damƙe ƙasurgumin mai safarar miyagun ƙwayoyi a Jigawa

‘Yan sanda sun damƙe ƙasurgumin mai safarar miyagun ƙwayoyi a Jigawa

Daga ABUBAKAR M TAHEER a Jigawa Jami'an 'Yan Sandan Jihar Jigawa sun sanar da damƙe ƙasurgumin mai safarar miyagun ƙwayoyi a ƙaramar Hukumar Auyo. A cikin wata sanarwar manema labarai da Jami'an hulɗa da jama'a na hukumar, SDP Shiisu Adam ya sa wa hannu ya bayyana cewa, sun yi nasarar damƙe matashin ne a Garin su na Auyo. Matashin mai Suna Auwal Muhammad Sani mai shekaru 22, ya bayyana cewa yana samun waɗannan muggan ƙwayoyi ne daga wani mai safarar ƙwayoyin mai suna Sule Kulle da ke ƙauyen Adaha. An samu a tattare da shi ƙullin wiwi guda 265, sai…
Read More
Buhari ya bai wa Ministan Ilimi wa’adin makonni 2 ya warware yajin aikin ASUU

Buhari ya bai wa Ministan Ilimi wa’adin makonni 2 ya warware yajin aikin ASUU

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu da ya warware yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) suka daɗe suna yi tare da kawo masa rahoto nan da makonni biyu. Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a ranar Talata bayan da ya karɓi bayanai daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sassan da abin ya shafa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin ƙungiyoyin jami’o’i. Idan dai za a iya tunawa, ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta shiga yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya a ranar 14 ga watan Fabrairu, sannan sauran ƙungiyoyin ma…
Read More
Shahararren shiri mai dogon zango na Labarina ya kusa dawowa

Shahararren shiri mai dogon zango na Labarina ya kusa dawowa

Daga AISHA ASAS Shahararren fim ɗin nan mai dogon zango na Labarina ya kusa dawowa ga masu kallon finafinan Hausa a Nijeriya da ma ko’ina a faɗin duniya, inda za a fara zango na 5 da kuma na 6 a jere. Darakta kuma shugaban kamfanin Saira Movies, Aminu Saira, ne ya wallafa hakan a farkon makon nan ta kafafen sadarwarsa na zamani, inda ya bayyana cewa, tun da fari kamfanin Saira Movies ya tsara fara sake nuna fim ɗin ne a ƙarshen watan nan na Yuli, amma sakamakon rashin lafiya da wasu daga cikin jaruman fim ɗin guda biyu suka…
Read More
Tugun ‘yan baƙin ciki ba zai kashe mini gwiwa ba – Sadiya Umar Farouq

Tugun ‘yan baƙin ciki ba zai kashe mini gwiwa ba – Sadiya Umar Farouq

Daga WAKILINMU Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa duk wani tugu da 'yan baƙin ciki masu son ganin bayan kyawawan shirye-shiryen inganta rayuwa da gwamnatin Buhari ke yi domin cimma burin 'yanto 'yan Nijeriya marasa galihu miliyan 100 daga ƙuncin fatara zuwa shekara ta 2030 ba zai kashe mata ƙarfin gwiwa ba. Ministar ta bayyana haka ne a martanin da ta yi kan wani rahoto da wasu masu kiran kan su 'APC Initiative for Good Governance', wato Ƙungiyar Tabbatar da Nagartaccen Mulki na APC, su ka bayar inda su ka yi iƙirarin…
Read More
Tattaunawa ta musamman da Sa’in Daular Usmaniyya

Tattaunawa ta musamman da Sa’in Daular Usmaniyya

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato 'Na duƙe tsohon ciniki kuma duk wanda ya zo duniya kai ya tarar!' Wannan ɗaya ne daga cikin kirarin da ake yi wa noma, wacce ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci, rage zaman kashe wando da ma uwa uba bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Sai dai kash, duk da muhimmanci da tasirin da noma ke da shi ga al’umma, rashin ba wa ɓangaren kulawar da ta dace, musamman ma a yankin Arewa dake filin noma, ya sanya qarancin ayukkan ya yawaita a tsakanin ‘yan Arewa, abinci haka, dama sauran ƙalubalen dake akwai. Wakilin Blueprint…
Read More
Kotu ta ba wa Ganduje damar ranto Naira Biliyan 10 don yin kyamarar tsaro

Kotu ta ba wa Ganduje damar ranto Naira Biliyan 10 don yin kyamarar tsaro

Daga AMINA YUSUF ALI Babbar Kotun Tarayyar mai zaman ta a Kano ta yi amanta ta lashe inda ta kore umarnin da ta bayar na hana Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ciyo bashin kuɗi Naira biliyan 10. Ita dai wannan qara Yusuf Iyaka Rabi'u, Darakta Janar na haɗakar ƙungiyoyi masu zaman kansu shi ne ya shigar da ƙarar inda ya nemi kotu ta dakatar da Gwamna Ganduje daga ciyo wancan bashin wanda ya yi ikirarin zai ciyo shi ne don samar da kyamarar tsaro a jihar Kano. Waɗanda aka yi qarar su sun haɗa da, Antoni Janar na jihar Kano,…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Sanatan APC, Ali Ndume ya yi rashin Mahaifi

Da ɗumi-ɗumi: Sanatan APC, Ali Ndume ya yi rashin Mahaifi

Daga AMINA YUSUF ALI Mahaifin ɗaya daga cikin sanatocin Jam'iyyar APC mai wakiltar gundumar Kudancin Borno a Majalisar Dattawa ta Nijeriya, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya riga mu gidan gaskiya. Wannan sanarwar ta rashin mahaifin sanatan tana ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da Sanatan ya yi ranar Talata, 19 ga watan Yuli, 2022 a Abuja. Ɗan majalisar ya bayyana cewa, za a yi jana'izar mahaifin nasa ne Alhaji Ali Buba Ndume, a ranar Talata a garin Maiduguri babban birnin Jihar Borno. Wani sashen na sanarwar ya yi bayani kamar haka: "Muna masu nadamar sanar da rasuwar Alhaji Ali Buba…
Read More
Ƙarya fure take ba ta ’ya’ya

Ƙarya fure take ba ta ’ya’ya

Daga AMINA XU Wasu abokai sun aiko min sako cewa, BBC ta ba da labarai game da ƙasar Sin cewa, tana cin zalun musulmai da tilasta musu aiki a yankin Xinjiang…….Abin baƙin ciki ne ganin yadda Intanet ke bunƙasa matuƙa a karni na 21, amma wasu kafofin yaɗa labarai sun zama wani dandali na yaɗa jita-jita da labarai marasa tushe. A haƙiƙa, kafofin yada labarai na ƙasashen yamma sun sha yaɗa irin waɗannan ƙarairayi game da ƙasar Sin da ma sauran wasu ƙasashe, don neman shafa musu baƙin fenti. Hausawa kan ce, ”Gani ya kori ji”, ba za a kai…
Read More
Ƙwarin tubalin tattalin arzikin Sin yana ƙara wa kamfanonin waje ƙwarin gwiwar zuba jari

Ƙwarin tubalin tattalin arzikin Sin yana ƙara wa kamfanonin waje ƙwarin gwiwar zuba jari

Daga FA'IZA MUSTAPHA Wani rahoton kafar yaɗa labarai ta china Daily ta ƙasar Sin, ya ruwaito a yau Talata cewa, kamfanonin ƙasashen waje na ƙara imani da tattalin arzikin kasar Sin kuma sun ƙarfafa ƙudirinsu na fadada zuba jari a ƙasar Sin. Wannan baya rasa nasaba da ci gaban tattalin arziki da ƙasar ta samu cikin rabin farko na bana, inda ya ƙaru da kaso 2.5. Wannan kuma na da alaƙa da tubali mai kwari da aka gina tattalin arzikin ƙasar a kai. Yayin da ake fama ɓullar annobar COVID-19 da wasu matsalolin duniya, haƙiƙa ƙasar Sin ta yi namijin…
Read More