Editor

9513 Posts
Shin ‘yan ta’adda sun fi ƙarfin jami’an tsaronmu ne?

Shin ‘yan ta’adda sun fi ƙarfin jami’an tsaronmu ne?

Daga SALMAN MUKHTAR A kwanakin baya an kai hare-hare guda biyu da suka ɗauki hankalin mutanen Najeriya, waɗanda sun ƙara fito da asalin ƙarfin 'yan ta'adda da kuma nuna yatsa ga ƙarfin jami'anmu. Hari na farko, shi ne wanda aka kai gidan gyaran hali na Kuje (Abuja), inda waɗannan maciya amanar ƙasa su ka yi ta harbe-harbe tare da ɓalle wannan magarƙama, in da rahotanni suka nuna aƙalla kashi 90% na mutanen da ke ciki sun tsere. A cikin wanda aka nema aka rasa a wannan magarƙama, har da tsohon jami'in ɗan sanda, Abba Kyari, da ake tuhuma da laifin…
Read More
Arewa: Idan jifa ya wuce kanka, ya faɗa kan uban kowa!

Arewa: Idan jifa ya wuce kanka, ya faɗa kan uban kowa!

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN Matuƙar 'yan Arewa suna kan wannan irin batu da fahimtar, ni in har zan amfana ko kuma in har na samu to kowa ya mutu, ko kuma in har na tsira to kowa ya hallaka, to Arewa za tai ta ganin abin baƙin ciki yau da gobe. Irin wannan tunanin ne ke sanya wasunmu ke bin azzaluman 'yan siyasa, saboda in har za su ba su kuɗi, to sauran al'umma su mutu.Har ka ji ana ihu ana cewa "Ruwan da ya dake ka shi ne ruwa" Irin wannan ne ke sanya ka ga mutane sun haɗa…
Read More
Wai me Buhari yake zuwa yi Daura?

Wai me Buhari yake zuwa yi Daura?

Daga RAHAMA ABDULMAJID Abin mamaki ne matuƙa yadda shugaba Buhari ya mayar da zuwa ƙauyensu yawon salla kamar wani rukuni na biyu a shika-shikan Musulunci. Ba zuwansa Salla ko ƙauyen ne ke ci min tuwo a kwarya ba, a'a yadda a matsayinsa na tsohon jami'in tsaro ya san tasirin nuna naƙasu ko jarumta na jagora a idon maƙiya, kuma aka sha shi ya warke a kan hakan. Amma sam taurin kai baya bari ya ɗauki darasi har a kan kansa balle waninsa. A watan Agusta na shekarar 1985, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya tafi Hajji a matsayin Amirul Hajji inda ya…
Read More
Rashin ciyarwa ne ke kai matan aure ga zina – Maryam Nadabo

Rashin ciyarwa ne ke kai matan aure ga zina – Maryam Nadabo

"Kuskure ne kallon mutanen banza da ake wa mata 'yan siyasa" Daga AISHA ASAS Ga dukkan alamu dai mata sun miƙe, sun kuma amince Allah na taimakon wanda ya tashi don neman na rufa wa kai asiri, duk da cewa, su na fuskantar ƙulubale a cikin wasu daga cikin ayyukan da suke zaɓa a matsayin sana'a, ba don komai ba kuwa sai don kasancewar su mata. A wannan satin, shafin Mata A Yau ya yi ma ku babban kamu da yake fatan ya zama barka da salla ga masu bibiyar jaridar Blueprint Manhaja. Fatan Allah ya maimaita. Ba kuwa kowa…
Read More
Taimaka wa jami’an tsaro gano maɓoyar ɓata-gari

Taimaka wa jami’an tsaro gano maɓoyar ɓata-gari

Daga ABBA YAKUBU ABDULLAHI A yayin da na ke wannan rubutu rahotanni na bayyana cewa, kawo yanzu a na cigaba da gano wasu manyan masu aikata laifi da suka tsere daga gidan Gyara Halinka na Kuje da ya ke Abuja, Babban Birnin Tarayya, sakamakon harin da aka ɗora alhakin sa kan ƙungiyar 'yan ta'adda ta ISWAP, waɗanda aka ce sun je ne domin kuɓutar da wasu 'yan uwansu da ke tsare a gidan yarin su kimanin 64. Bayan waɗanda aka je kuvutarwa har da ƙarin wasu vata gari da suka yi amfani da wannan dama suka tsere. A sanarwar da…
Read More
Buhari bai ba wa Ministan Ilimi, Adamu Adamu wa’adin magance yajin aikin ASUU ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Buhari bai ba wa Ministan Ilimi, Adamu Adamu wa’adin magance yajin aikin ASUU ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH Fadar Shugaban Ƙasa ta ce, babu inda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu wa'adin makonni biyu a kan ya magance matsalar yajin aikin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) da ta ƙi ce, ta ƙi cinyewa. Fadar ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da ta fitar ta hannun mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, a ranar Laraba. A Talatar da ta gabata wasu rahotanni suka ce, bayan da Shugaba Buhari ya saurari hukumomin da ke faɗi-tashin ganin an magance wannan yajin aikin, sai ya bai wa Minista Adamu Adamu wa'adin makonni…
Read More
Ƙasar Sin za ta tsaya kan manufar buɗe ƙofarta ga duniya

Ƙasar Sin za ta tsaya kan manufar buɗe ƙofarta ga duniya

Daga CMG HAUSA Firaministan ƙasar Sin mista Li Keqiang ya ce, tattalin arzikin ƙasarsa ya haɗe da na duniya cikin wani matsayi mai zurfi, kana buɗe ƙofarta ga duniya wata babbar manufa ce ta ƙasar. Saboda haka, Sin za ta tsaya kan wannan muhimmiyar manufa, gami da ƙoƙarin inganta harkoki a wannan fanni. Mista Li ya faɗi haka ne a jiya Talata, yayin da yake halartar taron manyan ‘yan kasuwan kasashe daban daban ƙarƙashin laimar dandalin tattauna tattalin arzikin duniya, wanda ya gudana ta kafar bidiyo. A cewar firaministan ƙasar Sin, manufar buɗe kofar kasar ta shafi ƙasashe masu sukuni,…
Read More
Mai dokar barci…

Mai dokar barci…

Daga IBRAHIM YAYA Da alamun ƙasashen da suke iƙirarin kare haƙƙin bil-Adama, su ne kuma suke take wannan haƙƙi ta hanyar kashe fararen hula, waɗanda ba su san hawa ba balle sauka. Wai mai dokar barci ya ɓige da gyangyaɗi. Sanin kowa ne cewa, a kan tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa wasu ƙasashe dake fama da rikici ko tashe-tashen hankula ne, domin su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin wadannan ƙasashe, amma sabanin haka, sai irin waɗannan ƙasashe, har ma gasar kashe fararen hula suka yi a ƙasar Afghanistan. Wani binciken da kafar yaɗa labaran BBC ta gudanar kan…
Read More
An shirya taron farko na ƙaramin kwamitin aikin gona na kwamitin gwamnatocin ƙasashen Sin da Nijeriya

An shirya taron farko na ƙaramin kwamitin aikin gona na kwamitin gwamnatocin ƙasashen Sin da Nijeriya

Daga CMG HAUSA Kwanan baya, aka gudanar da taro na farko na karamin kwamitin aikin gona, na kwamitin gwamnatocin ƙasashen Sin da Najeriya ta kafar bidiyo. A yayin taron, ɓangarorin biyu sun waiwayi nasarorin da aka cimma, a hadin gwiwar da ke tsakanin ƙasashen biyu, a fannonin amfani da fasahohin aikin gona, da cinikayyar noma, da ingancin abinci, da horar da ƙwararru, da kuma manyan ababen more rayuwa da dai sauransu, tare da yin mu'amala sosai kan ƙara sa ƙaimi, ga ciyar da hadin kai mai inganci a ƙasashen Sin da Najeriya gaba. Kana ɓangarorin biyu sun bayyana aniyarsu, ta…
Read More
Za a fara sanya jaruma Sola Sobowale a fim ɗin Indiya

Za a fara sanya jaruma Sola Sobowale a fim ɗin Indiya

Daga AISHA ASAS Fitacciyar jaruma a masana'antar fim ta Kudu wato Nollywood, Sola Sobowale ta yi tsalle mai tsayi, inda ta samu nasarar samun aikin fim daga Ƙasar Indiya. Jarumar wadda aka fi sani daToyin Tomato ce ta bayyana hakan a shafinta na Instagram. Inda ta bayyana tafiyar da zata yi Ƙasar Indiya domin aiki da sananniyar mai shirya fim Hamisha Daryani Ahuja, a wani fim da za a fara aikinsa. "Ina farin cikin sanar da ku cewa, zan yi tafiya zuwa Ƙasar Indiya don aiki tare da shaharariyyar darakta kuma furodusa Hamisha Daryani Ahuja, a aikin fim ɗin da…
Read More