Editor

9513 Posts
Tarihin da Ahmed Musa ya kafa masu wahalar karyawa a Nijeriya

Tarihin da Ahmed Musa ya kafa masu wahalar karyawa a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ahmed Musa, ya fara buga wa Super Eagles ta Nijeriya wasa ne a ranar 5 ga watan Agustan 2010, inda ya shiga wasan ne a canjin Mikel John Obi, a wasan da suka doke Madagascar da ci 2-0 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin AFCON na shekarar 2012. Ya buga gasar AFCON guda uku (2013, 2019 da 2021). Ya samu nasarar lashe guda daya a cikin 2013 AFCON. Sannan ya buga gasar cin kofin duniya guda biyu (2014 da 2018). Musa shi ne ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallaye a ragar Nijeriya…
Read More
Gwamna Sani Bello ya yaba wa sojoji bisa daƙile harin ‘yan ta’adda a Neja

Gwamna Sani Bello ya yaba wa sojoji bisa daƙile harin ‘yan ta’adda a Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yaba wa sojoji da sauran jami’an tsaro bisa gaggawar daƙile harin 'yan ta'adda da suka yi yunqurin kai hari kan Sarkin Pawa, hedikwatar ƙaramar hukumar Munya a jihar ranar Litinin. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, ‘yan ta’addan sun yi yunƙurin kai hari a garin da kuma wani sansanin soji da misalin ƙarfe 2:23 na safe, amma sojoji da sauran jami’an tsaro suka fatattake su. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mary Noel-Berje, ta fitar a Minna, gwamnan ya ce…
Read More
Guguwa ta lalata gidaje da gine-gine 1,300 a Jigawa

Guguwa ta lalata gidaje da gine-gine 1,300 a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Gwamnatin Jigawa ta ce gidaje 1,300 ne guguwar ta lalata a Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa. Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bayar da rahoton cewa, lamarin da ya faru a ranar Talata da daddare, ya yi varna sosai. Mataimaki na musamman ga Gwamna Muhammad Badaru kan ci gaban al’umma da taimakon jama'a, Hamza Muhammad, ya shaida wa NAN a ranar Asabar cewa, sama da gidaje 1,300 ne ibtila'in guguwar ya afkawa, inda wasu suka rushe gaba ɗaya, wasu kuma suka lalace. Muhammad ya ce guguwar ta kuma lalata wasu sassan babban asibitin yankin…
Read More
Kotu a Kano ta umarci matashi ya biya diyyar Naira miliyan 52 bisa raunata wani

Kotu a Kano ta umarci matashi ya biya diyyar Naira miliyan 52 bisa raunata wani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A Juma'ar da ta gabata ne dai wata Kotun Shari'ar Muslunci da ke zamanta a unguwar PRP a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Abubakar Ayuba, ɗan kimanin shekaru 20 da haihuwa da laifin yi wa wani Salisu Usaini mummunan rauni a hannu, har ta kai ga hannun ya ruɓe a ka yanke shi a asibiti. Laifin, a cewar alƙalin kotun, Nura Yusuf Ahmad, ya saɓa wa sashi na 159 na kundin dokar laifuka (Penal Code) ta Jihar Kano. Shi ya sa alƙali Ahmad ya yanke wa mai laifin hukuncin ɗaurin…
Read More
Shugaban Amurka, Joe Biden ya harbu da COVID-19

Shugaban Amurka, Joe Biden ya harbu da COVID-19

Daga BASHIR ISAH Yanzu haka Shugaban Ƙasar Amurka, Joe Biden, na can a killace a Fadar White House bayan da gwaji ya nuna yana ɗauke da cutar Covid-19. Wannan na faruwa ne duk da Shugaban ya karɓi cikakken rigakafin korona, amma duk da haka ya nuna wasu alamu a tattare da shi, kuma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa inji sakatariyar yaɗa labarai, Karine Jean-Pierre. A wani saƙon Tiwita da ya wallafa, Shugaba Biden ya ce yana lafiya kuma yana ci gaba da gudanar aikinsa. Sai dai kuma, mai ɗakinsa Jill Biden ta ce, an gwada ta an kuma…
Read More
Yar shekara 64 ta lashe zaɓen Shugabar Ƙasar Indiya

Yar shekara 64 ta lashe zaɓen Shugabar Ƙasar Indiya

Daga BASHIR ISAH Rohotanni daga Ƙasar Indiya sun ce, Droupadi Murmu 'yar shekara 64 daga ƙabila mara rinjaye, ta lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar. Bayanai sun nuna Droupadi ta lashe zaɓen ne a ranar Alhamis, 21 ga Yulin 2022 tare da goyon bayan jam'iyya mai mulki. Wannan nasarar ta sa Droupadi zama mutum na farko da zai taɓa riƙe wannan muƙami daga al'ummar da ake nuna wa wariya a ƙasar. Wani ɓangare na sakamakon da hukumar zaɓen ƙasar ta fitar ya nuna Droupadi wadda 'yar asalin ƙabilar Santhal ce, ta samu goyon bayan da yawan 'yan jam'iyyar MP…
Read More
Abun da aka shuka shi za a girba!

Abun da aka shuka shi za a girba!

Daga SAMINU HASSAN Wani sakamakon bincike na jin ra'ayin alumma, da jaridar The Guardian ta Amurka ta wallafa a baya bayan nan, ya nuna yadda duk cikin Amurkawa biyar, ɗaya daga cikinsu ke ganin abu ne mai kyau, a cimma burin siyasa ta hanyar tarzoma. Ko shakka babu hakan abun tsoro ne, da tayar da hankali, ganin cewa wannan tunani ya yi hannun riga da ainihin tushen dimokaraɗiyya, wanda ya tanadi cimma duk wani buri ta maslaha da kwanciyar hankali. Wani abun lura game da wannan bincike, shi ne yadda Amurkawa ke saurin yarda da farfagandar ’yan siyasa, wadda ke…
Read More
Moussa Faki Mahamat: Hulɗar Afrika da Sin abin koyi ne

Moussa Faki Mahamat: Hulɗar Afrika da Sin abin koyi ne

Daga CMG HAUSA Shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar tarayyar ƙasashen Afrika ta AU, Moussa Faki Mahamat, ya bayyana a jiya Laraba cewa, hulɗar dake tsakanin AU da ƙasashen Afrika da Sin abin koyi ne a wannan zamani. A kuma jiya, Moussa Faki Mahamat ya karɓi takardar aiki na sabon shugaban tawagar Sin a ƙungiyar, kana jakada na musamman, a hedkwatar AU dake birnin Addis Ababan ƙasar Habasha, Hu Changchun. Moussa Faki ya darajanta dadadden zumuncin dake tsakanin Afrika da Sin, da kuma ci gaban da ɓangarorin biyu suka samu a hadin kansu, yana mai jaddada cewa, huldar dake tsakanin AU da…
Read More
Amurka ba za ta iya ɓata sunan Xinjiang ba

Amurka ba za ta iya ɓata sunan Xinjiang ba

Daga CMG HAUSA A kwanakin nan ne, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta gabatar da abin da ake kira wai "ƙudirin dokar daƙile kisan kiyashi da ta’adanci" ta shekarar 2022, rahoton da ta saba fitarwa a kowace shekara ga majalisa, ta kuma ba da "Dabaru na hasashe, neman hanawa, da yin raddi ga ayyukan ta'addanci" a tarihin Amurka. Inda aka sake sanya batun "kisan ƙare dangi" da batun "sanya aikin tilas" da sauran batutuwa da suka shafi yankin Xinjiang na kasar Sin a cikin rahoton. Rahoton na shekara-shekara na shekarar 2022, wanda ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta gabatar, ya ci gaba…
Read More
Gaskiya ɗaya ce: Buhari ba shugaban ƙasa ba ne, ministan harkokin ƙasashen wajen Nijeriya ne

Gaskiya ɗaya ce: Buhari ba shugaban ƙasa ba ne, ministan harkokin ƙasashen wajen Nijeriya ne

Daga LARABI LARABEEN Idan da Shugaba ne ba zai shirya tafiya cikin abinda ko awa goma sha biyu ba a yi ba da kai wa tawagar masu tsaren lafiyarsa ba. Kuma har an samu asarar rayukan jama'a a cikinsu. Idan da Shigaba ne ba zai tsallake zuwa wata ƙasar ba cikin abinda bai wuce awa goma sha biyu da kai hari babban gidan gyaran hali na Kuje inda fursunoni kusan 600 suka tsere daga gidan bayan harin da aka kai. Idan da Shigaba ne ba zai samu sukunin tafiyar ba. Bayan abinda bai kai ko sati guda ba daga dawowarsa…
Read More