23
Jul
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ta tabbata cewar Kano Pillars ta faɗi daga gasar Firimiyar Nijeriya bana a karo na uku a tarihin ƙungiyar. Tun farko ƙungiyar da aka kafa a 1990 ta faɗi daga gasar Firimiyar ƙasar a shekarar 1994 da 1999. Ƙungiyar da ake kira sai masu gida wadda ta lashe kofin babbar gasar tamula ta Nijeriya karo huɗu ba za ta buga kakar da za a yi ta 2022/23 ba. Ƙungiyar tana da daɗaɗɗen tarihi a fagen taka leda a ƙasar da Afirka, wadda ta samar da fitattun 'yan wasa masu magoya baya da yawa. Shugaban marubuta labarin…
