Editor

9513 Posts
Fifita ilimin boko a kan na addini

Fifita ilimin boko a kan na addini

Duniya ina zaki damu? A haƙiƙanin gaskiya wannan rayuwa mun kai wani mataki da iyaye da kansu ke nuna wa ’ya’yansu duniya ta fi lahira. Wannan kuma ba ƙaramin ƙalubale ba ne gare mu Musulmi. Sakamakon hakan, ya sa yara za su taso da sangarta, rashin tarbiyya, ga rashin kula da addinin Allah. A haka kuma za ku ga ko sallah ma ba ta dame su ba, kuma ba su ɗauki iyayensu a bakin komai ba. Me ya jawo hakan? A wani ɓangaren kuma ku dubi amfanin ilimantar da 'ya mace. A wannan yanayin da muke ciki kashi casa’in 90%…
Read More
2023: Zaɓen Shettima a matsayin mataimakin Tinubu daidai ne – NPCF

2023: Zaɓen Shettima a matsayin mataimakin Tinubu daidai ne – NPCF

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa farar dabara ce zaɓen da Bola Tinubu ya yi wa Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a babban zaɓen 2023. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da shugaban ƙungiyar kansiloli na ƙasa (NPCF), Honarabul Muslihu Yusuf Ali, mai wakiltar gundumar Gurungawa, Kumbotso, Jihar Kano ya fitar a ranar Asabar. Ali ya ce, nasarar da Tinubu ya samu na zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na APC na 2023, abu ne da babu makawa. Ya ce dukkanin 'yan takarar sauran jam'iyyu babu wanda zai iya karawa da Tinubu saboda ya…
Read More
Litar fetur sai yadda hali ya yi

Litar fetur sai yadda hali ya yi

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Yanzu dai an haƙiƙance tsadar litar man fetur sai yadda hali ya yi a Nijeriya tun da gaba ɗaya a hukumance gwamnati ta miƙa ragamar kasuwancin kamfanin fetur NNPC a hannun 'yan kasuwa. Ka ga ba sauran wanda za a yi wa ƙorafi don an ga litar fetur ta yi tsada. Dama an ɗauka cewa lamarin zai inganta bayan ganin gidajen mai a jihohi na sayar da fetur kan Naira 190 har ma an samu inda su ka sayar Naira 225 maimakon Naira 165 da a ka sani. Gaskiya ni ma sai da na lura na…
Read More
Illolin shaye-shayen ƙwayoyi da hanyoyin shawo kan lamarin

Illolin shaye-shayen ƙwayoyi da hanyoyin shawo kan lamarin

Shaye-shaye ya zama ruwan dare a tsakanin al'umma musamman ma matasa maza, wanda babban abin takaici halayya ce da aka fi dangantawa ga maza, sai ga shi ta zama ruwan dare har mata sun fi maza iyawa. Masu aure da waɗanda ba su da shi shaye-shaye na nufin duk wani yanayin da ɗan adam zai sa kan shi don sauya yanayin tunaninsa ko nazarin shi ta yadda ba zai iya bambanta ya kamata da akasin hakan ba. A zamanin baya, sai dai mu ji labarin irin wannan ɗabi’ar a wasashen ƙetare, wasa-wasa har ta shigo cikin ƙasarmu da al’ummarmu. Da…
Read More
Yunwa ba Dimukuraɗiyya ba ce

Yunwa ba Dimukuraɗiyya ba ce

Daga BELLO WANG Kamfanin watsa labarai na BBC, ya watsa wani labari a kwanan nan, wanda ke cewa jama’ar ƙasashen Larabawa, suna yanke ƙauna ga tsarin dimokuradiya irin na ƙasashen yamma. A ganinsu, tsarin ya hana gwamnati taka rawa yadda ake bukata, a fannonin tabbatar da tsaro da raya tattalin arizki. BBC ya watsa labarin ne, bisa rahoton da ƙungiyar binciken ra’ayin jama’a ta Arab Barometer ta gabatar, wanda Michael Robbins, shehun malami na jami’ar Princeton ta ƙasar Amurka, ya wallafa. Shi kuma wannan malami ya rubuta dalilin da ya sa Larabawa suke yanke kauna ga tsarin dimokuraɗiyya na ƙasashen…
Read More
Shugabannin JKS da na Ƙasar sun karɓi allurar rigakafin COVID-19 wadda aka sarrafa a ƙasar

Shugabannin JKS da na Ƙasar sun karɓi allurar rigakafin COVID-19 wadda aka sarrafa a ƙasar

Daga CMG HAUSA Mataimakin shugaban hukumar kiwon lafiya ta ƙasar Sin Zeng Yixin, ya ce shugabannin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, da jagororin ƙasar sun karɓi allurar rigakafin COVID-19 da aka sarrafa a cikin ƙasar. Zeng ya bayyana hakan ne a Asabar din nan, yayin taron manema labarai na tsarin haɗin gwiwar kandagarki da shawo kan annoba na majalissar gudanarwar ƙasar Sin, yana mai cewa "Hakan ya nuna amincewar da rigakafin COVID-19 samfurin ƙasar Sin ya samu”. Kazalika, ƙarin wasu shugabannin ƙasashen duniya sama da 30, sun karɓi rigakafin samfurin na ƙasar Sin.” Jami’in ya ƙara da cewa, akwai nau’o’in…
Read More
Shugaba Xi ya taya Ƙasar Masar murnar cika shekaru 70 da kafuwarta

Shugaba Xi ya taya Ƙasar Masar murnar cika shekaru 70 da kafuwarta

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da saƙon taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar ƙasar Masar, ga takwaransa na Masar ɗin Abdel-Fattah al-Sisi. Cikin saƙon wanda ya aike a Asabar ɗin nan, shugaba Xi ya ce Masar ta ci gaba da bin hanyar nasara bayan samun ‘yancin kai, ta kuma samu bunƙasuwa, tare da taka muhimmiyar rawa a harkokin da suka shafi ƙasa da ƙasa da na shiyyoyi. Shugaban na Sin, ya ce ƙasar sa na mayar da hankali matuƙa ga bunƙasa alakar ta da Masar. Ya ce a shirye yake ya yi aiki tare…
Read More
Ganduje ya bai wa ɗan Kano tallafin karatu miliyan N3

Ganduje ya bai wa ɗan Kano tallafin karatu miliyan N3

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Kano, Umaru Abdullahi Ganduje, ya bada tallafin karatu na kuɗi Naira miliyan N3 ga wani matashin jihar, Suyudi Sani, saboda bajintar da ya nuna a jarrabawar neman shiga jami'a da hukumar JAMB ta saba shiryawa inda ya zama ɗalibin da ya fi kowa samun maki bayan da ya samu maki 303. Gwamnatin Kano ta miƙa wa matashin cekin kuɗin ne ta hannun Kwamishinar Manyan Makarantun Jihar, Dakta Mariya Mahmud Bunkure, kuma tuni ya samu gurbin karatu a Jami'ar Bayero da ke Kano (BUK), inji Kwamishinar. Mariya ta ƙara da cewa, Suyudi ya nuna bajinta a…
Read More
HOTUNA: Sanata Adamu ya cika shekara 76

HOTUNA: Sanata Adamu ya cika shekara 76

Daga BASHIR ISAH Jiga-jigan 'yan siyasa daga ciki da wajen Jihar Nasarawa na ci gaba da miƙa saƙon taya murna na cika shekara 76 da haihuwa, ga Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu (Turakin Keffi). Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule bai bari an baro shi baya ba wajen taya jigon siyasar murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bi shi har gidansa da ke Keffi ya miƙa masa katin taya murna.
Read More
Bankin UBA zai fara harkokinsa a ƙasar Dubai

Bankin UBA zai fara harkokinsa a ƙasar Dubai

Daga AMINA YUSUF ALI Bankin UBA ya faɗaɗa harkokinsa, inda har yanzu haka ya bude sabon reshensa a haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (Dubai). Shi dai wannan reshe na UBA an buɗe shi ne a cibiyar hada-hadar kuɗin ta qasar Dubai (DIFC). Sannan ya samu lasisin fara hada-hadar sa, kuma humakar saita al'amuran kuɗin na Dubai (DFSA), shi zai cigaba da gudanar da da al'amuran bankin. Wannan faɗaɗa harkokinsa da bankin UBA ya yi ana ganin zai qara sa wa ya samu qarin damarmaki a gabas ta tsakiya, Afirka, da Asiya ta kudu, wanda ya ƙunshi ƙassashe 72 tare da ƙiyasin alumma…
Read More