Editor

9513 Posts
Adadin motoci masu amfani da sabon makamashi ya zarta miliyan 10 a Sin

Adadin motoci masu amfani da sabon makamashi ya zarta miliyan 10 a Sin

Daga CMG HAUSA Rahoton ma’aikatar tabbatar da kwanciyar hankalin jama’a ta ƙasar Sin ya nuna cewa, ya zuwa ƙarshen watan Yunin bana, jimillar adadin motocin ƙasar ya kai miliyan 406, inda daga cikinsu, motocin dake amfani da sabon makamashi mai inganci suka kai fiye da miliyan 10.01. Kaza lika adadin sabbin motocin dake amfani da sabon makamashi da aka yi rajista a cikin watanni shida, na farkon shekarar bana a faɗin ƙasar, ya kai miliyan 2 da dubu 209, adadin da ya ƙaru da miliyan 1 da dubu 106, bisa na makamancin lokacin bara, wato ya ƙaru da kaso 100.26…
Read More
Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin ta yaba wa China Daily saboda bincike tare da gabatar da bayanai game da jita-jitar da wata hukumar Birtaniya ta bayar kan batun Xinjiang

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin ta yaba wa China Daily saboda bincike tare da gabatar da bayanai game da jita-jitar da wata hukumar Birtaniya ta bayar kan batun Xinjiang

Daga CMG HAUSA Yayin taron manema labarai da aka yi yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian ya yaba wa kafar watsa labarai ta ƙasar Sin wato China Daily, bisa yadda ta yi bincike tare da gabatar da bayanai game da jita-jitar da wata hukumar ilmi ta ƙasar Birtaniya ta bayar kan jihar Xinjiang, inda ya jaddada cewa, ko da yake an shirya jita-jitar kamar gaskiya, ba wani abu ba ne face zargi mara tushe. Rahotanni na cewa, tun daga watan Mayun shekarar 2021, cibiyar Helena Kennedy ta jami’ar Sheffield Hallam ta Birtaniya, ta gabatar da rahotanni 4…
Read More
Bikin Sallah: Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun kwana Biyu

Bikin Sallah: Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun kwana Biyu

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bayyana Litinin, 11 da Talata, 12 ga Yuli, 2022 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Babbar Sallah. Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya a ranar Alhamis, mai dauke da sa hannun Babban Sakataren ma’aikatar, Shuaib Belgore. “Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin 11 da kuma Talata 12 ga Yuli Julin 2022, a matsayin ranakun hutu don gudanar da bukukuwan Babbar Sallah," kamar yadda ma'a'ikatar ta wallafa a shafinta na Tiwita. A ranar Asabar mai zuwa ake sa ran al'ummar Musulmin…
Read More
Duk marubucin zube zai iya rubuta fim – Zubairu Balannaji

Duk marubucin zube zai iya rubuta fim – Zubairu Balannaji

"Rubutu baiwa ne, ba a yi masa ci-da-ƙarfi" Daga AISHA ASAS Sanannen matashin marubuci da duniyar rubutu ta ba shi aron lokaci tare kuma da mallaka masa damar yawo cikin lungu da saƙon da ke cikin ta, kasancewar sa ba kawai marubucin zube ba har ma na finafinai. Zubairu M. Balannaji, haziƙin marubuci ne da ke cikin zaratan marubuta da ke ƙoƙarin ganin sun ciyar da harkar rubutu kai har ma ta finafinai gaba. Mai karatu zai amince da zance na ne idan ya yi duba da littafansa da suke kewaye a gidajen ma'abuta karatu tare kuma da shahararren fim…
Read More
Masanan ƙasa da ƙasa sun amince da sakamakon Sin a fannin kare haƙƙin bil Adam

Masanan ƙasa da ƙasa sun amince da sakamakon Sin a fannin kare haƙƙin bil Adam

Daga CMG HAUSA A jiya Talata ne aka kira taro mai taken “Kara ƙarfafa aikin gudanar da harkokin haƙƙin dan adama, domin kare hakkin bil adama yadda ya kamata” na hukumar kare haƙƙin dan adam ta MƊD karo na 50 ta kafar bidiyo, inda masana mahalartan taron suka yi tattaunawa mai zurfi kan batun, da yadda za a tafiyar da harkokin kare haƙƙin dan adam a faɗin duniya. Yayin taron, malamin ilmin siyasa na jami’ar Buea ta ƙasar Kamaru Hassan Njoya, ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, ƙasashe masu tasowa suna fuskantar ƙalubale a fannoni guda biyu,…
Read More
Jayland Walker da aka harbe shi har lahira

Jayland Walker da aka harbe shi har lahira

Daga AMINA XU Abokai, “duniya a zanen MINA” yau na yi zane game da dalilin rasuwar wani saurayi baƙar fata mai suna Jayland Walker. A makon jiya, ‘yan sanda 8 sun harbe shi har lahira da harsasai fiye da 60 a birnin Akron na jihar Ohio dake ƙasar Amurka, Jayland Walker mai shekaru 25 a duniya ya rasu sakamakon nuna bambancin launin fata da amfani da ƙarfin tuwo, waɗanda ke daga cikin matsalolin dake dabaibaye al’ummar Amurka matuƙa. Mai zane: Amina Xu
Read More
Mu gani a ƙasa…

Mu gani a ƙasa…

Daga IBRAHIM YAYA A kwanakin baya ne, aka kammala taron kolin shugabannin ƙasashen Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da Afirka ta Kudu (BRICS). Duk da cewa taron ya gudana ta kafar bidiyo, amma hakan bai hana shi cimma manyan sakamako da zai amfanawa ƙasashen da ma duniya baki ɗaya ba. A duk lokacin da aka ambaci ƙungiyar, abin da mutum zai yi tunani shi ne, yadda manufofi da tsare-tsarenta za su amfani ɗaukacin bil-Adama. Bayanai na nuna cewa, haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasashen ƙungiyar BRICS ya kai matsayin koli, har ma an samu muhimman nasarori 10 a ɓangarori…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya rantsar da sabbin ministoci

Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya rantsar da sabbin ministoci

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa majalisarsa garambawul a ranar Laraba yayin da ya rage wata bakwai kafin zaɓen 2023. Kazalika, Shugaban ya rantsar da sabbin ministoci guda bakwai waɗanda Majalisar Dattawa ta amince da naɗinsu kwanan nan. Bayan rantsar da su, Buhari ya yi kira ga sabbin ministocin da su ɗauki wannan muƙami da suka samu a matsayin wata dama ta yi wa ƙasa aiki bilhaƙƙi. Sabbin ministocin da aka rantsar ɗin sun haɗa da; Henry Ikoh (Abia), Umana Okon Umana (Akwa-Ibom), Udi Odum (Ribas), Ademola Adegoroye (Ondo), Umar Ibrahim El-Yakub (Kano), Goodluck Nana Opiah…
Read More
Sharhi: Laifin wani ba ya shafar al’umma duka

Sharhi: Laifin wani ba ya shafar al’umma duka

Daga LUBABATU LEI Xiaozhong Johnny wani mai wallafa bidiyo ne a shafin sada zumunta, wanda ya dan yi suna a ƙasar Sin. Xiaozhong ya fara zuwa Afirka ne sama da shekaru biyu da suka wuce, kafin daga bisani ya zauna a birnin Lome, babban birnin ƙasar Togo. Kamar yadda matasan yanzu suke yi, Xiaozhong shi ma ya kan dauki hotunan bidiyo iri na “Vlog” bisa ga harkokin rayuwarsa na yau da kullum a Afirka, sa’an nan ya wallafa su a shafukan sada zumunta bisa sunan Xiaozhong Johnny, sai dai bai yi zaton hakan zai sa ya samu dimbin masu bibiyarsa…
Read More