Editor

9513 Posts
An kai hari kurkukun Kuje da ke Abuja

An kai hari kurkukun Kuje da ke Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari Cibiyar Kula Da Tsaro Ta Kuje da bama-bamai a daren ranar Talata. Majiyoyi sun ce, ana ci gaba da harbe-harbe da ƙarar fashewar abubuwa a kusa da wurin, wanda ke wani yanki da ake kira Shetuko a ƙaramar hukumar Kuje. Har zuwa lokacin da ake wannan rahoto, ba a tabbatar da ainihin musabbabin faruwar lamarin ba, amma majiyoyin da ke kusa da wurin sun ce wataƙila harin ta'addanci ne. Da aka tuntuɓi Mataimakin Sufeto Janar na ’yan sanda (AIG), shiyya ta 7 a…
Read More
’Yan bindiga sun kai wa tawagar Shugaba Buhari hari a Katsina, sun jikkata biyu

’Yan bindiga sun kai wa tawagar Shugaba Buhari hari a Katsina, sun jikkata biyu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu gungun ’yan bindiga sun buɗe wuta kan ayarin motocin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da aka tura domin tattaki zuwa Daura, jihar Katsina domin gudanar da bukukuwan Sallah a ranar Talata. Da ya ke mayar da martani ga wannan lamari a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, mai taimaka wa Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya yaba wa jami'an tsaron Fadar Shugaban Ƙasa kan nasarar daƙile harin. “Fadar shugaban ƙasa ta bayyana harin a matsayin abin baƙin ciki da rashin jin daɗi, lamarin harbin da ya faru a kusa da Dutsinma, jihar Katsina, a…
Read More
Sakatare Janar na OPEC, Barkindo ya kwanta dama

Sakatare Janar na OPEC, Barkindo ya kwanta dama

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sakatare-Janar na Ƙungiyar Ƙasashe Masu Fitar da Man Fetur OPEC, Muhammad Sanusi Barkindo, ya riga mu gidan gaskiya.Barkindo ya rasu a ranar Talata da misalin ƙarfe 11 na dare yayin da yake da shekaru 63 a duniya kamar yadda Mele Kyari ya sanar. Barkindo shine tsohon GMD na NNPC na uku da ya rasu cikin shekaru biyu bayan Maikanti Baru da Joseph Dawha. Mele Kyari, Manajan-Daraktan Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPC, ya bada sanarwar mutuwarsa a wallafarsa ta Tiwita a sa'o'in farko na ranar Laraba. Ya kuma kwatanta rasuwarsa da babban rashi ga…
Read More
Tarihin Marigayi Abubakar Tafawa Ɓalewa

Tarihin Marigayi Abubakar Tafawa Ɓalewa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa, mutum ne mai haƙuri, ladabi da biyayya, son haɗin kai tare kuma da cikakken kishin qasa wanda ya yi faɗa da zalunci. Mutum ne shi mai kunya, marar yawan magana, mai tsantseni da kuma gudun duniya. Tafawa Ɓalewa, Fasihi ne kuma haziƙin mutum ne wanda Allah ya ɗaukaka shi a duniya. Shi ne mutumin da duniya ta yi wa laƙabi da Mai Maƙogwaron Zinaren Afirka, wato ‘Golden Voice of Africa’ a Turance saboda zunzurutun iya maganarsa a gaban jama’a. Malamin makaranta ne shi, marubuci, manomi, sannan kuma ɗan siyasa. Ya bayar da…
Read More
Masu iya sayen bindiga a Zamfara da sauran garuruwa don kare kansu

Masu iya sayen bindiga a Zamfara da sauran garuruwa don kare kansu

Daga MUS'AB ISAH MARAFA Wannan dama da Gwamnatin Zamfara ta ba wa 'yan jiha wani cigaba ne daga inda ake yanzu. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce cikin wani Hadisin Tirmizi "wanda aka kashe wurin kare dukiyarsa ya yi shahada. Wanda aka kashe wurin kare addininsa, ya yi shahada; wanda aka kashe wurin kare jininss ya yi shahada; wanda aka kashe wurin kare iyalinsa ya yi shahada." Musulunci bai yarda ka tsaya wani ɗan iska ya wulaqanta ka ya wulaƙanta iyalinka don kawai yana da bindiga, ko da ko kai ba ka da bindiga balle a ce kana da…
Read More
Wa masu gidajen biredi za su yi wa yajin aiki?

Wa masu gidajen biredi za su yi wa yajin aiki?

Daga SALMAN MUKHTAR A yau na tsinci wani labari daga kafar sadarwa ta BBC Hausa akan yajin aikin da ƙungiyar masu Gidan Biredi watau (Association of Master Bakers and Caterer Of Nigeria), ke shirin shiga a satin nan sakamakon tsadar fulawa da kayan haɗi. Al'amarin yajin aikin nasu ya gicciyar da tunanina da na wasu ire-irena a kan wa za su yi wa? Gwamnati, da ba ta da gonar noma, ba ta da alkama, ba ta da kamfanin fulawa, ba ta da gidan biredi, a ƙarshe ba ta da bakin magana ballantana ta sa baki a sassauta muku? 2.Masu noma…
Read More
Tsakanin Bulama Bukarti da Gardi Zahra Mansur: darasi da nazari da izina

Tsakanin Bulama Bukarti da Gardi Zahra Mansur: darasi da nazari da izina

Daga DAKTA MUHAMMAD SULAIMAN FAGGE Wato da farko dai ya kamata Bulama Bukarti ya gode wa Allah. Mutane da yawa har da ni mai rubutun nan, mun kyautata masa zaton cewa shi ba mutumin banza ba ne, musamman da har za a zarge shi da harka da mata. Kuma wannan shaidar da ya samu daga bakuna masu yawa, tana da muhimmanci sosai, duk da cewa, ko me za a yi wasu ba za su yarda ba. Amma abin tambaya a nan, meye idan ka munana zato ga ɗan uwanka, bayan abin da kake zaton, ba tabbas? Wannan batu dole ne…
Read More
Ɓacewar takardun karatun ’yan siyasa wasa ne da hankalin ’yan Nijeriya

Ɓacewar takardun karatun ’yan siyasa wasa ne da hankalin ’yan Nijeriya

Daga ABBA YAKUBU ABDULLAHI Wani muhimmin batu da ya sake kunno kai a fagen siyasar ƙasar nan shi ne batun ɓacewar takardun shaidar karatun wasu ’yan siyasa masu neman manyan muqamai a ƙasar nan. Labari na baya bayan nan shi ne na sanarwar ɓacewar takardun shaidar kammala makarantar firamare da sakandire na mataimakin ɗan takara na wucin gadi ga Bola Ahmed Tinubu wanda Jam'iyyar APC ta tsayar domin ya yi mata takarar shugaban ƙasa. Rahotanni na bayyana cewa, Kabir Ibrahim Masari wanda aka gabatar da sunan sa a matsayin mataimakin Tinubu, ya shaida wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta INEC…
Read More
Yadda za ka gane budurwarka yaudarar ka ta ke yi

Yadda za ka gane budurwarka yaudarar ka ta ke yi

Daga AMINA YUSUF ALI Barkan mu da sake haɗuwa a wani makon cikin jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako mun zo mu ku da yadda namiji zai gano cewa, budurwar da ya ke tare da ita yaudarar sa ta ke yi. Ya kamata mu sani, ba wai maza ne kawai suke yaudarar mata ba. Su ma matan akwai su da yawa mayaudara waɗanda suke soyayya da namiji ba don suna son sa tsakani da Allah ba, sai dai don yaudara. To me ya sa ba sa rabuwa da waɗannan samari tunda ba son su suke yi…
Read More
Kyautata dangantaka da Sin na iya taimaka wa Amurka shawo kan matsalar tattalin arzikin

Kyautata dangantaka da Sin na iya taimaka wa Amurka shawo kan matsalar tattalin arzikin

Daga FAEZA MUSTAPHA Da safiyar yau Talata ne mataimakin firaministan Sin Liu He da sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen suka tattauna bisa gayyatar jami’ar ta Amurka. Cikin batutuwan da Jami’an biyu suka tattauna, akwai na samar da daidaito a fannin sarrafa hajoji da shigar da su kasuwanni da farfaɗo da tattalin arzikin duniya. Dukkan ƙasashen biyu na da fasahohi da dabaru daban-daban da za su amfani juna. Ƙasar Sin a nata ɓangare, ta fi samar da kayayyaki masu rahusa, kana ta yi suna a duniya, wajen ƙerawa da sarrafa kayayyaki. A don haka, ’yan kasuwar Amurka za su iya amfana…
Read More