Editor

9513 Posts
Mataimakin firaministan ƙasar Sin ya jaddada muhimmancin wanzar da nasarorin yaƙi da fatara

Mataimakin firaministan ƙasar Sin ya jaddada muhimmancin wanzar da nasarorin yaƙi da fatara

Daga CMG HAUSA Mataimakin firaministan ƙasar Sin Hu Chunhua, ya jaddada muhimmancin wanzar da nasarorin yaƙi da fatara, tare da buƙatar ingiza raya yankunan karkara daga dukkanin fannoni, domin tabbatar da cewa, akasarin alummun da aka tsame daga kangin talauci ba su sake komawa ba. Hu, wanda mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin ƙolin JKS, ya yi wannan tsokaci ne, yayin ziyarar aiki da ya gudanar a jihar Tibet mai cin gashin kanta tsakanin ranekun 1 zuwa 4 ga watan nan na Yuli. Mataimakin firaministan ya ganewa idanunsa yadda alamura ke gudana a fannonin ayyukan yi, da sakamkon fitar…
Read More
Babu wani ɗan Nijeriya da aka zalunta saboda addini, gwamnati ga Sanatocin Amurka

Babu wani ɗan Nijeriya da aka zalunta saboda addini, gwamnati ga Sanatocin Amurka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta yi Allah-wadai da kiran da wasu Sanatocin Amurka su biyar suka yi na neman a sake fasalin Nijeriya a matsayin ƙasar da ke nuna halin ko-in-kula kan cin zarafin addinai musamman ma Kiristoci. Sanatocin da suka yi wannan kiran a wata wasiƙa da suka aike wa sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, sun kuma yi zargin tauye haƙƙin Kiristoci na gudanar da addininsu. Da ya ke mayar da martani ga wannan zargi a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a birnin Landan, Ministan Yaɗa Labarai da…
Read More
Babu jarrabawa a ranar Babbar Sallah, inji NECO

Babu jarrabawa a ranar Babbar Sallah, inji NECO

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Jarrabawa ta Ƙasa, NECO ta ce ba za a yi jarrabawa a ranar 9 ga watan Yuli ba, savanin raɗe-raɗin da wasu ke yi na cewa za a yi jarrabawa a ranar Eid-el-Kabir. Majalisar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Azeez Sani, ya raba wa manema labarai a Abuja ranar Litinin. Ya ce hukumar tana sane da muhimmancin bukukuwan addini, don haka a ko da yaushe ta kan yi tsari da tanadin irin waɗannan ranakun wajen sanya ranar jarrabawa. “Hukumar ta ayyana…
Read More
HOTUNA: Kirista sun taya Musulmi gyaran Masallacin Idi a Kaduna

HOTUNA: Kirista sun taya Musulmi gyaran Masallacin Idi a Kaduna

Yayin da al'ummar Musulmi ke shirye-shiryen bikin Babbar Sallah, wasu matsa da dattawan Kirista a yankin Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, sun haɗa kai wajen taya musulmin yankin gyaran filin Masallacin Idi a ƙarshen makon da ya gabata. Bayan da aka yaɗa hotunan a soshiyal midiya, masu amfani da kafafen sun tofa albarkacin bakinsu, inda galibi suka yaba da hakan tare da nuna irin wannan shi zai taimaka wajen inganta haɗin kan ƙasa da kuma zaman lafiya.
Read More
Kotu ta yanke wa wanda ya kashe kwarton matarsa hukuncin kisa

Kotu ta yanke wa wanda ya kashe kwarton matarsa hukuncin kisa

Wata babbar kotu a Jihar Ogun ta yanke wa wani mai suna Adelake Bara hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun sa da laifin harbe wani mai suna Olaleye Oke, wanda ya kama yana yin lalata da ɗaya daga cikin matansa uku. Hakan ya biyo bayan hukuncin da mai shari’a Patricia Oduniyi ta yanke a ranar Litinin, 20 ga watan Yuni, 2022, inda ta bayyana cewa, masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhumar da ake yi masa ba tare da wata shakka ba cewa Bara na da laifi. Mai shari’a Oduniyi ya ce, laifin ya ci karo da dokar…
Read More
Samun kaina a Kannywood ce babbar nasarar da na samu – Rahina Bello

Samun kaina a Kannywood ce babbar nasarar da na samu – Rahina Bello

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A wannan mako filin Nishaɗi ya zanta da wata matashiya 'yar fim da ta shiga harkokin finafinai da ƙafar dama, Rahina M. Bello, wata matashiya ce da cikin ƙanƙanin lokaci ta yi fina-finai da yawa, a zantawarta da wakilinmu a Kano, za ku ji yadda a cikin shekara guda (Heena) ta shirya finafinai goma. Ku biyo mu: MANHAJA: Za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatunmu?Rahina: Sunana Rahina M. Bello amma an fi sanina da Heena. Za mu so ki ba mu taƙaitaccen tarihinki?An haifeni a barikin Sojoji na Ibadan, babana Soja…
Read More
Maikatanga ya samu kambun karramawa a matsayin ƙwararren mai ɗaukar hoto a gasar ‘GLF Africa 2022’

Maikatanga ya samu kambun karramawa a matsayin ƙwararren mai ɗaukar hoto a gasar ‘GLF Africa 2022’

Daga AISHA ASAS a Abuja Ƙwararren ɗan jarida mai ɗaukar hoto, Malam Muhammad Sani Maikatanga, ya yi nasarar lashe kambun ƙwararren mai ɗaukar hoto a gasar da Cibiyar Masu Kula da Hoton Ƙasashen Duniya (GLF) ta gudanar ta wannan shekara. Maikatanga ya samu wannan nasarar ne da hotonsa da ya yi wa laƙabi da 'Fishers on the Run', wanda ya ɗauka a bikin al'ada na kamun kifi da ake gudanarwa duk shekara a garin Argungu da ƙarƙashin Jihar Kebbi. Hoton ya samu ƙuri'u masu tarin yawa da suka yi wa saura zarra, wanda hakan ne ya kai shi ga taka…
Read More
Matakan da ma’abuta kwalliya za su bi don kare fatarsu

Matakan da ma’abuta kwalliya za su bi don kare fatarsu

Daga AMINA YUSUF ALI mata ma'abuta kwalliya yau filin na share hawayenku ne, domin abu ne sananne mata da yawa su na kukan matsalolin da suke gani tare da fatarsu musamman ma fuska, waɗanda suka kasa gano dalilin aukuwan su. Da yawa na bazama neman magani don kawar da matsalolin, sai dai abin takaice ko sun magance su na ɗan lokaci ne, sai su dawo. Hakan kan sa su shiga damuwa tare da halin tambayar kai. Idan kina ɗaya daga cikin matan da ba sa rabo da yin kwalliya a kullum, ga wasu matakai da za ki dinga amfani da…
Read More
An ƙaddamar da layin dogo na farko a Masar wanda kamfanin Sin ya gina

An ƙaddamar da layin dogo na farko a Masar wanda kamfanin Sin ya gina

Daga CMG HAUSA A Jiya Lahadi ne aka ƙaddamar da wani layin dogo na jirgin ƙasa a ƙasar Masar, wanda kamfanin Sin ya gina, kuma ya kasance hanyar jiragen ƙasa ta farko dake amfani da wutar lantarki a Masar. Shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi, da firayin minista Mostafa Madbouly, da sauran jamian Masar, da jakadan Sin dake Masar Liao Liqiang sun halarci bikin gwada layin dogon, inda suka isa tashar Badr daga tashar Adly Mansour ta jirgin ƙasa. Yayin ƙaddamarwar, ministan sufuri na Masar Kamel el-Wazir ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, kashi na farko na aikin gwajin hanyar zai gudana…
Read More
Wasu cibiyoyin ƙasar Sin sun tallafa wa makarantun firamare a Habasha da injunan samar da tsaftataccen ruwan sha

Wasu cibiyoyin ƙasar Sin sun tallafa wa makarantun firamare a Habasha da injunan samar da tsaftataccen ruwan sha

Daga CMG HAUSA Wasu cibiyoyin ƙasar Sin 4, sun tallafawa wasu makarantun firamare dake yankin SNNP na kudancin ƙasar Habasha, da injunan samar da tsaftataccen ruwan sha. Wata sanarwar da cibiyoyin suka gabatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, cewar cibiyar nazarin bunƙasa jagoranci ta Sin da Afirka ko (CALDI) ta jami’ar Tsinghua ta ƙasar Sin, da kamfanin HurRain NanoTech, da asusun raya karkara na ƙasar Sin (CFRD), da asusun fama da talauci ta ƙasar Sin, a matsayin sassan da suka yi haɗin gwiwar ba da taimakon.Makarantun da suka samu tallafin kuwa sun haɗa da firamaren Key-Afer, da ta Tulungo, da…
Read More