Editor

9513 Posts
Ko mace na da damar sakin mijinta? (1)

Ko mace na da damar sakin mijinta? (1)

Daga AISHA ASAS Na san da yawa za su yi mamakin wannan darasi na mu, musamman ma maza da za su ga abin kamar cin fuska, kasancewar saki ɗaya daga cikin ababen da suke tinƙahon su kaɗai ke da iko kan sa. Kasancewar darasin na mu na yau tambaya, za mu fara da amsa ta, domin kawar da kwankwanton da mai karatu yake ciki. Amsar kuwa ita ce, mace na da damar sakin mijinta, sai dai ba irin damar da mijinta ke da kan ta ba. Na san za ku ce Asas ta zo da wani sabon al'amari, sai dai…
Read More
Buhari ya tsige muƙaddashin Akanta-Janar, Anamekwe saboda rashawa

Buhari ya tsige muƙaddashin Akanta-Janar, Anamekwe saboda rashawa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhmamadu Buhari ya tsige muƙaddashin Akanta-Janar na Ƙasa Chukwuyere N. Anamekwe. Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, tuni aka maye gurbin Anamekwe da Mr. Okolieaboh Ezeoke Sylvis, tsohon Darakta na Asusun Bai-ɗaya (TSA), a matsayin mai riƙo. Bayanai sun ce an tsige Anamekwe ne saboda dalilai masu nasaba da rasahawa, inda aka nuna cewa da ma dai Hukumar Yaƙi da Cin-hanci (EFCC) tana bincike a kansa saboda zargin rashawa. An kuma ce, gwamanti ta nuna rashin gamsuwarta da kalaman da aka ce Anamekwe din ya yi cewa da bashi gwamnati ta biya albashin ma'aikata a…
Read More
Da me a ke layya?

Da me a ke layya?

Da farko ina amfani da wannan dama domin mu tunatar da junanmu. Layya dai ibada ce don haka tana da hukunce-hukunce tare da tanade-tanade, amma fahimtar hakan sai a wajen malamai masana. Ɗan uwa, a Musulunci a kula, Layya ba a buƙatar a mallaki dabba ta hanyar haramun ko kuma a yi layya domin a burge ko a fusata jama'a. Duk wanda ya kyautata niyya kuma ya yi aiki da ilimi, wannan ce hanyar dacewa. A yanzu za a samu ga namiji ya yi layya a tilascin matarsa ko kuma gasa ta abokai, duka hakan da matsala don haka hatta…
Read More
Sin: Ɓangaren Amurka ne ke yaɗa labaran bogi da ƙarairayi

Sin: Ɓangaren Amurka ne ke yaɗa labaran bogi da ƙarairayi

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya musanta kalaman da jakadan Amurka dake ƙasar Sin R.Nicholas Burns ya yi game da rikicin ƙasashen Rasha da Ukraine da kuma dakin gwajin ƙwayoyin halittu na ƙasar Amurka dake Ukraine, yana mai jaddada cewa, jami'an Amurka ne, ba ƙasar Sin ba, wadanda suka riƙa yada labaran bogi da kuma yada ƙarairayi. Zhao Lijian ya ce, ƙasar Sin a ko da yaushe tana yanke hukunci bisa gaskiya da adalci ta hanyar dogaro da shaidu na tarihi da ‘yanci kan batun Ukraine. Akwai bayanai masu tarin yawa…
Read More
Rashin tallafi kan iya durƙusar da harkar noman albasa – Aliyu Mai-ta-samu

Rashin tallafi kan iya durƙusar da harkar noman albasa – Aliyu Mai-ta-samu

Daga AMINU AMANAWA a Sokoto Albasa ɗaya ce daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen sarrafa abinci ko kuma sarrafa magunguna da sauran kayan maƙulashe. Nijeriya ƙasa ce da ke kan gaba a nahiyar Afirka wajen noma da ma sarrafa albasar. Da alama a Najeriya, Jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma, ce ke jagorantar jihohin ƙasar wajen noman albasar, abinda ma ya sa dubban matasa da dattawa samun hanyar dogara da kai kama daga masu noma, kasuwanci, dako, sufuri, dillanci da makamantansu. Sai dai kash! duk da muhimmanci da rawar da noma da kasuwancin albasar ke…
Read More
Adalci shi ne mafita ga rashin tsaro

Adalci shi ne mafita ga rashin tsaro

Ganin yadda ake jingina hare-haren 'yan bindiga akan makiyaya a Nijeriya, ya sa wasu manyan ƙasa suka kafa wata sabuwar ƙungiyar kare harkokin makiyayan da ake kamawa ba tare da laifin komai ba. Sai dai sabuwar ƙungiyar mai suna ‘Nomadic Rights Concern’ a Turance ba za ta kare waɗanda ke cikin harkar varna da fasadi ba. Sabuwar ƙungiyar makiyayan da ta yi taron ta na farko a Kaduna, ta ƙaddamar da sabbin shugabannin ta kuma ɗaya daga cikin iyayen ƙungiyar, Dr. Ahmed Mahmud Gumi, ya ce, ƙungiyar adalci za ta tabbatar domin samun zaman lafiya a Nijeriya, ba nuna banbanchin…
Read More
Mun shekara biyar muna fassara Alƙur’ani zuwa harshen Ibo, inji Ƙungiyar Musulmi ta Ibo

Mun shekara biyar muna fassara Alƙur’ani zuwa harshen Ibo, inji Ƙungiyar Musulmi ta Ibo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja A Juma'ar da ta gabata wata ƙungiyar Musulmi daga yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya ta ƙaddamar da Alƙur’anin da ta fassara zuwa harshen Ibo. Ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar ta 'Ibo Muslims D’awah Group', Malam Muhammad Muritala Chukuemeka ne ya bayyana hakan a ziyarar girmamawa da ƙungiyar ta kai wani kamfanin jarida da ke Abuja ranar Talata. “Yanzu haka muna da kwafi 500 na wannan fassarar Alƙur’ani, kuma mun aika guda 100 zuwa yankin Kudu maso Gabas domin ci gaba da aikin da’awa ga ’yan uwanmu ’yan ƙabilar Ibo, don haka ina kira ga…
Read More
Bai kamata iyaye su riƙa janye ƙararrakin fyaɗe daga kotuna ba – Shugabar FIDA

Bai kamata iyaye su riƙa janye ƙararrakin fyaɗe daga kotuna ba – Shugabar FIDA

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Shugabar Ƙungiyar Lauyoyi Mata ta Nijeriya (FIDA), Aisha Muhammad, a ranar Laraba, ta yi fatali da yawan janye ƙarar fyaɗe daga kotuna da wasu iyaye su ke yi a Nijeriya. Da ta ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya yayin wata ziyara da ya kai Kaduna, Aisha ya bayyana cewa, ƙungiyar na karɓar ƙararrakin fyaɗe a kullum, inda ta ƙara da cewa, amma yawancinsu an janye su kafin su kai ga kotu. A cewarta, galibin iyaye suna tsoron wulaƙancin da ’ya’yansu za su iya fuskanta a lokutan aure, don haka su ke janye irin…
Read More
Bankuna sun nemi masu neman canji su fara bin layi wata guda kafin buƙata

Bankuna sun nemi masu neman canji su fara bin layi wata guda kafin buƙata

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da canjin kuɗaɗen ƙasar waje suka yi matuƙar wahalar gaske, Bankuna sun umarci masu neman sayen kuɗaɗen ƙasar wajen da su fara bin layin neman kuɗin tun wata guda gabanin lokacin da za su yi amfani da kuɗin.  Bankuna sun ba da sanarwar tun a watan Mayun shekarar nan da muke ciki ta 2022. Bayan da wasu ɗalibai da kuma 'yan kasuwa suka yi ta ƙorafin yadda aka ja dogon lokaci kafin su samu canjin kuɗaɗen duk kuwa da sun cika dukkan sharuɗɗan da suka kamata.  A wata wasiƙa da wata majiya ta bayyana…
Read More
Duk wanda ya sauya sheƙa a bakin kujerarsa, garaɗin APC ga sanatocinta

Duk wanda ya sauya sheƙa a bakin kujerarsa, garaɗin APC ga sanatocinta

Daga BASHIR ISAH Jam'iyya mai mulki ta APC ta gargaɗi sanatocinta masu shirin sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar PDP cewa, suna iya rasa kujerunsu muddin suka aikata hakan. APC ta yi wannan barazana ne bisa la'akari da shirin da wasu sanatocinta su 15 ke da shi na ficewa daga jama'iyyar. Jam'iyyar ta faɗa wa sanatocin cewa, ficewa daga cikinta kasada ce babba domin kuwa hakan ka iya zama sanadiyyar rasa kujerunsu a Majalisar Tarayya. A hannu guda, su ma sanatocin kansu cike suke da tsoron kada bayan sun sauya sheƙar PDP ta ƙi cika alƙawarin kyautata musu da ta yi, musamman…
Read More