Editor

9513 Posts
Al’ummar yankin Hong Kong na ƙara jin daɗin rayuwarsu

Al’ummar yankin Hong Kong na ƙara jin daɗin rayuwarsu

Daga AMINA XU Abokai, “Duniya a Zanen MINA” a yau na zana wani hoto game da zaman rayuwar jama’ar yankin Hong Kong bayan shekaru 25 da dawowar yankin ƙarƙashin ikon kasar Sin. Waɗannan tsoffi biyu a cikin zanena suna raye-raye cikin farin ciki, abin da ya bayyana halin da jama’ar yankin ke ciki. Ko kun san cewa, a cikin waɗancan shekaru 25 da suka gabata, yawan al’ummar yankin ya karu daga miliyan 6 da dubu 502.1 zuwa miliyan 7 da dubu 413.1, a yayin da matsakaicin tsawon rayuwar maza da mata ya ƙaru da shekaru 6.2 da ma 5.5, lamarin…
Read More
Abin dariya ne da ‘yan siyasar Birtaniya suka bada ra’ayinsu kan batun yankin Hong Kong

Abin dariya ne da ‘yan siyasar Birtaniya suka bada ra’ayinsu kan batun yankin Hong Kong

Daga CMG HAUSA Yayin da aka cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong ƙasar Sin, firaministan kasar Birtaniya Boris Johnson da jami’in kula da harkokin waje da raya ƙasa na kasar Liz Truss sun ba da jawabi da sanarwa cewa, Birtaniya tana da alhakin kula da mazaunen yankin Hong Kong bisa haɗaɗɗiyar sanarwa a tsakanin Sin da Birtaniya, dake nuna cewa Birtaniya ba ta yi watsi da yankin Hong Kong ba. Wannan batun siyasa abin dariya ne, wanda ya shaida cewa, tsoffin ‘yan mulkin mallaka ba su son amincewa da haƙiƙanin yanayi na yanzu, wato ba su da ƙarfi…
Read More
Shugaban Nijeriya ya yi maraba da isowar jirgin ruwan farko a tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki

Shugaban Nijeriya ya yi maraba da isowar jirgin ruwan farko a tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki

Daga CMG HAUSA Shugaban Ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi maraba da samun nasarar isar jirgin ruwan farko zuwa tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki, wacce ita ce tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta farko a ƙasar da ake gudanar da aikin gina ta a Lagos, cibiyar kasuwancin ƙasar. Babban jirgin ruwan dakon kaya mai samfurin ZHEN HUA 28, ya taso ne daga yankin Hong Kong na ƙasar Sin, ya kuma isa kasar Najeriya a ranar Juma’a, wanda ke ɗauke da manyan injuna guda 3 da ake amfani da su wajen loda kayayyaki…
Read More
Ƙishirwa ta kashe ‘yan ci-rani 20 a ƙoƙarinsu na shiga Libya

Ƙishirwa ta kashe ‘yan ci-rani 20 a ƙoƙarinsu na shiga Libya

Masu aikin ceto a kan iyakar Chadi da Libya sun sanar da gano gawarwakin ‘yan ci-rani 20 a cikin hamada, waɗanda alamu ke nuna tsananin ƙishirwa ne ya yi sanadin mutuwarsu.Tawagar masu aikin ceton ta sanar da gano gawarwakin ne a kudu maso gabashin yankin Kufra mai nisan kilometre 120 daga Libya. Sanarwar masu aikin ceton ta ce, alamu na nuna motar 'yan ciranin ce ta samu matsala a tsakar sahara lokacin da su ke ƙoƙarin shiga Libya daga Chadi ko dai don shiga Turai ko kuma don gudanar da kasuwanci a Libyan wadda ta yi fama da yakin basasa…
Read More
Jan aikin da ke gaban Erik ten Hag a Man United

Jan aikin da ke gaban Erik ten Hag a Man United

Ranar Litinin sabon kocin Manchester United, Erik ten Hag ya fara jan ragamar atisayen ƙungiyar, domin shirin tunkarar kakar bana. Ranar 21 ga watan Afirilu aka sanar da ɗaura Tem Hag a matakin kocin United daga Ajax, domin maye gurbin Ralf Rangnick. United wadda ta yi ta shida a gasar Premier League da aka ƙarƙare, za ta fara buga babbar gasar ƙwallon ƙafa ta bana ranar 7 ga watan Agusta, inda za ta karɓi baƙuncin Brighton. ’Yan ƙwallo tara Ten Hag ya samu yin atisaye tare da su daga cikin waɗanda ke buga wa United wasanni da suka haɗa da…
Read More
Ganduje zai rufe bankuna uku a Kano saboda rashin biyan haraji

Ganduje zai rufe bankuna uku a Kano saboda rashin biyan haraji

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin mulkin Abdullahi Umar Ganduje, ta ba da wa'adin makwanni biyu kacal ga bankunan kasuwanci da suke a Kano domin su biya bashin harajin rajistar kasuwancinsu ko kuma gwamnati ta garƙame bankunan.  Bankuna da gwamnatin take yi wa sharaɗin dai su ne, First Bank, Ecobank da kuma Unity Bank. An gurfanar da bankunan uku a wata kotun tafi-da-gidanka wacce take gudanar da Shari'a a ƙarƙashin Babban Majistare Ibrahim Gwadabe. A zaman kotun na ranar Alhamis ɗin da ta gabata a jihar Kano ne dai kotun ta gurfanar da bankunan inda ta tuhume su…
Read More
Jami’ar NOUN ta yi sabbin naɗe-naɗe

Jami’ar NOUN ta yi sabbin naɗe-naɗe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Majalisar Gudanarwar Jami’ar NOUN ta Nijeriya, ta amince da naɗin sabon magatakarda, shugaban kula da shige da ficen kuɗaɗe da kuma shugaban ɗakin karatu, na wa’adi guda na shekaru biyar. Sabbin waɗanda aka naɗa sune, Oladipo Adetayo Ajayi a matsayin magatakarda, Malam Nasir Gusau Marafa a matsayin shugaban kula da shige da ficen kuɗaɗe da Dakta Angela Ebele Okpala a matsayin shugaban ɗakin karatu na jami’ar. An miƙa naɗin ga waɗanda aka naɗa a wasiƙu daban-daban na ranar 27 ga watan Yuni, 2022, kuma magatakarda mai barin gado, Felix I. Edoka ya sanya wa hannu. Edoka…
Read More
2023: APC ta ƙaddamar da dakarun matasa a jam’iyyar don tallafa wa Tinubu

2023: APC ta ƙaddamar da dakarun matasa a jam’iyyar don tallafa wa Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Matasan Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dayo Isreal, a Abuja ranar Laraba, ya ƙaddamar da mambobin tawagar dakarun matasan APC. Tawagar za ta jagoranci gyara da rajistar duk ƙungiyoyin goyon bayan APC da matasa suka kafa, gabanin zaɓen 2023. Isra'ila, a lokacin ƙaddamarwar, ya ce, tagawar za ta yi amfani da na'ura mai amfani da fasaha don jawo goyon baya ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki a babban zaɓen shekara mai zuwa. Ya ƙara da cewa, “za a buɗe sabunta ƙungiyoyin tallafa wa matasa da ɗalibai na tsawon wata ɗaya, daga ranar Juma’a…
Read More
Kiciniyar tikitin mataimakin Tinubu a Arewa maso Yamma

Kiciniyar tikitin mataimakin Tinubu a Arewa maso Yamma

*Gwamnonin yankin sun shiga ganawa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jagororin Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya na shiyyar Arewa maso Yamma sun naɗa tawagar wakilai da za su je su gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, game da zaƙulo wanda zai zame masa mataimaki a babban zaɓen 2023 mai ƙaratowa.  An cimma wannan matsayar ne a wurin taron jagororin shiyyar Arewa ta Yamma, da suka haɗa da gwamnoni, 'yan takarar gwamna, ministoci da sauransu, wanda ya gudana jiya a Abuja. A wata sanarwa da mataimakin shugaban APC na Arewa ta Yamma, Salihu Lukman,…
Read More
An kwaɓe Nanono a damuna, an naɗa magajinsa a damuna

An kwaɓe Nanono a damuna, an naɗa magajinsa a damuna

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Bara a damuna shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi wani garambawul inda ya kwave wasu daga cikin ministocinsa da su ka haɗa da Tsohon Ministan Noma, Sabo Nanono da na Wutar Lantarki, Injiniya Saleh Mamman. Duk da tuni an naɗa magajin Mamman daga jihar Taraba wato ƙaramin ministan ayyuka Alhaji Mu’azu Sambo, amma sai bana a ka naɗa ministan da ya maye gurbin Sabo Nanono daga Kano wato Umar Yakub. Abin da ya ɗauki hankali na shi ne yadda lamarin ya dace da lokacin damuna. Lokacin a ka cire Nanono har wani hoto a ka yaɗa…
Read More