Editor

9513 Posts
Matar Alaafin na Oyo ta bi shi bayan makwanni kaɗan da rasuwarsa

Matar Alaafin na Oyo ta bi shi bayan makwanni kaɗan da rasuwarsa

Daga AMINA YUSUF ALI Makwanni kaɗan da rasuwar Sarkin Oyo wanda aka fi sani da Alafin ɗin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ɗaya daga cikin matansa mai suna Olori Kafayat, ita ma ta ce ga garinku. Rahotanni sun bayyana cewa, basarakiyar mai suna, Olori Kafayat, wacce mahaifiya ce a gurin ɗan sarkin wato, Yarima Adebayo Adeyemi, wanda aka fi sani da D’Guv, ta rasu ne ranar Juma'a 1 ga Yuli, 2022. Cikakken bayani a game da mutuwar tata dai bai samu ba. Har lokacin da aka haɗa wannan rahoton dai babu wani ƙarin bayani. Amma daraktan kafofin yaɗa labarai da…
Read More
Duk da bambancin addinin da ke tsakanina da matata, littattafanmu ba su faɗa da juna – Tinubu

Duk da bambancin addinin da ke tsakanina da matata, littattafanmu ba su faɗa da juna – Tinubu

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya babbaya wa duniya wani abun da kan wakana a tsakaninsa da matarsa, Oluremi Tinubu. A cewar ɗan siyasar, matarsa da ta kansance mai bin addinin Kirista shi kuma Musulmi, kan ajiye littafin Baibul ɗinta a kusa da Ƙur'aninsa ba tare da samun wata mishkila ba. Tinubu ya bayyana haka ne a wani shafinsa na soshiyal midiya, inda ya ce duka litattafan biyu masu tsarki kan kasance ajiye wuri guda alhali ba a samun wata rashin jituwa a tsakaninsu. A cewarsa, "A ɗakin kwananmu, matata kan ajiye…
Read More
An naɗa Arabo sabon Sakataren Ƙaramar Hukumar Lafiya

An naɗa Arabo sabon Sakataren Ƙaramar Hukumar Lafiya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya An naɗa Alhaji Mohammed Haliru Arabo a matsayin sabon saktataren Ƙaramar Hukumar Lafiya, fadar gwamnatin jihar Nasarawa.  A cikin wata sanarwa ta musamman ɗauke da sanya hannun shugaban Ƙaramar Hukumar Lafiya, Honorabul Aminu Mu’azu Maifata da aka bai wa wakilinmu kwafi, Honorabul Maifata ya bayyana sabon sakataren a matsayin mai ƙwazo da sanin ya kamata da kuma ƙwarewa. Shi ya sa a cewarsa mahukuntan ƙaramar hukumar suka yanke shawarar naɗa masa mukamin.  Ya taya sabon sakataren murnar naɗin nasa, inda ya buƙace shi da ya yi aiki tuƙuru don cigaban ƙaramar hukumar Lafiya da…
Read More
Jama’ar mazaɓar Tofa, Dawakin Tofa da Rimin Gado sun koka da jagorancin Tijjani Joɓe

Jama’ar mazaɓar Tofa, Dawakin Tofa da Rimin Gado sun koka da jagorancin Tijjani Joɓe

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An ƙalubalanci ɗan majalisar Tarayyar mai wakiltar Ƙananan hukumomin Tofa, Dawakin Tofa da Rimin Gado a Majalisar Tarayya, Tijjani Abdulƙadir Joɓe da cewa tsawon lokaci da ya yi yana wakiltar yankin ba wani abu takamaimai na cigaban al'umma da ya kawo wa yankin. Ɗaya daga cikin 'yan Jam'iyyar NNPP Hon. Rabiu Abdullahi Rimin Gado ya bayyana hakan lokacin wata zantawa da 'yan jarida a Kano.  Ya ce kusan shekaru 16 ba wasu ayyukan raya ƙasa da yake yi, sannan ba wanda ya samar wa aiki ko ya ba shi wani wadataccen jari da zai gina…
Read More
Sarkin Fulanin Legas ya gudanar da taron zaman lafiya ga sarakunan Fulani

Sarkin Fulanin Legas ya gudanar da taron zaman lafiya ga sarakunan Fulani

Daga DAUDA USMAN a Legas Sarkin Fulanin Jihar Legas mai Martaba Dakta Mohammed Abubakar Bambado na II kuma shugaban Majalisar Sarakuna da Qungiyoyin Fulani a Nijeriya ya gudanar da taron sarakuna da sauran shuwagabannin ƙungiyoyin Fulani na ƙasar nan a Jihar Legas domin tattauna hanyoyin zaman lafiya a ƙasar nan. Taron wanda ya gudana a harabar babban ofishin Sarkin Fulanin dake cikin garin Legas a ƙarshen makon da ya gabata, waɗanda suka samu halartar taron sun haɗa da Sarkin Fulanin Abeokuta kuma sakataren majalisar Alhaji Kabiru Labar da harɗon jihar Oyo, Alhaji Yakubu Bello da Alhaji Abubakar shugaban ƙungiyar Miyetti…
Read More
Ana tuhumar wani ƙwara da lalata da mata ‘yan aikinsa a Jos

Ana tuhumar wani ƙwara da lalata da mata ‘yan aikinsa a Jos

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Garin Jos ta fara sauraron tuhumar da ake yi wa wani ƙwara ɗan asalin Ƙasar Lebanon, wanda ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a Jihar Filato, bisa laifin tilasta wa wasu yara mata ƙanana da ke yi masa aikin gida, yana lalata da su. A zaman da kotun ta yi a Jos, alƙalin kotun Mai Shari'a Dorcas Venenge Agashi wacce ta saurari tuhumar da ake yi wa wannan ƙwara a ƙarar da aka shigar ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya, an ba da belin wanda ake ƙarar bisa buƙatar lauyan wanda ake…
Read More
Fargabar matsalar tattalin arzikin Nijeriya

Fargabar matsalar tattalin arzikin Nijeriya

A makon da ya gabata, Bankin Duniya ya fitar da rahotonsa kan taɓarɓarewar tattalin arzikin Nijeriya. Rahoto a ƙarƙashin duba irin ci gaban da Nijeriya ta samu, Cibiyar Hada-hadar Kuɗi Ta Duniya ta bayyana cewa, taɓarɓarewar yanayin tattalin arzikin Nijeriya na ƙara jefa al'ummar ƙasar cikin wani hali. Rahoton ya nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki ya zama annoba ga rayuwar ’yan Nijeriya wanda dole ne hukumomi su yi yaƙi da hakan. Haɓakar hauhawar farashin kayayyaki da ke fitowa daga yaƙin Yukren, Bankin ya ce, zai iya jefa qarin 'yan Nijeriya miliyan ɗaya cikin matsanancin talauci. Tabbas tashe-tashen hankulan da yaƙin…
Read More
Kotu ta ɗaure sanata shekara 7 a kurkuku saboda rashawa

Kotu ta ɗaure sanata shekara 7 a kurkuku saboda rashawa

Daga WAKILINMU Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Legas ta yanke wa Sanata Peter Nwaoboshi hukuncin zaman kurkuku na shekara bakwai bayan da ta kama shi da laifin almundahanar kuɗaɗe. Haka nan, kotun ta ba da umarnin rufe wasu kamfanoni guda biyu mallakar sanatan, wato Golden Touch Construction Project Ltd da kuma Suiming Electrical Ltd, daidai da tanadin Sashe na 22 na Dokar Haramcin Almundahana ta 2021. Kotun ta yanke hukuncin ne bayan  Hukumar Yaƙi da Chin-hanci da Rashawa (EFCC) ta ɗaukaka ƙara tana ƙalubalantar hukuncin da Mai Shari'a Chukwujekwu Aneke na Babbar Kotun Tarayya ya yanke a ranar…
Read More
An ceto waɗanda ake zargin an nemi maida su Kiristoci a Jos

An ceto waɗanda ake zargin an nemi maida su Kiristoci a Jos

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar tsaro ta DSS ta kai sumame wani gida da ke unguwar JMDB a yankin Tudun Wada da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, inda ta ceto mutum 21, ciki har da wasu almajirai. Da take tabbatar da lamarin, Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ta shaida wa manema labarai cewa mutanen da aka kuɓutar sun ce an kai su cocin ne ta ƙarfin tsiya ana qoqarin mayar da su addinin Kiristanci. Babban sakataren cocin ECWA, Rabaran Yunusa Nmadu, ya ce gidan da aka kai samamen na cocin ne, amma ba sa…
Read More
Kamfanin CRCC na ƙasar Sin ya kammala aikin samar da ruwan sha a Angola

Kamfanin CRCC na ƙasar Sin ya kammala aikin samar da ruwan sha a Angola

Daga CMG HAUSA An kammala aikin samar da ruwan sha na Cabinda na ƙasar Angola, wanda kamfanin gine gine na ƙasar Sin (CRCC) ya aiwatar, inda aka fara amfani da shi a ranar 30 ga watan Yuni. An ba da rahoton cewa, an gudanar da aikin ne bisa ma’unin gine-gine na ƙasar Sin, wanda zai samar da ruwa mai yawan kyubik mita 50,000 a ko wace rana, tare da amfanawa mazauna yankin 600,000. Gwamnan lardin Cabinda, ya bayyana cewa, aikin zai iya samar da ruwan famfo na sa’o’i 24 a ko wace rana, wanda hakan zai kawar da matsalar ƙarancin…
Read More