Editor

9513 Posts
Ana sa ran yankin Hong Kong zai samu wani sabon cigaba a cikin shekaru biyar masu zuwa

Ana sa ran yankin Hong Kong zai samu wani sabon cigaba a cikin shekaru biyar masu zuwa

Daga CMG HAUSA Tun a lokacin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 18, shugaban ƙasar Xi Jinping ya nuna kulawa matuka game da wadata da zaman lafiyar yankin musamman na Hong Kong, da moriyar jama'ar wurin da walwalarsu, inda ya yi nuni da cewa, ci gaba shi ne ginshikin raya yankin Hong Kong da kuma magance matsaloli daban-daban. Shin ta yaya yankin Hong Kong zai samu sabon ci gaba cikin shekaru 5 masu zuwa? A wajen bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong ƙasar Sin, da kuma bikin rantsar da gwamnati ta shida ta yankin,…
Read More
An buga littattafai huɗu dake bayyana yadda Xi Jinping ke aiki a ƙananan hukumomi

An buga littattafai huɗu dake bayyana yadda Xi Jinping ke aiki a ƙananan hukumomi

Daga CMG HAUSA A kwanakin baya, aka buga wasu littattafai hudu dake bayyana yadda shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ke aiki a kananan hukumomi, ciki har da mai taken “A taimakawa jama’a kyautata zaman rayuwarsu yadda Xi Jinping ya yi aiki a Zhengding” da dai sauransu. Littattafan guda huɗu, sun mayar da hankali ne kan yadda Xi Jinping ya jagoranta tare da inganta gyare-gyare a cikin gida da buɗe kofa ga ƙasashen waje da kuma zamanintar da ƙananan hukumomin da ya taɓa yi wa aiki. Kana an waiwayi yadda Xi Jinping yake gudanar da harkokin mulki tare da yadda yake…
Read More
Hajji 2022: Malamai na ci gaba da ilimantar da mahajjatan Najeriya a Saudiyya

Hajji 2022: Malamai na ci gaba da ilimantar da mahajjatan Najeriya a Saudiyya

Daga MU'AZU HARDAWA a Madina A ci gaba da ƙoƙarin ilimantar da mahajjata game da muhimmancin aikin Hajji kaɓaɓɓiya da take yi, Hukumar Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta gargaɗi mahajjatan ƙasar da suka isa ƙasa mai tsarki don sauke farali kan su kasance masu lura da kuma bin doka yayin zamansu a Saudiyya. Babban limamin Hukumar 'Yan Sandan Najeriya, Sheikh Alhassan Yaakub, shi ne ya yi wannan gargaɗi a lokacin da yake gabatar da nasiha ga mahajjatan a birnin Madina. Malamin ya buƙaci alhazan su gode wa Allah bisa baiwar da Ya yi musu ta zama daga masu sauke faralin…
Read More
Zul-Hajj: An hori al’umma su dage da aikata alheri

Zul-Hajj: An hori al’umma su dage da aikata alheri

Daga MUAZU HARDAWA a Madina Yayin da aka shiga watan Zul-Hijja, wata na ƙarshe a kalanadar Musulunci, an hori al'umma musamman Musulmi, da su kara himma wajen aikata ibada da sauran ayyukan alheri. Limamin masallacin Manzon Allah (S.A.W) da ke birnin Madina a ƙasar Saudiyya, shi ne ya yi wannan horo sa'inlin da yake gabatar da huɗubar Sallar Juma'a a ranar Juma'ar da ta gabata. Huɗubar mai tsawon minti 30, ta maida hankali ne kan muhimmancin aikin Hajji da Umrah da kuma yin jihadi don daukaka kalmar Allah. Limamin ya ce, dukkan nasara na daga wajen Ubangiji, don haka ya…
Read More
Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin bikin cika shekaru 25 da dawowar HK ƙasar Sin da na ƙaddamar da sabuwar gwamnatin yankin

Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin bikin cika shekaru 25 da dawowar HK ƙasar Sin da na ƙaddamar da sabuwar gwamnatin yankin

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin ya gabatar da jawabi a taron bikin murnar cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong ƙarƙashin Jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin da kuma bikin ƙaddamar da sabuwar gwamnatin yankin ta 6. Xi Jinping, wanda shi ne shugaban kwamitin koli na JKS, kuma shugaban rundunar sojin ƙasar, ya taya John Lee, sabon jami’in farko na gwamnatin yankin da manyan jami’ai da mambobin majalisar zartarwar sabuwar gwamnatin yankin murna. Shugaban ya ce aiwatar da manufar “Ƙasa Ɗaya Mai Tsarin Mulki Biyu” ta haifar da nasarorin da kowa ke iya gani a yankin HK. Kuma tun bayan…
Read More
Ta yaya manufar “ƙasa ɗaya, amma tsarin mulki iri biyu” ta cimma nasarar da aka gani a Hong Kong?

Ta yaya manufar “ƙasa ɗaya, amma tsarin mulki iri biyu” ta cimma nasarar da aka gani a Hong Kong?

Daga CMG HAUSA "A cikin shekaru 25 da suka gabata, a ƙarƙashin cikakken goyon baya daga ƙasar uwa, da kuma ƙoƙarin haɗin gwiwa da gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, da ma dukkan ɓangarorin al'ummar yankin suke yi, manufar 'ƙasa daya, amma tsarin mulki iri biyu' ta samu nasarar da aka sani a Hong Kong. " A ranar 1 ga watan Yuli, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi a wajen bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong ƙasar Sin, da kuma bikin rantsuwar kama aiki ta gwamnatin yankin musamman na Hong Kong karo na shida,…
Read More
Shin maƙarƙashiya aka shirya don sauke Alƙalin Alƙalai, Ibrahim Tanko?

Shin maƙarƙashiya aka shirya don sauke Alƙalin Alƙalai, Ibrahim Tanko?

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi A bisa ƙoƙarin toshe duk wata kafa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekara ta 2023 musamman idan lamarin ya jiɓanci kotuna, magoya bayan ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu suka ɗauki mataki na sunƙuru na sauke Alƙalin Alƙalai na Tarayyar Nijeriya, Ibrahim Tanko Muhammad daga kan kujerarsa ta mulki. Kafar yaɗa labarai ta ‘Pointblanknews.com’ tun tuni a hukumance ta gano cewar, masu ilimin yin wannan yaqin sunƙuru suna son yin amfani da salon yadda aka ture tsohon Alƙalin Alƙalai na Tarayyar Nijeriya, Mai Shari’a Walter  ne, a yunƙurin su na…
Read More
An yanke wa mawaƙi R. Kelly hukuncin ɗaurin shekara 30 a gidan yari

An yanke wa mawaƙi R. Kelly hukuncin ɗaurin shekara 30 a gidan yari

Daga AISHA ASAS Wata kotu a Amurka ta aike da shahararren mawaƙi R. Kelly gidan yari har na tsayin shekaru 30, kan samunshi da laifin cin zarafin mata da ƙananan yara ta fuskar jima'i. Mai shari'a Judge Ann Donnelly ce ta zartar da hukuncin a Kotun Tarayya da ke Brooklyn, kusan shekara ɗaya kenan bayan kama mawaƙin da aikata laifin a garin New York. R. Kelly na ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan R&B da duniya ta san da zamansu tare da ba su muhalli na musamman, kafin ya samu kansa a aikata wannan ɗanyen aiki ga ƙananin mata, wanda ya…
Read More
An buƙaci a dawo da aikin duba-gari a Jihar Jigawa

An buƙaci a dawo da aikin duba-gari a Jihar Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Kimanin sati shida kenan Hukumar Tsaftace Muhalli ta Jihar Jigawa (JISEPA) ta yi tana yashe magudanan ruwa a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, a ƙoƙarin hukumar na kare muhalli da hana afkuwar ambaliyar ruwa a lokacin ruwan damina. Babban Manajan-darakta na hukumar,  injiniya Lawan Ahmed ya tabbatar da haka ga manema labarai a ranar Labar da ta gabata a ofishinsa. Ya ce  ma'aikatan hukumar sun share sati huɗu a Ƙaramar Hukumar Babura suna gyaran magudanun ruwa kuma suka gudanar da feshen maganin sauro da nufin inganta rayuwar al'umma ta ɓangaren tsaftar muhalli. Alhaji Lawan…
Read More
An sace ‘yan Chana da kashe jami’an tsaro a Jihar Neja

An sace ‘yan Chana da kashe jami’an tsaro a Jihar Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu 'yan bindiga sun kai hari wata mahaƙar ma'adinai a Jihar Neja, inda suka sace ma'aikata 'yan ƙasar Chana aƙalla huɗu, tare da kashe jami'an tsaro aƙalla shida wazanda suka ƙunshi 'yan sanda da sojoji da kuma 'yan sintiri na bijilante. Kwamishinan 'yan sanda na jihar Bala Kuryas, wanda ya tabbatar wa manema labarai, ya ce tuni aka tura jami'ai domin ganowa tare da ceto waɗanda aka sace a wani yanki na Ƙaramar Hukumar Shiroro. Sai dai kuma wata majiya ta shada wa BBC, cewa sojoji 4 da 'yan sandan sintiri 4 da kuma…
Read More