Editor

9513 Posts
Peng Liyuan ta ziyarci cibiyar wasannin kwaikwayo na gargajiyar ƙasar Sin da ke yankin al’adun West Kowloon ta Hong Kong

Peng Liyuan ta ziyarci cibiyar wasannin kwaikwayo na gargajiyar ƙasar Sin da ke yankin al’adun West Kowloon ta Hong Kong

Daga CMG HAUSA A yammacin Alhamis da ta gabata, Madam Peng Liyuan, uwargidan shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ta ziyarci cibiyar wasannin kwaikwayo na gargajiyar ƙasar Sin, wadda ke yankin al'adun na West Kowloon, a yankin musamman na Hong Kong, don fahimtar halin wurin, da yadda yake samun ci gaba, inda ta kuma tattauna da ma'aikatan wurin. Yayin ziyarar Mai fassara: Bilkisu Xin
Read More
Ansaru ta haramta harkokin siyasa a Birnin Gwari

Ansaru ta haramta harkokin siyasa a Birnin Gwari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Ansaru ta haramta duk wasu harkoki da ke da alaqa da siyasa a yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna. Ƙungiyar cigaban masarautar yankin ta ce, yanzu haka ƙungiyar ta shimfiɗa wasu sharuɗɗa da suka dace da salon shugabancinta, kuma duk wanda aka samu da saɓa su, yana iya fuskantar hukunci mai tsanani. Bayanan da BBC ta tattara sun bayyana cewa, ƙungiyar ta raba wa jama’a wani saƙo da ke ƙunshe da dukkan manufofinta, ciki har da na kawo ƙarshe tsarin dimukraɗiyya da kuma harkokin siyasa a yankin bakiɗaya. A yanzu dai…
Read More
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 82 a Zamfara

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 82 a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hedikwatar Tsaro (DHQ) a ranar Alhamis, ta bayyana cewa, wani farmakin da rundunar sojin sama ta 'Operation HADARIN DAJI' ta kai ta sama ta kashe ’yan ta’adda aƙalla 82 yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban a ƙauyen Ƙofar Ɗanya da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfara. Rundunar sojin ta kuma ce, an kama ɓarayin mai 26 da dakarun 'Operation DAKATAR DA BARAWO' da 'OCTOPUS GRIP' suka kama a yankin Neja Delta na ƙasar nan. Daraktan ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Benard Onyeuko ne ya bayyana haka a lokacin da ya…
Read More
PDP ta dakatar da ɗan majalisa a Kebbi

PDP ta dakatar da ɗan majalisa a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Jam'iyyar PDP a mazaɓar Dikko da ke Ƙaramar Hukumar Argungu ta dakatar da tsohon ɗan majalisar wakilai, Hon. Sani Bawa Argungu. Wannan yana ƙunshe ne a wata takardar sanarwa mai ɗauke da sa hannun ilahirin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar na mazaɓar Dikko da ke cikin garin Argungu da aka raba wa manema labarai ranar Litinin ɗin da ta gabata 27 ga watan Yuni 2022. Takardar ta bayyana cewa sun yanke shawarar dakatar da Honorabul Sani Bawa Argungu ne daga shiga duk wani al'amari na jam'iyyar har sai baba-ta-gani bayan wani zama da shugabannin  mazaɓar ta…
Read More
Ƙara wa’adin rijistar zaɓe dama ce ga al’ummar Yobe – Hon. Shariff Abdullahi

Ƙara wa’adin rijistar zaɓe dama ce ga al’ummar Yobe – Hon. Shariff Abdullahi

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Ɗan takarar kujerar Gwamnan jihar Yobe a ƙarƙashin inuwar Jam'iyyar PDP, Hon. Shariff Abdullahi ya yaba da matakin da Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ɗauka na ƙara wa'adin rijistar katin zaɓe zuwa ƙarshen watan Yuni, 2022. Tare da kira ga ilahirin al'ummar jihar Yobe da qasa baki ɗaya su yi amfani da wannan dama. Ya sanar da hakan a takardar manema labarai mai ɗauke da sa hannunsa tare da bayyana cewa, "mun yaba wa matakin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ɗauka na ƙara lokacin rijistar zaɓe…
Read More
Kwalejin Nasarawa za ta yi bikin cikar shugabarta shekaru biyu a kan kujera

Kwalejin Nasarawa za ta yi bikin cikar shugabarta shekaru biyu a kan kujera

Daga JOHN D. WADA a Lafiya A yanzu shire-shire ya yi nisa don gudanar da wani babban bikin cika shekaru biyu na shugabancin shugabar Kwalejin Kimiyya da Fasaha wato Mustapher Isah Agwai Polytechnic ta gwamnatin Jihar Nasarawa dake Lafiya babban birnin jihar, wato Misis Justina Kotso.  Shugaban sashin wasa labaran makarantan, Ali Hassan Mohammed ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa dake makarantar jiya Alhamis 30 ga watan Yunin shekarar 2022 da ake ciki.  Ya ce makarantar tana gudanar da babban bikin ne don murnar ɗimbin ayyukan cigaba da nasarori da shugabar makarantar,…
Read More
An ja kunnen tsofaffin sojoji su guji haɗa kai da ‘yan ta’adda

An ja kunnen tsofaffin sojoji su guji haɗa kai da ‘yan ta’adda

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya gargaɗi tsofaffin sojojin da suka yi ritaya su 125 daga rundunoni uku da ke ƙarƙashin runduna ta uku ta sojojin sulke da ke Jos, da su nisanci haɗa kai da 'yan ta'adda, da duk wasu masu neman kawo lalacewar tsaro a ƙasar nan, bayan sun koma kusa da iyalansu.  Babban Hafsan ya ce Rundunar Sojojin Nijeriya za ta cigaba da tuntuvar tsofaffin sojojin don amfani da shawarwarinsu da gudunmawarsu a ƙoƙarin da rundunar ke yi na yaƙi da ayyukan ta'addanci da tabbatar da zaman lafiya. …
Read More
Yadda ’yan kasuwa suka mayar da titinan Zariya wurin kasuwanci

Yadda ’yan kasuwa suka mayar da titinan Zariya wurin kasuwanci

Daga MOH'D BELLO a Zariya Yanzu haka ƙananan 'yan kasuwa sun maida sababbin titituna da gwamnati jihar Kaduna ta kammala wajen kasuwanci a birnin Zariya dake ƙaramar Hukumar ta Zariya. Wakilinmu wanda ya leƙa kasuwar ya ruwaito cewa ƙananan 'yan kasuwar waɗanda da suka haɗu da masu sayar da kayan miya da ma’auna da mahauta har da masu sayar da man fetur a cikin galoli duk su ne suka mamaye sabo titin da ya tashi daga Ƙofar gidan Bellon Gima ya ratsa Kusfa zuwa Azaran Dabuwa da titin da ya tashi daga Ƙofar Gidan Bellon Gima zuwa Unguwar Ƙaura ta…
Read More
Xi Jinping: muddin muka tsaya tsayin daka kan “ƙasa ɗaya, amma tsarin mulki iri biyu”, ko shakka babu makomar Hong Kong za ta yi kyau

Xi Jinping: muddin muka tsaya tsayin daka kan “ƙasa ɗaya, amma tsarin mulki iri biyu”, ko shakka babu makomar Hong Kong za ta yi kyau

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya isa yankin musamman na Hong Kong na ƙasar Sin ne, ta jirgin ƙasa mai saurin gaske da yammacin yau Alhamis, don halartar bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong ƙasar Sin, da kuma bikin rantsar da gwamnati ta shida ta yankin, wanda za a gudanar a ranar 7 ga watan Yuli, kana zai yi rangadi a yankin. A tashar jiragen ƙasa mai saurin gaske ta Hong Kong West Kowloon, jama'a daga sassa daban-daban na Hong Kong sun yi wa Xi Jinping maraba sosai. A jawabin da ya yi a bikin…
Read More
Bai dace Amurka ta cigaba da karya dokokin cuɗanyar ƙasa da ƙasa ba

Bai dace Amurka ta cigaba da karya dokokin cuɗanyar ƙasa da ƙasa ba

Daga SAMINU ALHASSAN Ga alama dai mahukuntan Amurka, na ci gaba da aiwatar da mummunar manufar nan ta muzgunawa kamfanonin ƙasar Sin dake gudanar da halastattun ayyukan su bisa doka. A baya-bayan nan, gwamnatin Amurkan ta sake ƙaƙaba takunkumin cinikayya kan wasu kamfanonin Sin guda 5, waɗanda ta zarga da cewa wai, suna taimakawa ayyukan soji da na tsaron ƙasar Rasha. To sai dai kuma, tuni masu fashin baƙi suka fara bayyana rashin dacewar wannan mataki na gwamnatin Amurka, duba da cewa mataki mafi dacewa, shi ne mika wannan batu gaban kwamitin tsaro na MƊD, wanda bisa doka, shi ne…
Read More