30
Jun
Daga CMG HAUSA Jiya Laraba, shugaban ƙasar Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadéra, ya baiwa tawaga ta 18 ta runkunin jiyya da Sin ta tura ƙasar lambar yabo a fadarsa, inda likitoci 9 suka samu lambar yabo ta jami’an soja, masu aikin fassara da dafa abinci, suka samu lambar yabo ta barada. A yayin bikin, Faustin-Archange Touadéra ya nuna cewa, ya karrama runkunin da wannan lambar ne, don jinjinawa taimakon da suka bayar da ayyuka masu inganci da suka gudanar, da kuma bayyana matuƙar godiyar jama’arsa ga runkunin. Ya ce, a cikin shekara daya da ta gabata, tawagar ta bai wa…
