Editor

9513 Posts
HOTUNA: Adamu ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Jihar Osun

HOTUNA: Adamu ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Jihar Osun

Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC don zaɓen gwamna da zai gudana a Jihar Osun. An kafa kwamitin ne ƙarkashin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas da takwaransa na Jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Sai dai, Gwamna Sanwo-Olu bai samu halartar bikin ƙaddamarwar ba sakamakon wani aikin ƙasa da ya ɗauke shi.
Read More
Kasar Sin ta nuna damuwa kan yadda ‘yan sandan Amurka suka kashe mutane ba bisa doka ba

Kasar Sin ta nuna damuwa kan yadda ‘yan sandan Amurka suka kashe mutane ba bisa doka ba

Daga CMG HAUSA Wakilin ƙasar Sin ya nuna damuwa kan yadda ‘yan sandan ƙasar Amurka suka kashe mutane ba bisa doka ba, yayin da yake tattaunawa da mai sa ido kan batun kashe mutane ba bisa doka ba, a wajen taron kwamitin kare haƙƙin dan Adam na MƊD karo na 50 jiya Laraba. Wakilin ƙasar Sin ya nuna cewa, an sha jin labaru masu tarin yawa dangane da yadda ‘yan sandan Amurka suka ci zarafin wasu yayin da suke aiwatar da doka. An ruwaito cewa, a cikin shekara guda bayan mutuwar George Floyd, wanda ya mutu sakamakon cin zarafi yayin…
Read More
An kammala taron tattauna zaman lafiya na Sin da kusuwar Afrika karo na farko

An kammala taron tattauna zaman lafiya na Sin da kusuwar Afrika karo na farko

Daga CMG HAUSA An kammala taron zaman lafiya da samar da ingantaccen shugabanci da ci gaba na Sin da kusurwar Afrika karo na farko a ranar Talata a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha, inda aka yi kiran haɗin gwiwa don cimma muradun bai ɗaya na shiyyoyin. Mahalarta taron na kwanaki biyu da aka kammala, sun tattauna tare da fidda sanarwar haɗin gwiwa kan wasu muhimman batutuwa goma sha biyu. Sanarwar haɗin gwiwar ta bayyana cewa, shiyyar kusurwar Afrika wato HOA, wani muhallin zama ne ga al’ummar dake shiyyar, kana ana buƙatar samun tabbatar da zaman lafiyar shiyyar, da kwanciyar…
Read More
CNTAC: Haramcin da Amurka ta sanya wa kayayyakin Xinjiang ya sava dokokin ciniki

CNTAC: Haramcin da Amurka ta sanya wa kayayyakin Xinjiang ya sava dokokin ciniki

Daga CMG HAUSA Ƙungiyar kare muradun kamfanonin samar da tufafi na ƙasar Sin CNTAC, ta ce haramcin da Amurka ta sanyawa dukkan kayayyakin da ake samar a yankin Xinjiang Uygur mai cin gashin kai na ƙasar Sin, ya saɓa wa dokokin cinikayya da tattalin arziki na ƙasa da ƙasa. CNTAC ta ce, tana adawa mai tsanani game da matakin Amurka na haramcin da ta sanya, wanda ba kawai yana haifar da mummunar illa ga moriyar kamfanonin saka tufafi na ƙasar Sin ba ne, har ma zai haifar da illoli ga tsarin dokokin kamfanonin saka tufafi na duniya. A cewar ƙungiyar…
Read More
Ekweremadu da matarsa sun faɗa a komar ‘yan sanda a ƙetare

Ekweremadu da matarsa sun faɗa a komar ‘yan sanda a ƙetare

Daga BASHIR ISAH 'Yan Sanda a birnin London sun tsare tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dr. Ike Ekweremadu tare da mai ɗakinsa, Beatrice. A cewar jaridar Sky, an tsare su biyun ne bisa zargin haɗin baki wajen ɗebe sassan jikin wani yaro. Sai dai, an ce tuni an ɗauki yaron da lamarin ya shafa zuwa wani wuri don ba shi kariya. Jaridar Sky ta ruwaito cewa, "Ana tuhumar wasu mutum biyu da haɗin baki wajen ɗaukar wani yaro zuwa Birtaniya domin ɗebe wasu sassan jikinsa, in ji 'yan sanda. “An tsare Beatrice Nwanneka Ekweremadu, 'yar shekara 55 da kuma…
Read More
Kamfanin Blueprint ya ɗage babban taronsa na shekara-shekara

Kamfanin Blueprint ya ɗage babban taronsa na shekara-shekara

Daga BASHIR ISAH Hukumar Gudanarwar ta Kamfanin Jaridun Blueprint, ta ba da sanarwar ɗage taron laccar da kamfanin ya saba shiryawa da kuma miƙa lambobin yabo shekara-shekara wanda da fari ta tsara gudanarwa ranar Alhamis, 23 ga Yuni, 2022. Sanarwar ɗagewar na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labaran da Babban Jami'in Gudanarwar kamfanin, Malam Salisu Umar, ya fitar ranar Laraba a Abuja. Jami'in ya ce, za a sanar da sabon lokacin da taron zai gudana nan ba da daɗewa ba. Ya ƙara da cewa, an ɗage taron ne saboda taron ECOWAS/NEC da zai gudana a ranar Alhamis wanda hakan ya…
Read More
Sauya sheƙa ba shi ne mafita ba, cewar Adamu ga sanatocin APC

Sauya sheƙa ba shi ne mafita ba, cewar Adamu ga sanatocin APC

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya roƙi sanatocin APC kan su yi haƙuri su daina ficewa daga jam'iyyar. A ranar Larabar da ta gabata Adamu ya bi sanatocin har cikin Majsalisar Tarayya ya gana da su, bayan la'akari da yadda sanatocin APC suka ba da himma wajen sauya sheƙa zuwa jam'iyyun adawa, lamarin da ba zai haifar wa jam'iyyar ɗa mai ido ba. Yayin ganawar tasu, Adamu ya roƙi sanatocin da ba su kai bantensu ba a zaɓen fidda gwanin jam'iyyar don shiga takara a babban zaɓen 2023, da su yi haƙuri. Majiyarmu ta…
Read More
Za mu kawo sauyin da zai bunƙasa rubutun adabi – Bala Anas Babinlata

Za mu kawo sauyin da zai bunƙasa rubutun adabi – Bala Anas Babinlata

"Da yawa masu aibata rubutun Hausa ba sa karanta littafan" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Marubuci Malam Bala Anas Babinlata ba voyayye ba ne a fagen rubutun adabi da shirya finafinan Hausa. Littafinsa na 'Ɗa Ko Jika' na daga cikin ayyukansa da suka ƙara masa ɗaukaka da shuhura a duniyar adabi, saboda irin salon rubutunsa mai tafiya da tunanin mai karatu, musamman a tsakanin shekarun 1991 zuwa 2000. A tsakanin wannan lokaci Bala Babinlata ya rubuta littattafai har fiye da 10, waɗanda akasarinsu sun shiga gidaje da dama a Nijeriya har da ƙasashen waje, wasu kuma an karanta su a tashoshin…
Read More
Tsaftace amfani da intanet: Kungiyar NADIR ta yi na’am da yunƙurin NITDA

Tsaftace amfani da intanet: Kungiyar NADIR ta yi na’am da yunƙurin NITDA

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Network of Advocates for Digital Reporting ko kuma NADIR a taƙaice, ta nuna goyon bayanta ga Hukumar Bunƙasa Fasahar Yaɗa Labarai Ƙasa (NITDA) dangane da dokokin da hukunar ta samar don sa ido tare da tsaftace sha'anin yaɗa bayanai ta kwamfuta da intanet. NADIR ta ce yunƙurin da NITDA ta yi, ta yi shi a kan lokaci musamman ma duba da lokacin zaɓen 2023 irin lokacin da wasu kan yi amfani da intanet wajen yaɗa bayanan ƙarya da na gaskiya. NADIR ta yi waɗannan bayanan ne cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar mai ɗauke…
Read More
Rahotanni game da kalaman Tedros cewa, Covid-19 na iya ɓulla daga ɗakin gwaje-gwajen Wuhan ba gaskiya ba ne

Rahotanni game da kalaman Tedros cewa, Covid-19 na iya ɓulla daga ɗakin gwaje-gwajen Wuhan ba gaskiya ba ne

Daga CMG Hausa Wasu rahotanni na cewa, a baya-bayan nan babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a asirce cewa, "Mai iyuwa asalin COVID-19 na iya ɓulla daga ɗakin gwaje-gwajen Wuhan." Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin ya bayyana Larabar nan cewa, sakatariyar hukumar ta WHO ta yiwa ɓangaren ƙasar Sin ƙarin haske, yana mai jaddada cewa, babban darektan hukumar bai furta irin waɗannan kalamai a bainar jama'a ko a ɓoye ba, kuma bayanan da aka bayar gaba daya ba gaskiya ba ne. Babban darektan da kansa bai amince da…
Read More