Editor

9513 Posts
Masari ya ɗauki nauyin Kiristoci 28 zuwa aikin ibada ƙasar Isra’ila

Masari ya ɗauki nauyin Kiristoci 28 zuwa aikin ibada ƙasar Isra’ila

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta ɗauki nauyin mabiya addinin Kirista 'yan asalin jihar zuwa ƙasar Isra'ila da kuma Jordan don gudunar da aikin ibadarsu. Kamar yadda Manhaja ta samu, Kiristocin waɗanda suka fito daga sassa daban-daban na jihar za su je ƙasar Isra'ila ne da ƙasar Jordan domin ziyarar wuraren ibadarsu da kuma wuraren tarihi masu muhimmanci a addinin na su. Da yake ƙarin haske a kan batun ga majiyar Manhaja ta Katsina Post mai bai wa gwamnan jihar shawara akan addinin Kiristocin, Rabaran Ishaya Jimrau, ya bayyana cewa mutanen…
Read More
Jami’in Sin: taron shugabannin BRICS ya samu kyawawan sakamako

Jami’in Sin: taron shugabannin BRICS ya samu kyawawan sakamako

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron shugabannin BRICS karo na 14 da ya gudana a daren jiya, ta kafar bidiyo daga birnin Beijing, faɗar mulkin ƙasar. Yayin taron manema labarai da aka yi bayan taron, mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Xu, ya ce taron ya gudanar cikin nasara, wanda ke da muhimmiyar ma’ana ga makomar ƙungiyar. Ma ya furta cewa, a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Xi, shugabannin ƙasashen BRICS sun tattauna sosai kan yadda za a raya kyakkyawar hulɗar abota, a kokarin sa kaimi ga ci gaban duniya. Haka kuma Shugaba Xi ya gabatar…
Read More
BRICS ta fitar da sanarwar Beijing da ta yi alƙawarin kare tsaro da zaman lafiya a duniya

BRICS ta fitar da sanarwar Beijing da ta yi alƙawarin kare tsaro da zaman lafiya a duniya

Daga CMG HAUSA Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da ta fitar yayin taron kolinta na 14, ƙungiyar ƙasashen BRICS, ta yi alƙawarin kare zaman lafiya da tsaro a duniya. Haka kuma, yayin taron tattalin arziki da kasuwanci na ƙungiyar, an fitar da shirin raya harkokin kasuwanci a ƙasashen BRICS na Beijing, da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa da inganta farfaɗowar tattalin arzikin duniya. Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa
Read More
Sin za ta ɗauki managartan matakai don cigaba da tallafa wa ajandar cigaba mai ɗorewa ta MƊD nan da 2030

Sin za ta ɗauki managartan matakai don cigaba da tallafa wa ajandar cigaba mai ɗorewa ta MƊD nan da 2030

Daga CMG HAUSA A yammacin yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya jagoranci wani babban taron tattaunawa kan ci gaban duniya ta kafar bidiyo, tare da gabatar da muhimmin jawabi. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, sai al'ummomin ƙasashen duniya suna rayuwa mai kyau ne kadai za a iya samun ɗorewar wadata, da tabbatar da tsaro, da kare haƙƙin dan-Adam. Ƙasar Sin za ta ɗauki managartan matakai, don ci gaba da tallafawa ajandar samun dauwamammen ci gaba ta MƊD nan da shekarar 2030. Ƙasar Sin za ta kara zuba jari a fannin samar da albarkatu a haɗin gwiwar…
Read More
Ya kamata gwamnati ta ɗauki matakin sassauta wa al’umma ƙuncin rayuwa – Ɗanpass

Ya kamata gwamnati ta ɗauki matakin sassauta wa al’umma ƙuncin rayuwa – Ɗanpass

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ɗaya daga cikin Dattawan Arewa Ɗansaran Kano, Alhaji Gambo Abdullahi Ɗanpass ya yi kira ga mahukuntan ƙasar nan da su ɗauki matakai don sassautawa al'umma, musamman na Arewa halin da suka shiga na ƙuncin rayuwa da suka haɗa da yawan tashin farashin da kayan abinci da na masarufi, wanda ya ce hakan na matuƙar galabaitar da rayuwar al'umma. Ɗanpass ya yi nuni da cewa yanzu ta kai shinkafa da aka hana shigowa da ita, ta gidan ma da ake nomawa anan na neman ta gagari talaka, sannan noman ma da ake ga damuna ta taho…
Read More
Yadda ɗan banga ya yi wa ‘yar shekara 13 fyaɗe a Nasarawa

Yadda ɗan banga ya yi wa ‘yar shekara 13 fyaɗe a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Hukumar tsaron farin kaya da aka fi sani da Nigeria Security and Civil Defense Corps a turance na ƙasa reshen Jihar Nasarawa ta cafke wani mataimakin shugaban ‘yan banga mai suna Dalla I. Usman mai kimanin shekaru 42 dangane da aikata laifin fyaɗe wa wata ƙaramar yarinya mai suna Ummi Musa mai kimanin shekaru 13. Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai ciki har da wakilin mu a helkwatar hukumar dake Lafiya babban birnin jihar ranar Talata, 22 ga watan Yunin shekarar 2022 da ake ciki, jami’in hulɗa da jama’a na…
Read More
Yadda aikin hanyar Abuja zuwa Kano ke janyo asarar rayuka a Zariya

Yadda aikin hanyar Abuja zuwa Kano ke janyo asarar rayuka a Zariya

Daga MOHAMMED BELLO HABIB a Zariya Al’ummomin Gwargwaje dake cikin Ƙaramar Hukumar Zariya cikin Jihar Kaduna, sun koka a kan yawaitar haɗurra a yankinsu. Mai magana da yawun al’ummomin, Alhaji Shagari Mai Nama a tattaunawar shi da wakilin Manhaja a Zariya, ya koka akan yawaitar haɗurran, inda ya ce a duk rana ana samun haɗurra 2 zuwa 3 a yankin waɗanda kuma suke haifar da asarar rayukan al’umma akan wannan babban hanyar saboda yawan ababen hawa da suke ƙaruwa a kodayaushe, kuma hanya ce da ta haɗe Kudanci da Arewacin ƙasar nan. Alhaji Mainama ya ƙara da cewa tunda a…
Read More
Kotun Birtaniya ta ƙi amincewa da belin Ekweremadu da matarsa

Kotun Birtaniya ta ƙi amincewa da belin Ekweremadu da matarsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotun majistare na Uxbridge da ke ƙasar Birtaniya ta ƙi bayar da ba da belin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice kan zarginsu da safarar mutane da kuma sassan jiki. ’Yan sanda sun kama mutanen biyu ne a ranar Alhamis a birnin Landan. An tattaro cewa, waɗanda ake zarginsu da hannu a lamarin wani yaro ne mai shekaru 15 da haihuwa wanda Ekweremadu da matarsa suka kawo shi ƙasar Birtaniya daga kan titin Legas a Nijeriya. An tsare su a hannun ’yan sanda a ƙasar Birtaniya. An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar…
Read More
An gano yaron da Sanata Ekweremadu da matarsa suka yi safara zuwa Birtaniya don cire ƙodarsa

An gano yaron da Sanata Ekweremadu da matarsa suka yi safara zuwa Birtaniya don cire ƙodarsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An samu wata shaida dangane da yaron da tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya da matarsa Beatrice, da ake zargi da yin safararsa zuwa ƙasar Birtaniya don cire ƙodarsa. Idan za a iya tunawa dai jami'an 'yan sandan ƙasar Birtaniya sun damƙe tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Ike Ekweremadu tare da mai ɗakinsa Beatrice akan yunƙurin cire sassan jikin yaro. Kazalika, sashen ƙwararrun 'yan sandan ƙasar sun miƙa waɗanda ake tuhumar zuwa kotu a birnin Landon don gudanar da bincike.  Yaron wanda ba a san sunansa ba, ba kuma a ga hotonsa ba, wakilin…
Read More
Rashawa: ICPC ta gano sama da biliyan N1 a gidan Buratai

Rashawa: ICPC ta gano sama da biliyan N1 a gidan Buratai

Daga BASHIR ISAH Tsohon Babban Hafsan Hafsoshi, Tukur Buratai, ya sake samun kansa cikin wata sabuwar badaƙalar rashawa bayan da hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC ta gano maƙudan kuɗaɗe sama da biliyan N1.89 ɓoye cikin wani gida a Abuja da aka ce mallakar Buratai ɗin ne. An rawaito cewa, jami'an ICPC sun yi wa gidan da ke yankin Wuse dirar mikiya ne baya ne biyo bayan bayanan sirrin da hukumar ta samu. Jaridar Peoples Gazette ta ce, da aka nemi jin ta bakinsa kan batun, Buratai ya ce ICPC ba ta da izinin binciken gidansa. Buratai wanda shi ne…
Read More