Editor

9513 Posts
Kotu ta yi watsi da ƙarar da Buhari ya shigar yana ƙalubalantar ‘yan majalisa a kan dokar zaɓe

Kotu ta yi watsi da ƙarar da Buhari ya shigar yana ƙalubalantar ‘yan majalisa a kan dokar zaɓe

Daga AMINA YUSUF ALI Kotun ƙoli ta Nijeriya ta yi watsi da ƙarar da Shugaban Ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari da Antoni Janar na Tarayya suka shigar suna ƙalubalantar 'yan majalisa a kan dokar sashe na 84(12) na dokar zaɓe a ƙasar nan. A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai wato 24 ga watan Yunin 2022, Babbar kotun ta bayyana cewa, bayan duba zuwa ga dokar da aka tabbatar da ita cikin watan Fabrairu na shekarar 2022 da muke ciki, ta ce ba ta da hurumin da za ta iya ƙalubalantar matsayin dokar zaɓen a Shari'a. A cikin hukuncin da…
Read More
Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta buƙaci alummar jihar su ɗauki makamai don kare kai

Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta buƙaci alummar jihar su ɗauki makamai don kare kai

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Biyo bayan ƙaruwar ‘yan fashi da makami a Jihar Zamfara, gwamnatin jihar ta umurci mutane da su shirya tare da samun bindigogi domin kare kansu daga ‘yan bindigar. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa jaridar Blueprint Sunday, mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar, Ibrahim Dosara. A cewar sanarwar, gwamnati ta umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya bayar da lasisi ga duk wanda ya cancanta da kuma buƙatar samun irin waɗannan bindigogi domin kare kansu. “Gwamnati a shirye ta ke ta bai wa mutane dama musamman…
Read More
Wang Yi ya yi bayani kan ganawar shugabannin ƙasashen BRICS ƙarƙashin jagorancin Xi

Wang Yi ya yi bayani kan ganawar shugabannin ƙasashen BRICS ƙarƙashin jagorancin Xi

Daga CMG HAUSA Shugaban kiasar Sin Xi Jinping ya jagaranci ganawar da aka yi tsakanin shugabannin ƙasashen ƙungiyar BRICS karo na 14 ta kafar bidiyo a ranar 23 ga wata. Haka kuma ya jagoranci taron tattauna ci gaban ƙasa da ƙasa a jiya tare kuma da gabatar da wani muhimmin jawabi. Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya yi bayani kan manufofin da shugaba Xi ya gabatar, da tasiri mai zurfi da za su yi ga ƙasa da ƙasa. Wang Yi ya bayyana cewa, ganawar da ƙasar Sin ta shirya tana da babbar ma’ana…
Read More
Magance cutar Sikila a Nijeriya

Magance cutar Sikila a Nijeriya

A Nijeriya, an ware ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara domin tunawa da ranar cutar sikila ta duniya. Ana bikin ranar ne don wayar da kan jama'a na duniya kowace shekara da nufin havaka ilimin jama'a da fahimtar cutar sikila da ƙalubalen da marasa lafiyar da danginsu da masu kula da su ke fuskanta. Kafin mu san ya cutar ta ke, dole mu fara sanin yadda ake kamuwa da ita. Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana ɗauke da abubuwa iri daban–daban, kamar su 'plasma', 'Red Blood Cells' (RBC),…
Read More
An shawarci Mahajjatan Nijeriya su kasance jakadu nagari a ƙasa mai tsarki

An shawarci Mahajjatan Nijeriya su kasance jakadu nagari a ƙasa mai tsarki

Daga DAUDA USMAN a Legas An shawarci al'ummar Musulmin Nijeriya musamman maniyyata aikin Hajjin bana da su zama jakadu nagari yayin gudanar da aikin Hajji a ƙasa maitsarki. Sarkin Fawan Ƙaramar Hukumar Amuwo Odofin dake cikin garin Legas, Alhaji Usaini Iliyasu shi ne ya yi wannan kiran yayin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke cikin kasuwar Amuwo Odofin, sa'ilin da yake yin sallama da wasu mahauta masu niyyar tafiya aikin Hajjin bana. Usaini ya cigaba da cewa a sakamakon waɗansu maniyyata 'yan Nijeriya suna haɗa gudu da susar katara wajen zuwa ƙasa mai tsarki domin su sauke…
Read More
Cigaba abu ne na zahiri a tarihin Sin

Cigaba abu ne na zahiri a tarihin Sin

Daga CMG HAUSA Shugaban Ƙasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron tattauna ci gaban ƙasa da ƙasa jiya da yamma ta kafar bidiyo. Cikin jawabin buɗe taron, Xi Jinping ya bayar da labarinsa na kasancewa manomi a wani ƙaramin ƙauye dake yankin tsaunikan Loess na ƙasar Sin a ƙarshen shekarun 1960. Wannan labari na shugaban ƙasar Sin ya bayyana cewa, ba tare da la’akari da inda suke ba, burin ɗaukacin mutane shi ne samun ingantacciyar rayuwa. Ga shugabanni kuwa, ci gaba da raya ƙasa ne kaɗai zai iya cimma burin jama’a na samun ingantacciyar rayuwa da zaman lafiyar al’umma. Mai…
Read More
Sin ta yi kira ga Amurka da ƙasashen Yamma su soke takunkuman da suka yi gaban kansu wajen ƙaƙabawa

Sin ta yi kira ga Amurka da ƙasashen Yamma su soke takunkuman da suka yi gaban kansu wajen ƙaƙabawa

Daga CMG HAUSA Ƙasar Sin, ta yi kira ga Amurka da ƙasashen yammacin duniya, su gaggauta soke takunkuman da suka yi gaban kansu wajen ƙaƙabawa, da dakatar da keta haƙƙoƙin jama’a a wasu ƙasashe. Wakilin na Sin ne ya yi kiran a jiya, yayin zama na 50 na majalisar kare haƙƙin ɗan Adam ta MƊD, a lokacin da yake halartar tattaunawar da aka yi tsakanin wasu masana masu zaman kansu, a ɓangren haƙƙoƙin bil adama da haɗin giwar ƙasashen duniya. Fassara wa: Fa’iza
Read More
2023: Ɗan takarar Gwamnan Nasarawa a PDP ya zaɓi mataimakinsa

2023: Ɗan takarar Gwamnan Nasarawa a PDP ya zaɓi mataimakinsa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa a zaɓen shekarar 2023 a inuwar Jami’iyyar PDP, Honorabul Joseph Ombugadu ya sanar da Alhaji Yahaya Usman Ohinoye a matsayin mataimakinsa a takarar kujerar. Da yake jawabi wa ɗimbin magoya bayan jam’iyyar da manema labarai jim kaɗan bayan ya sanar da mataimakin nasa, Joseph Ombugadu ya bayyana cewa da shi da ƙungiyar yaƙin neman zaɓensa da sauran shugabannin jam’iyyar a jihar sun ga ya dace ne su zaɓi Alhaji Yahaya Usman Ohinoye don ya mara masa baya a tafiyar idan aka yi la’akari da cancantarsa da kuma ƙwarewarsa…
Read More
NDLEA ta ƙwace kilo 251 na miyagun ƙwayoyi a Jihar Nasarawa

NDLEA ta ƙwace kilo 251 na miyagun ƙwayoyi a Jihar Nasarawa

• Ta cafke masu fataucin ƙwayoyi 240 cikin wata shida Daga JOHN D. WADA a Lafiya Hukuma Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Nijeriya (NDLEA), reshen Jihar Nasarawa ta ce ta ƙwace kimanin kilogiram 251 na miyagun ƙwayoyi a jihar. Kwamandan hukumar a jihar, Peter Onche-Odaudu ne ya sanar da haka a jawabinsa a lokacin da yake ganawa ta musamman da manema labarai a shalkwatar hukumar dake birnin Lafiya, fadar gwamnatin jihar ranar Alhamis 23 ga watan Yunin shekarar 2022 da ake ciki. Ya ce hukumar ta kuma cafke masu fataucin ƙwayoyin sama da 240 daga watan Janairu…
Read More
Bauchi ta zaƙulo ma’aikatan bogi 8,211 da samun rarar kuɗi Naira biliyan ɗaya

Bauchi ta zaƙulo ma’aikatan bogi 8,211 da samun rarar kuɗi Naira biliyan ɗaya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamnatin Jihar Bauchi ta zaƙulo ma'aikatan bogi 8,211 tare da kuma samun rarar kuɗi har sama da Naira biliyan ɗaya. Wani mai shekaru 71 da haihuwa yana ɗaya daga cikin ma’aikatan bogi 8, 211 da gwamnatin Jihar Bauchi ta zaƙulo a cikin jerin sunayen ma’aikatanta, kamar yadda Sakataren Gwamnatin jihar, Barista Ibrahim Mohammed Kassim ya zayyana. Kassim ya kuma bayyana bambancin alƙaluman kuɗaɗen albashin ma’aikatan gwamnatin jihar ta yadda aka samu wannan rarar ta maƙudan kuɗaɗe, inda yake cewa lokacin da suka hau karagar mulki, kuɗaɗen albashin ma’aikata yana laƙume zunzurutun kuɗaɗe Naira biliyan shida…
Read More