Editor

9513 Posts
Habasha na ƙara nuna sha’awar cinikayyar riɗi a kasuwannin Sin

Habasha na ƙara nuna sha’awar cinikayyar riɗi a kasuwannin Sin

Daga CMG HAUSA Masu samar da ridi da fitar da shi ƙetare, sun bayyana matuƙar sha’awarsu na kara zurfafa hulɗar cinikayya da ƙasar Sin, a yayin da ake samun ƙaruwar masaya daga ƙasar Sin. Sisay Asmare, shugaban ƙungiyar masu sarrafa wake da nau’ikan amfanin gona da ake fidda mai da fitar da su zuwa ƙetare ta ƙasar Habasha, (EPOSPEA), ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan cewa, ƙasar Sin ta kasance a matsayin babbar kasuwar da ƙasar Habasha ke samar mata da ridi a shekaru 10 da suka gabata, yayin da kashi 60 zuwa kashi 70…
Read More
Yankin Xinjiang na ƙasar Sin ya yi Allah wadai da dokar wai magance aikin tilas da Amurka ta kafa

Yankin Xinjiang na ƙasar Sin ya yi Allah wadai da dokar wai magance aikin tilas da Amurka ta kafa

Daga CMG HAUSA Sassa daban daban daga jihar Xinjiang mai cin gashin kai ta Uygur ta ƙasar Sin, sun yi Allah wadai da dokar da Amurka ta kafa mai suna wai “ Dokar magance aikin tilas ta Uyghur," inda suka bayyana cewa, matakin wani yunƙuri ne na lahanta moriyar wasu ba tare da samun amfani komai ba ga ita kanta, kuma matakin ya kawo illa matuƙa ga muhallin kasuwancin ƙasa da ƙasa. Xu Guixiang, kakakin gwamnatin jihar ya bayyana a taron manema labarai a ranar Juma’a cewa, matakin da Amurka ta ɗauka na haramta sayen kayayyakin yankin Xinjiang tamkar wani…
Read More
Ɓatanci: Sufin Zamani ya aika wa MOPPAN da takardar ban-haƙuri

Ɓatanci: Sufin Zamani ya aika wa MOPPAN da takardar ban-haƙuri

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani ɓangare na cika sharuɗɗan da aka gindaya masa, mawaƙi Sarfilu Umar, wanda aka fi sani da Sufin Zamani, ya aika wa ƙungiyar shirya finafinai ta MOPPAN takardar ban-haƙuri. Hukumar DSS ce ta buƙaci mawaƙin ya rubuta takardar ban-haƙurin bayan da ta kama shi da laifin yi wa matan Kannywood ɓatanci cikin wata waƙa da ya yi. A cikin takardar da ya rubuta, Sufin Zamani ya jaddada nadamarsa ta yin waƙar ɓatancin, tare da bada haƙuri yadda ya kamata. Cikin sanarwar da Kakakin MOPPAN na Ƙasa, Al-Amin Ciroma ya fitar ta nuna cewa, wannan tabbaci…
Read More
Safarar mutane: Jami’ar Ingila ta dakatar da Ekweremadu cigaba daga aiki da ita

Safarar mutane: Jami’ar Ingila ta dakatar da Ekweremadu cigaba daga aiki da ita

Daga AMINA YUSUF ALI Wata jami'a a ƙasar Ingila mai suna University of Lincoln, United Kingdom, ta sallami tsohon mataimakin shugaban majalisar dokoki, Ike Ekweremadu, wanda bai dace da fara aiki tare da ita a matsayin Farfesa na wucin gadi na hulɗarta da ƙasashen waje a jami'ar. Wannan kora dai ta biyo bayan kama Ekweremadu da mai ɗakinsa Beatrice da hukumar ƙasar ta Landan ta yi a kan zargin haɗa baki da safarar wani yaro mai suna Ukpo Nwamini David zuwa birnin Landan don cirar ƙodarsa. Shi dai David mai ƙarancin shekaru hukuma ta tabbatar da cewa, bai mallaki hankalin…
Read More
Mutane sun farwa limamin coci kan yi wa Ekweremadu addu’a

Mutane sun farwa limamin coci kan yi wa Ekweremadu addu’a

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu mutane sun bayyana rashin jin daɗinsu kan yadda limamin coci, Johnson Suleman ya yi wa Ekweremadu da matarsa addu’ar Allah ya kuɓutar da su, inda suka yi ta cece-kuce a Manhajar Tuwita. Rundunar ’yan sandan birnin Landan ta kama tsohon mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu tare da matarsa Beatrice bisa zargin haɗa baki da juna na safarar sassan jikin wani yaro. Ekweremadus ya buƙaci ƙodar yaron ga ɗiyarsu, Sonia, wacce ke fama da matsalar ƙoda. Da ya ke mayar da martani ga labarin, Suleman ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa, “an ji labarin…
Read More
Gareth Bale ya fice daga Madrid zuwa MLS

Gareth Bale ya fice daga Madrid zuwa MLS

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rahotanni daga Birtaniya da Amurka sun nuna cewa, Gareth Bale ya koma Los Angeles FC bayan ya bar Real Madrid. Jaridar Los Angeles Times, ta nakalto majiyar Major League Soccer tare da sanin yarjejeniyar ta ce, tauraron mai shekaru 32 zai iya buga wasa a LAFC daga ranar 1 ga watan Yuli. A halin da ake ciki, ESPN ta ruwaito cewa, Bale zai tashi zuwa Los Angeles a ƙarshen mako mai zuwa don sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta ƙare a ƙarshen kakar wasa ta bana, tare da zaɓin ƙarin shekara. Bale ya taɓa zama…
Read More
MOPPAN ta gurfanar da wanda ya yi wa matan Kannywood ɓatanci

MOPPAN ta gurfanar da wanda ya yi wa matan Kannywood ɓatanci

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar masu shirya finafinai ta MOPPAN, ta gurfanar da wani mai suna Sufin Zamani a gaban hukumar DSS saboda ɓatancin da ya yi wa matan Kannywood. MOPPAN ta ce ta ɗauki wannan mataki ne biyo bayan ƙorafin da wasu matan Kannywood suka aikewa shugabanta na ƙasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, mai taken: "Ƙorafin cin zarafi da wani mawaƙi mai suna 'Sufin Zamani," takardar da tsohuwar jarumar fim Wasila Isma'il ta sanya wa hannu, a madadin Matan Kannywood. Wannan ya sanya MOPPAN gaggauta shiga binciken ƙorafin, inda daga bisani ta rubuta wa Hukumar DSS, domin yin abin da…
Read More
Super Eagles ta koma matsayi na 31 a jadawalin FIFA

Super Eagles ta koma matsayi na 31 a jadawalin FIFA

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta koma matsayi na 31 a sabon jadawalin FIFA da aka fitar a ranar Alhamis. An buga sabon matsayi na ne akan gidan yanar gizon FIFA. A Afirka, Super Eagles yanzu ta koma matsayi na huɗu bayan Senegal da Morocco da Tunisia, waɗanda ke matsayi na ɗaya da na biyu da na uku. Saliyo wadda ta yi rashin nasara a hannun Eagles a wasannin neman cancantar shiga gasar AFCON ta 2023, ta koma mataki na 113 yayin da Guinea-Bissau ta kasance a matsayi na 115. Sao Tome and Principe, wacce ta…
Read More
2023: INEC ta wallafa sunayen ‘yan takarar da ta yarda da su daga kowacce jam’iyya

2023: INEC ta wallafa sunayen ‘yan takarar da ta yarda da su daga kowacce jam’iyya

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta wallafa bayanan wasu 'yan takarar shugabancin Nijeriya da na majalisu waɗanda jam'iyyu suka tura wa hukumar a matsayin waɗanda za su wakilci jam'iyyun a kakar zaɓen ta 2023. Rahotanni sun bayyana cewa, wannan bayani INEC ce ta wallafa shi ne a ranar Juma'ar da ta gabata a ofishinta na ƙasar nan. Bayanan da ta wallafa game da 'yan takarar sun haɗa da, Sunayen 'yan takarar shugaban ƙasa da kowacce jam'iyya ta tsayar a matsayin ɗan takararta da abokan takararsa (mataimaki), sannan da 'yan takararsu na 'yan majalisar dattawa da…
Read More
Na yi kuskuren ɗaukar Atiku a matsayin mataimakina a 1999 – Obasanjo

Na yi kuskuren ɗaukar Atiku a matsayin mataimakina a 1999 – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ɗaya daga cikin kurakuran da ya tafka a rayuwarsa shi ne zaɓar mataimaki a 1999. Obasanjon ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyi a wani taro na wasu ɗalibai a Abeokuta da ke Jihar Ogun, ranar Asabar 25 ga Yuni, 2022, kamar yadda jaridar Intelregion ta ruwaito. Obasanjo dai shi ne ya yi nasara a zaɓen Shugaban Nijeriya a shekarun 1999 da 2003, inda Atiku Abubakar ya zama mataimakinsa. "Ba zan ce bana kuskure ba, na yi su da yawa," inji Obasanjo.…
Read More