Mutane sun farwa limamin coci kan yi wa Ekweremadu addu’a

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu mutane sun bayyana rashin jin daɗinsu kan yadda limamin coci, Johnson Suleman ya yi wa Ekweremadu da matarsa addu’ar Allah ya kuɓutar da su, inda suka yi ta cece-kuce a Manhajar Tuwita.

Rundunar ’yan sandan birnin Landan ta kama tsohon mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu tare da matarsa Beatrice bisa zargin haɗa baki da juna na safarar sassan jikin wani yaro.

Ekweremadus ya buƙaci ƙodar yaron ga ɗiyarsu, Sonia, wacce ke fama da matsalar ƙoda.

Da ya ke mayar da martani ga labarin, Suleman ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa, “an ji labarin halin da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya shiga, Allah ya kuɓutar da shi, ya ba ɗiyarsa lafiya. Mun gode wa Allah da ya tsare rayuwar wannan ƙaramin yaro, wanda za a yi amfani da shi. Allah Ya taimake su su yi abin da ya dace. Wannan ma ya wuce!”