Safarar mutane: Jami’ar Ingila ta dakatar da Ekweremadu cigaba daga aiki da ita

Daga AMINA YUSUF ALI

Wata jami’a a ƙasar Ingila mai suna University of Lincoln, United Kingdom, ta sallami tsohon mataimakin shugaban majalisar dokoki, Ike Ekweremadu, wanda bai dace da fara aiki tare da ita a matsayin Farfesa na wucin gadi na hulɗarta da ƙasashen waje a jami’ar.

Wannan kora dai ta biyo bayan kama Ekweremadu da mai ɗakinsa Beatrice da hukumar ƙasar ta Landan ta yi a kan zargin haɗa baki da safarar wani yaro mai suna Ukpo Nwamini David zuwa birnin Landan don cirar ƙodarsa. Shi dai David mai ƙarancin shekaru hukuma ta tabbatar da cewa, bai mallaki hankalin kansa ba, hakan kuma ya saɓa wa doka.

Wata jaridar ƙasar mai suna The London Mail a ranar Asabar ɗin da ta gabata ta ruwaito cewa, mai magana da yawun jami’ar ya bayyana cewa, a yanzu haka dai jami’ar ta dakatar da dukkan ayyukan Ekweremadu a cikinta zuwa nan da wani lokaci.

Kakakin jami’ar ya ƙara da cewa, “sam ba mu ji daɗin wannan tuhumar da aka yi masa ba, amma a halin yanzu da hukumar tsaro take kan bincike a kansa, ba za mu iya cewa komai akan al’amarin ba”.

Hakazalika, ya qara da cewa: “A halin yanzu da matsalar take ƙarƙashin binciken jami’an tsaro, wannan mutumin ba zai cigaba da gudanar da ayyukan da yake yi a wannan makarantar ta Lincoln ba”.

A halin yanzu dai kotun garin Landan take tsare da Ekweremadu da mai ɗakinsa Beatrice, don jiran sake zaman kotu don cigaba da sauraren ƙarar tasu nan da 7 ga watan Yulin 2022.

Kodayake, ɗan majalisar na Nijeriya ya riga ya musanta zargin da kotun take tuhumarsa da shi. Ya bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa da ya aike ga ofishin jakadancin Nigeriya dake ƙasar Ingila.