Gareth Bale ya fice daga Madrid zuwa MLS

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rahotanni daga Birtaniya da Amurka sun nuna cewa, Gareth Bale ya koma Los Angeles FC bayan ya bar Real Madrid.

Jaridar Los Angeles Times, ta nakalto majiyar Major League Soccer tare da sanin yarjejeniyar ta ce, tauraron mai shekaru 32 zai iya buga wasa a LAFC daga ranar 1 ga watan Yuli.

A halin da ake ciki, ESPN ta ruwaito cewa, Bale zai tashi zuwa Los Angeles a ƙarshen mako mai zuwa don sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta ƙare a ƙarshen kakar wasa ta bana, tare da zaɓin ƙarin shekara.

Bale ya taɓa zama ɗan wasa mafi tsada a duniya kuma ya shafe shekaru takwas da suka gabata tare da Real Madrid, inda ya lashe kofunan gida uku da kofin zakarun Turai biyar.

Ɗan wasan na Wales ya zura ƙwallaye 139 a tarihin ƙungiyar inda ya zura ƙwallaye 39 a wasanni 106 da ya buga wa Wales.

Bale ya taka rawar gani wajen ganin Wales ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta bana, inda za ta kara da Amurka da Ingila da Iran a zagayen farko a Qatar.

Wannan dai shi ne karon farko da Wales ta samu gurbin shiga gasar tun a shekarar 1958.

Sa hannun Bale ya zo ne a lokacin da LAFC ta yi yunƙurin gina katafaren farawa a gasar MLS.

Kulob ɗin na California ya jagoranci matakin yammacin taron da maki 30 daga wasanni 15.

Bale zai kasance ɗan wasa na biyu da ƙungiyar ta saya a cikin ‘yan makonnin nan. Tsohon ɗan wasan Juventus da Italiya Giorgio Chiellini ya koma ƙungiyar a farkon watan nan.

Labarin matakin Bale na zuwa gasar Major League Soccer na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan rahotanni a Biritaniya sun nuna cewa yana tattaunawa da Cardiff kan yiwuwar tafiya.

Tsohon kulob ɗinsa na Tottenham da Newcastle kuma an zaɓo su ne a matsayin inda za su je.