Editor

9513 Posts
An gudanar da gasar harshen Sinanci ta Chinese Bridge ga ɗaliban jami’a da na sakandare a Uganda

An gudanar da gasar harshen Sinanci ta Chinese Bridge ga ɗaliban jami’a da na sakandare a Uganda

Daga CMG HAUSA An gudanar da gasar harshen Sinanci ta Chinese Bridge, ga daliban sakandare da jami’a, a cibiyar Confucius ta jami’ar Makerere dake Uganda. Taken gasar na bana, na rukunin ɗaliban jami’a shi ne, “Duniya Guda, Iyali Guda” yayin da na daliban sakandare ya kasance “Kwarewa a Harshen Sinanci”. Da yake jawabi a wajen gasar da aka yi ranar Asabar, jakadan Sin a Uganda Zhang Lizhong, ya ce gasar ta inganta musayar al’adu tsakanin ƙasashen biyu, kuma ta zama wani dandali da ɗalibai ke ƙulla abota. Ita kuwa daraktar cibiyar tsara manhajar karatu ta ƙasar, Grace Baguma, cewa ta…
Read More
Ƙasar Sin na adawa da duk wani yunquri na ɓata sunan shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”

Ƙasar Sin na adawa da duk wani yunquri na ɓata sunan shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”

Daga CMG HAUSA Game da sabuwar shawarar inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, wadda ƙasashen G7 suka gabatar, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin cewa, ƙasarsa har kullum tana maraba da duk wata shawarar dake inganta muhimman ababen more rayuwar al’ummar duniya, kana shawarwari daban-daban ba za su iya maye gurbin juna ba. Ya ce ƙasar Sin na nuna adawa ga duk wani yunƙuri na bata sunan shawarar “ziri daya da hanya ɗaya”, bisa hujjar inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, don cimma muradun siyasa. Rahotanni sun ce, kwanan nan,…
Read More
Alƙalin Alƙalai, Tanko Muhammad ya yi murabus

Alƙalin Alƙalai, Tanko Muhammad ya yi murabus

Daga BASHIR ISAH Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Mai Shari'a Tanko Muhammad, ya yi murabus daga aiki. Majiyar tashar Channels Television ta ce Jastis Muhammad ya yi murabus ne a Lahadin da ta gabata saboda dalili na rashin lafiya. Bayanai sun nuna cewa, an yi nisa da shirye-shirye don rantsar da Alƙali mafi girman muƙami a Kotun Ƙoli, wato Jatis Olukayode Ariwoola, a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya mai riƙon ƙwarya. Haka nan, bayanan sun ce nan ba daɗewa ba za a sanar da naɗin a hukumance. Kafin yin murabus, rahotanni sun tabbatar da Jastis Muhammad na fama da rashin lafiya sosai. Idan…
Read More
Kamfanin mai na Nijeriya ya samu lambar yabo kan ingancin kaya daga Turai

Kamfanin mai na Nijeriya ya samu lambar yabo kan ingancin kaya daga Turai

Daga AMINA YUSUF ALI A kwanakin nan ne dai wani kamfanin mai na asalin Nijeriya mai suna MOAHZ Oil and Gas, Wanda ɗaya ne daga cikin kamfanonin da suke ƙarƙashin rukunin kamfanoni na MOAHZ group, ya samu nasarar amsar kambun yabo daga ƙasar Turai saboda ingancin kaya da harkokinsa. Majalisar cinikayya ta ƙasar Birtaniya (EBA) ita ce ta jagoranci shirya taron da ba da wannan kambun girmamawar. A yayin da yake jawabin taya murna, shugabar gudanarwa ta majalisar EBA, Malama Anna Jones, ta bayyana cewa, manufar wannan taron ba da kyaututtukan da karramawa mai taken, 'Karramawar ingancin kaya na Duniya…
Read More
LEAD ta nemi INEC ta tsawaita rajistar katin zaɓe zuwa Disamba

LEAD ta nemi INEC ta tsawaita rajistar katin zaɓe zuwa Disamba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar 'Leadership and Entrepreneurship Advocacy' (LEAD), wata ƙungiya mai zaman kanta, ta buƙaci Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da ta tsawaita rajistar katin masu kaɗa ƙuri’a zuwa Disamba. Babban Darakta na LEAD, Chukwuma Okenwa, ne ya yi wannan kiran a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, a Enugu ranar Laraba. Okenwa ya yi magana kan yadda ake samun ƙaruwar sabbin masu rajista, da zanga-zangar da wasu matasa suka yi a faɗin ƙasar, kan rashin isassun injinan katin zaɓe da za su iya kai wa ga kowa a kullum. A cewarsa, har…
Read More
Masu zabiya na buƙatar kulawa ta musamman daga gwamnati – Shugaban Ƙungiyar Zabiya

Masu zabiya na buƙatar kulawa ta musamman daga gwamnati – Shugaban Ƙungiyar Zabiya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙungiyar Zabiya ta Nijeriya (AAN), Jake Epelle, a ranar Talata ya roƙi gwamnatin tarayya da ta jihohi kan shirin magance cutar kansar fata ga masu fama da zabiya (PWA). Epelle ya yi wannan roƙo ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a Kalaba. Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya masu hali da ƙungiyoyi da su taimaka waasu fama da zabiya. Shugaban ya ce, illar cutar kansar fata tana kashe masu zabiya kuma dole ne a yi wani abu don shawo kan cutar. Shugaban ya ƙara da cewa, matakin da…
Read More
Biyo bayan zaɓukan fidda gwani…Shin Adamu zai iya saisaita al’amuran APC?

Biyo bayan zaɓukan fidda gwani…Shin Adamu zai iya saisaita al’amuran APC?

…Ko ya zo a makare ne?…Ya zai warware sarƙaƙiyar takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa?…Ta ina zai ɓullo wa rikicin takarar Ahmad Lawan da Machina?…Shin Buni ya gadar ma sa kangarwar jam’iyya ne?…Me ya sa Fadar Shugaban Ƙasa ke sakar ma sa ragama? Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Biyo bayan kammala zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, rikici da ficewa daga cikin jam’iyyar ya varko sakamakon yadda wasu da ke neman takara suke ganin ba a yi musu adalci ba ko kuma ba su samu abinda suke so ba. Duk da cewa, wannan ba wani baƙon abu…
Read More
Canjin ‘yan takara: INEC ta gindaya sharuɗɗa ga jam’iyyun APC, LP da sauransu

Canjin ‘yan takara: INEC ta gindaya sharuɗɗa ga jam’iyyun APC, LP da sauransu

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) a ranar Juma'ar da ta gabata ta zana sharuɗɗan da ya kamata jam'iyyu su cika kafin su samu damar canza 'yan takarar mataimakin shuganan ƙasa kafin nan da kakar zaɓen ta 2023. INEC ta ba a wannan sharaɗin ne duba a yadda wasu jam'iyyun suka tsayar da sojan gona da suka aike da sunansa zuwa ga INEC, kafin su samu ɗan takarar na din-din-din. Wato dai kamar yadda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya miƙa sunan Doyin Okupe a atsayin mataimainsa na wucin gadi.…
Read More
Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin jin ra’ayoyin jama’a ta hanyoyi daban-daban

Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin jin ra’ayoyin jama’a ta hanyoyi daban-daban

Daga CMG HAUSA An gudanar da aikin jin ra’ayoyin mutane masu amfani da kafar sadarwar Intanet game da ayyukan da suka shafi babban taro karo na 20 na jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin. Game da wannan batu, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, babban taron karo na 20, muhimmin al’amarin siyasa ne na jam’iyyar kwaminis da na ƙasar Sin baki ɗaya. Neman jin ra’ayoyin al’umma ta kafar Intanet game da taron, hanya ce mai kyau da ake bi wajen tattaro kyawawan shawarwari da dabaru na samar da ci gaban ƙasa, wanda ya shaida salon demokuraɗiyyar ƙasar. Xi ya…
Read More