28
Jun
Daga CMG HAUSA Jiya ne, kashi na farko na kayayyakin agajin girgizar ƙasa da gwamnatin ƙasar Sin ta taimakawa Afganistan suka isa filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul, babban birnin ƙasar Afganistan. Jakadan ƙasar Sin dake Afghanistan Wang Yu, da Gholam Gaus, muƙaddashin ministan kula da bala'o'i da ayyukan jin kai na gwamnatin wucin gadin ƙasar Afghanistan, sun halarci bikin miƙa kayayyakin. A jawabinsa jakada Wang Yu ya bayyana a yayin bikin mika kayayyakin cewa, girgizar ƙasar da ta afkawa ƙasar Afganistan, ta taba zukatan jama'ar ƙasar Sin, kuma nan take gwamnatin ƙasar Sin ta yanke shawarar ba…
