Editor

9513 Posts
Sin da Equatorial Guinea sun rattaɓa hannu kan musayar bayanai don taimakawa aikin gona a Equatorial Guinea

Sin da Equatorial Guinea sun rattaɓa hannu kan musayar bayanai don taimakawa aikin gona a Equatorial Guinea

Daga CMG HAUSA A ranar 20 ga wata, a ma'aikatar harkokin waje da hadin gwiwar ƙasar Equatorial Guinea, jakadar ƙasar Sin dake ƙasar Equatorial Guinea Qi Mei da ministan harkokin wajen Equatorial Guinea Simeon Oyono Angue, suka rattaba hannu kan musayar bayanai a madadin gwamnatocin ƙasashen biyu, don taimakawa fasahar aikin gona a ƙasar. Uwar gida Qi Mei ta bayyana cewa, ƙasar Sin tana fatan tallafawa ƙasar Equatorial Guinea, don raya aikin gona na zamani bisa ƙarfin kanta, da inganta ƙarfinta na tabbatar da samar da abinci. A nasa jawabin minista Simeon Oyono Angue ya bayyana cewa, taimakon da ƙasar…
Read More
Sin ta kira taron tattauna mummunan tasirin da manufar mulkin mallaka ya haifar ga haƙƙin bil Adama

Sin ta kira taron tattauna mummunan tasirin da manufar mulkin mallaka ya haifar ga haƙƙin bil Adama

Daga CMG HAUSA Yayin taro karo na 50 na majalisar kula da kare haƙƙin Bil Adam ta MƊD, tawagar dindindin ta ƙasar Sin a ofishin MƊD dake Geneva, ta kira taron tattauna mumunan tasirin da manufar mulkin mallaka ta haifar ga haƙƙin bil Adam ta kafar bidiyo. Chen Xu, Wakilin dindindin na tawagar ƙasar Sin dake ofishin da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa dake Switzerland, ya bayyana cewa, kamata ya yi ɓangarori daban-daban su duƙufa kan kawar da mumunan tasirin da manufar mulkin mallaka ya haifar musamman ma a fannin haƙƙin bil Adam, ta yadda za a tabbatar da adalci…
Read More
INEC ta amince da tsawaita shirin rijistar masu zaɓe da kwana 60

INEC ta amince da tsawaita shirin rijistar masu zaɓe da kwana 60

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta amince da tsawaita wa’adin gudanar da shirin yi wa masu zaɓe rijista da kwana 60. Kafin wannan lokaci, ƙarshen watan Yunin 2022 INEC ta tsayar a matsayin lokacin da za ta kammala shirin yi wa masu zaɓe rijista. Jaridar Guardian ta rawaito cewa, Shugabar Kwamitin Majalisar Wakilai Kan Saha’anin Zaɓe, Aishatu Jibril Dukku ce ta bayyana tsawaita wa’adin ga takwarorinta a ranar Laraba. Ta ce, “Jiya (Talata) Kwamitin ya gana da INEC inda aka amince da batun tsawaita shirin yin rijistar…..” A ranar Litinin da ta gabata wata…
Read More
Yadda IBB ya soke zaɓen shugaban ƙasa na MKO Abiola 1993: Amsar tambayar Mijinyawa Lawan

Yadda IBB ya soke zaɓen shugaban ƙasa na MKO Abiola 1993: Amsar tambayar Mijinyawa Lawan

Daga SALIADEEN SICEY Moshood Kashimawo Olawale Abiola GCFR, wanda aka fi sani da MKO Abiola ɗan kasuwar Nijeriya ne, mawallafi ne, kuma ɗan siyasa. A ɓangaren sarautar gargajiya kuma, shi ne Aare Ona Kankafo XIV na ƙasar Yarbawa. Abiola sunan Najeriya ne na asalin Yarbawa. Ma'anar Abiola Shi ne "An haife shi cikin daraja/arziki'. Marigayi Cif MKO Abiola na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ya lashe zaɓen shugabancin qasa da aka yi a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993. An gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya a ranar 12 ga watan Yunin 1993, wanda shi ne na farko…
Read More
Alƙalan Kotun Ƙoli sun koka kan matsalolin da suka addabe su

Alƙalan Kotun Ƙoli sun koka kan matsalolin da suka addabe su

Daga BASHIR ISAH Alƙalan Kotun Ƙoli na Nijeriya sun koka kan taɓarɓarewar harkokinsu a ƙarƙashin Babban Alƙalin Nijeriya (CJN), Ibrahim Tanko Muhammad. A cewar jaridar Peoples Gazette, alƙalan sun bayyana damuwarsu ne cikin wata wasiƙa da suka rubuta suna masu kokawa kan matsalolin da ke addabarsu a bakin aiki, ciki har da rashin kari a kason da fannin shari’a ya saba samu a tsakanin shekaru huɗun da suka gabata. Cikin wasiƙar tasu, alƙalan sun ce, “Muna yi wa ƙasar nan aiki bilhaƙƙi. Mukan warware matsalolin da suka taso tsakanin Majalisar Zartarwa da ta dokoki, da kuma tsakanin gwamnatoci da ma…
Read More
Buhari ya kama hanyar naɗa sabbin ministoci

Buhari ya kama hanyar naɗa sabbin ministoci

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa wasu sunaye guda bakwai ga Majalisar Dattawa don tabbatar da su a matsayin ministoci. Sunayen na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Buharin ya aika wa Shugaban Majlaisar, Ahmad Lawan, inda shi kuma Lawan ɗin ya karanto wasiƙar yayin zaman majalisar a ranar Talata. A cikin wasiƙar, Buhari ya bayyana cewa, buƙatar neman tabbatar da ministocin ta yi daidai da Sashe na 147 ƙaramin sashe na 2 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa gyara. Sunayen da lamarin ya shafa su ne: Henry Ikechukwu Ikoh (Abia), Umana Okon…
Read More
Rayuwar yara na da muhimmanci ga cigaban ƙasar nan

Rayuwar yara na da muhimmanci ga cigaban ƙasar nan

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A wannan makon mai ƙarewa ne aka gudanar da bikin ranar yara ta Afirka, wacce ta mayar da hankali wajen duba halin rayuwar da yara a sassa daban-daban na nahiyar ke ciki, da kuma tattauna hanyoyin da za a bi don kyautata rayuwar su da yadda goben su za ta kasance, a matsayin su na yara manyan gobe. Na yi wannan rubutu ne domin yabawa da gudunmawar da iyaye ke bayarwa ga tarbiyyar yaran su da ƙalubalen da tarbiyyar iyali ke fuskanta a wannan zamani namu. Ban san yanzu ko su wa suka fi yawan kaiwa…
Read More
Takardar da ta tona ƙarairayin Amurka

Takardar da ta tona ƙarairayin Amurka

Daga CMG HAUSA A ƙarshen watan Mayun da ya gabata, sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka Antony Blinken ya gabatar da wani jawabi a kan manufofin ƙasar Amurka a kan kasar Sin, inda ya sha tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasar Sin da ma shafa wa ƙasar bakin fenti a kan manufofinta na gida da waje. Sai dai kome ƙoƙarinta, ba ta iya boye ainihin burin da take neman cimmawa na daƙile ci gaban ƙasar Sin daga dukkan fannoni ba. A ranar 19 ga wata da dare, ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta fitar da wata takarda mai taken "Kura-kurai…
Read More
Kasancewar mutane masu aƙidu da al’adu daban-daban na buƙatar haƙuri da mutunta juna

Kasancewar mutane masu aƙidu da al’adu daban-daban na buƙatar haƙuri da mutunta juna

Daga FA'IZA MUHAMMAD MUSTAPHA Majalisar Ɗinkin Duniya ta gudanar da wani taro a jiya, albarkacin ranar adawa da kalaman kiyayya ta duniya, inda zaunannen wakilin Sin dake majalisar Zhang Jun ya yi kira ga ƙasashen duniya su mutunta tare da haƙuri da juna, kana su rika tattaunawa cikin adalci don yaki da kalaman kiyayya. Ƙasar Sin ta kasance daya daga cikin ƙasashen da suka gabatar da ƙudurin ayyana ranar ta yaƙi da kalaman kiyayya a shekarar 2021, inda aka fara gudanar da ita karon farko a bana. Kamar yadda wakilin na Sin ya bayyana, yaƙi da kalaman ƙiyayya na bukatar…
Read More
Wakilin Sin a MƊD ya yi kira ga ƙasashen duniya da su haɗa kai don yaƙar kalaman nuna ƙiyayya

Wakilin Sin a MƊD ya yi kira ga ƙasashen duniya da su haɗa kai don yaƙar kalaman nuna ƙiyayya

Daga CMG HAUSA Jiya Litinin, zaunannen wakilin Sin dake MƊD Zhang Jun, ya yi jawabi a wajen kwarya-kwaryar taron MƊD game da ranar adawa da kalaman nuna kiyayya, inda ya yi kira ga ƙasashen duniya da su mutunta juna tare da yin shawarwari cikin adalci don yaƙi da irin wadannan kalamai. Zhang Jun ya nuna cewa, ƙasar Sin na goyon bayan babban taron MƊD da ya kira irin wannan taro don tunawa da rana ta farko a wannan fanni. Babban taron MƊD ya zartas da kuduri a watan Yuli na shekarar 2021, inda aka mai da ranar 18 ga watan…
Read More