Editor

9513 Posts
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 23 a Zamfara

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 23 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Aƙalla mutane 23 da suka haɗa da mata biyu da ’ya’yan tsohon Akawun Jihar Zamfara Alh. Abubakar Bello wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Furfuri da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu a jihar ta Zamfara. Wani mazaunin yankin mai suna Malam Haruna Manaja Furfuri a wata tattaunawa ta wayar tarho da Blueprint Manhaja, ya ce ‘yan bindigar sun yi wa garin ƙawanya ne da misalin ƙarfe 2:30 na safiyar Litinin. A cewarsa, ‘yan bindigan sun je kai tsaye gidan tsohon Akanta-Janar na Zamfara Alh. Abubakar Bello, inda suka yi garkuwa da matansa…
Read More
Ɗaliban Kaduna 701 ba za su rubuta jarrabawar WAEC ba

Ɗaliban Kaduna 701 ba za su rubuta jarrabawar WAEC ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗalibai 701 daga jihar Kaduna ba za su zana jarrabawar kammala sakandire ta WAEC ba saboda rashin ba su damar biyan kuɗaɗen da ya kamata su biya. Jaridar Punch ta ruwaito cewa ɗaliban, waɗanda suka fito daga makarantun sakandire daban-daban a jihar an ƙi ba su damar sanya makinsu na makaranta a shafin hukumar da ake shirya jarrabawar kammala karatun sakandiren. Ko da yake, hukumar daga bisani ta yi kira ga makarantun da abin ya shafa a kan cewa za a ƙara buɗe shafin domin su sanya makin nasu.Makarantun da abin ya shafi ɗalibansu…
Read More
2023: Tabbatar da nasarar Tinubu shi ne aikinmu – Sanata Adamu

2023: Tabbatar da nasarar Tinubu shi ne aikinmu – Sanata Adamu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa yanzu ba su da wani aiki a gabansu da ya wuce na tabbatar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa a APC, Sanata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kai bantensa a zaɓen 2023. Adamu ya ya bayyana haka ne ga manema labarai yayin ziyarar da shi da tawagarsa suka kai wa Tinubu a gidansa da ke Abuja ranar Alhamis don taya shi murnar lashe zaɓen fid-da gwani na APC da ya yi a Larabar da ta gabata. Da yake yi wa manema labarai jawabi yayin ziyarar, Adamu ya…
Read More
HOTUNA: Ziyarar Sanata Adamu da tawagarsa ga Tinubu

HOTUNA: Ziyarar Sanata Adamu da tawagarsa ga Tinubu

Alhamis da ta gabata, Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya jagoranci Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na Jam'iyyar zuwa gidan ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam'iyyar, Sanata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu don taya shi murnar lashe zaɓen fid-da gwani na APC a Larabar da ta gabata.
Read More
Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamnati ta ba da hutun gama-gari

Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamnati ta ba da hutun gama-gari

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 13 ga Yunin 2022 a matsayin ranar hutun gama-gari albarkacin Bikin Ranar Dimokuraɗiyya. Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja. Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen taya ‘yan Najeriya murna dangane da bikin wannan rana, tare da yin kira ga ‘yan kasa baki ɗaya da a ci gaba da mara wa gwamnati baya don tabbatar da ingancin ƙasa a dukkanin fannoni. “Yayin da muke bikin Ranar Dimokuraɗiyya, ya kamata mu waiwaya mu dubi ƙoƙarin magabatanmu sannan…
Read More
Da abokin daka akan sha gari

Da abokin daka akan sha gari

Daga SAMINU HASSAN Kamar yadda muke ji yau da kullum daga bakin masana, cewa babu wata ƙasa a duniyar nan da za ta samu cikakken ci gaba, ba tare da bunƙasa yankunanta na karkara ba, muna iya ganin shaidu na zahiri don gane da hakan a nan ƙasar Sin. Mahukuntan ƙasar Sin sun jima da fahimtar muhimmancin kawar da ƙangin talauci da raya karkara, a matsayin babban jigon gina ƙasa, tare da tabbatar da ba a bar wani ɓangare na alummar Sinawa a baya ba. Kaza lika da yake yankunan karkara na taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasa, ta hanyar…
Read More
Xi Jinping ya rubuta wasiƙa ga mahalarta taron ƙarawa juna sani na jam’iyyu shida dake Kudancin Afirka da suka kafa makarantar Julius Nyerere

Xi Jinping ya rubuta wasiƙa ga mahalarta taron ƙarawa juna sani na jam’iyyu shida dake Kudancin Afirka da suka kafa makarantar Julius Nyerere

Daga CMG HAUSA Jiya Laraba, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya rubuta sako ga dukkan mahalarta taron sanin makamar aiki na jami’ai matasa na jam’iyyu shida dake kudancin nahiyar Afirka, waɗanda suka kafa makarantar koyar da harkokin shugabanci ta Julius Nyerere. Xi ya ce, neman cimma muradun ci gaba, da farfaɗo da al’umma da samar da alfanu ga jama’a, na buƙatar jajircewar zuriyoyin al’umma. Kara gina duniya mai kyakkyawar makoma, na buƙatar mu’amalar ƙasa da ƙasa. Xi ya jaddada fatansa cewa, ya dace waɗannan jami’an su dauki nauyin dake wuyansu, da nuna kwazo wajen raya sha’anin ƙarfafa zumunta tsakanin Sin…
Read More
Sin ta yi kira da a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Tsakiyar Afirka

Sin ta yi kira da a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Tsakiyar Afirka

Daga CMG HAUSA Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD ya yi kira da a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tsakiyar Afirka. Dai Bing ya faɗi haka ne yayin wani taron kwamitin sulhu na MƊD kan batun yankin tsakiyar Afirka da aka yi a jiya, inda ya kuma nuna cewa, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na tsakiyar Afirka, yana amfanawa cikakken tsaron nahiyar Afirka. Kuma ƙasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan ƙasashen da ke yankin da su yi ƙoƙarin kiyaye ikon mulkin ƙasa da cikakkun yankunansu. Ya ce…
Read More
Sharhin littafin ‘Ruɗanin Tunani’

Sharhin littafin ‘Ruɗanin Tunani’

Daga NATA’ALA SAMBO BABI (NASABA) Sunan littafi: Ruɗanin TunaniMawallafi: Bello Muhammad Ɗan yayaYawan shafuka: shafi 99Shekarar da aka buga: 2012Kamfanin da ya buga: Makarantar HausaKamfanin da ya yi ɗab’i: Parresia Press, Ibadan. Daga farko kamin na shiga a cikin sharhin littafin 'Ruɗanin Tunani' zan ɗan cirato wani abu kaɗan daga wasar kwaikwayo na baka da na zube, ko kuma ace wasar kwaikwayo ta Da da ta Zamani, ya alla ko za a fi fahimtar irin namijin ƙoƙarin da aka yi akan samar da littafan wasar kwaikwayo, waɗanda cikin su, har da 'Ruɗanin Tunani'. Su dai masana suna ganin akwai dangantaka…
Read More